×

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai.

MUSULUNCI

Taqaitaccen Saqo game da Musulunci kamar yadda ya zo cikin Al-qur'ani da Sunnanr Annabi

Kwafin da babu Nassoshi a cikin

Saqo ne mai Muhimmanci wanda ya qunshi bayani game da Musulunci da yake bayanin mafi Muhimmancin Tushen sa da koyarwarsa da kyawawun sa wanda aka samo su daga Tushe na Asali shi ne Al=qur'ani Maigirma da Kuma Sunnar Annabi da kuma Saqon da aka turashi zuwa ga baki xayan Baligai na Musulmai da Yarukansu a kowane lokaci da kuma ko ina suke duk da savanin Yanayi da kuma Hali

1.Musulunci shi Saqon Allah zuwa ga Mutane baki xayan su shi ne Saqon Allah wanzazze

2.Kuma Musulunci ba Addinin wasu kevantattun Mutane ba ne ko jinsi a'a Addinin Allah ne ga Mutane baki xayan su

3.Musulunci shi ne Saqon Allah wanda ya zo don cika Saqonnin Annabawa da Manzanni waxanda suka gabata -Amincin Allah ya tabbata a gare su- zuwa ga Al-ummansu

4.Annabawa Amincin Allah a gare su Addininsu xaya ne kuma Shari'unsu sun sha banban

5.Musulunci yana kira -Kamar yadda kowane Annabi yayi: Nuhu da Ibrahim da Musa da Sulaiman da Daud da Isa -Amincin Allah a gare su- zuwa ga Imani cewa Ubanji kaxai shi ne Allah wanda yayi halitta kuma mai raya wa mai kashewa Mai Mulki Mamallaki, kuma shi wanda yake gudanar da Al-amura, kuma shi ne mai jin Qai mai Tausasasawa

6: Allah Maxaukakin Sarki shi ne wanda yayi halitta kuma shi ne wanda ya cancanci Ibada shi kaxai, kuma ba'a bautawa kowa waninsa tare da shi

7: Allah shi ne Mahalicci ga baki xayan halitta abunda muke iya gani da waxan da bama iya gani, kuma duk wani abu da ba shi ba to shi abun Halitta ne da cikin halittunsa, kuma shi ya halicci Sammai da Qasa cikin kwana Shidda

8.Kuma Allah Maxaukakin Sarki bashi da abikin tarayya a cikin Mulkin sa da halittun sa ko Bayin sa

9.Allah Maxaukakin Sarki bai Haifa ba kuma ba'a haifeshi ba kuma bashi wani kini ko mai kamanceceniya da shi

10.Allah Maxaukakin Sarki baya sauka a cikin wani abu, ko kuma ya saje da jikin wani abu daga cikin halittunsa

11.Allah Maxaukakin Sarki Mai rangwame ne muka mai jin Qai ga bayinsa shi yasa ya aiko Manzanni kuma ya saukar da litattafai

12. Allah shi ne Ubangiji Mai jin qai shi kaxai wanda shi ne zai yi Hisabi ga Halittu a ranar Al-qiyama lokacin da zai tashe su baki xayansu daga Qaburburansu, saboda ya sakawa kowanne Mutum da aikin da yayi na Al-kairi ko sharri, saboda dik wanda yayi aiki nagari kuma yana mai Imani to yana da Ni'ama Matabbaciya, kuma duk wanda ya Kafirta kuma yayi mummunan aiki to yana da Azaba Mai girma a Lahira.

13. Allah Maxaukakin Sarki ya halicci Xan Adam daga turvaya, kuma ya sanya Zurriyarsa tana yaxuwa bayansa, saboda Mutane a Asalisu daidai suke, kuma babu banbanci a tsakanin jinsi da jinsi ko kuma Mutane kan Mutane sai da tsoron Allah.

Kuma kowane Yaro ana haifarsa ne akanTurbar dai dai.

15. kuma babu wani Mutum da aka haifeshi da Savo ko ya gaji savon waninsa

16.Kuma Manufa na halittar Mutane ita ce bautar Allah shi kaxai

17. Musilunci ya Karrama Mutum -Maza da Mata- kuma ya xauke masa baki xayan Haqqoqin sa, kuma ya sanya shi abun tambaya akan baki xayan sauran Zaxuxxukan sa, da Ayyukansa da kuma Tasarrufin sa, kuma ya xora masa nauyin kowane irin aiki da zai cutar da kansa ko ga wani akan sa

18. kuma ya Sanya Namiji da Mace daidai da daidai wajen xaukar Alhakim aikinsu da kuma sakamako da bada lada

19. Musulunci ya karrama Mace, kuma ya sanya Mata su zamanto abokan tafiyar Maza, kuma ya lazamtawa Mazan ciyar da su idan ya kasance yana da iko, saboda haka ya Wajaba Uba ya ciyar da Xiyarsa, haka Uwa akan Xanta idan ya kasance ya Balaga kuma yana da Iko, haka Mata akan Mijinta

20. kuma Mutuwa ba Karewa bace ta har Abada, a'a ita wata tafiya daga Gidan aiki zuwa gidan Sakamako, kuma Mutuwa yana samun Jiki da Ruhi, Mutuwar Ruhi ita ce rabuwar Ruhi daga jiki, sannan kuma ya dawo zuwa jinkin bayan tashin Al-qiyama, kuma Ruhi baya tafiya zuwa wani jikin bayan Mutuwa, kuma baya sake tsiruwa a wabi jikin daban

21, kuma Musulunci yana kira ne zuwa Imani da jigajigan Imani Manya, kuma shi ne Imani da Allah da Mala'ikunsa da Imani da litattafan Allah Kamar Al-taura da linjila da Zabuea -kafin jirkita su- da kuma Al-qurani, da kuma Imani da bai xayan Annabawa da Manzanni -Amincin Allah a gare su- kuma yayi Imani da na qarshensu shi ne Muhammad SAW cikamakin Annabawa da Manzanni, kuma da Imani da Ranar Lahira, kuma muna sani cewa rayuwar Duniya da ita ce Qarshen rayuwa; da Halitta da Rayuwa sun zama Wasa tsantsa, kuma Imani da Hukuncin Allah da Qaddara.

22. kuma Annabwa Ma'asumai ne -Amincin Allah a gare su- cikin abunda suka isar da shi daga Allah, kuma Ma'asumai ne ga barin dukkanin abunda ya sava da Hankali, ko kuma kyawawan halaye su kyamace shi, kuma Annabawa an xira musu isar da Umarnin Allah ga bayin sa, kuma Annabawa basu da wani abu na abunda ya kevanxi Allantaka; aa suma Mutane kamar sauran Mutane Allah yai Musu wahayi da Manzantakar sa

23. Kuma Musulunci yana kira zuwa ga bautar Allah shi kaxai da ginshiqan Ibada Manya, sune Sallah wacce ita ce tsayuwa da Ruku'u da Sujada da anbaton Allah da yabonsa da kuma Addu'a, kuma Mutum yana sallatarta sau biyar a wuni, kuma a cikinta babu banbanci tsakanin Mawadaci da talaka da shugaba da kuma Talaka a sahu qwara xaya a cikin Sallah da kuma Zakka wacce taje wani yanki ne kaxan daga cikin Dukiya -daidai da sharaxai da kuma gwargwado wanda Allah ya qaddara,kuma tana wajaba ne a Dukiyar Mawadata kuma a bada ita ga Talakawa da wasunsu, kuma sau xaya ce a Shekara, da kuma Azumi wanda shi ne kamewa ga barin ci da sha da rana a watan Azumi, kuma yana koyawa Mutum Dauriya da haquri, da kuma Hajji wanda shi ne: Nufar Xakin Allah a Makka Mai Alfarma sau xaya a rayuwa ga Mai Iko wanda zai iya, kuma a cikin wannan Hajjin akwai daidaito ga kowa da kowa wajen fuskanta zuwa ga Mahalicci SWT, kuma Banbance banbance da Nuna wani fifiko duka ya kau a cikin sa.

24. kuma daga cikin mafi girman abunda Ibada ta kevanta da shi a Musulunci cewa yadda ake yinta da lokutanta da sharaxanta Allah SWT ne ya Shar'anta ta su kuma ya isar da ita ga Manzonsa SAW, kuma babu wani Mutum da ya da yayi shigege a cikin su ta hanyar qari ko ragi har zuwa wannan rana, kuma baki xayan Manyan Ibadu baki xayan Annabwa sunyi kira zuwa gare su -Amincin Allah a gare su-

25, Manzon Musulunci shi ne Muhammad Bn Abdullahi daga cikin Zuriyar Annabi Isma'ila Xan Annabi Ibrahim -Amincin Allah a garesu- an haife shi Makka a shekara ta 571 Miladiyya, kuma yai Hijita zuwa madina, kuma baiyi tarayya sa Mutanensa ba a Al-amuran bautar Gunki, sai dai shi ya kasance yana tarayya da su a Ayyukan kirki, kuma ya kasance kan kyawawan Halaye tun kafin a aiko shi, kuma Mutanensa sun kasance suna kiransa Amintacce, kuma Allah ya aiko shi yayin da ya cika Shekara Arba'in kuma Allah ya Qarfafe shi da da Ayoyi (Mu'ajizozi) Masu girma, kuma girmansu shi ne Al-qur'ani Mai girma, kuma shi ne mafi girman Ayoyin Annabawa, kuma shi ne Ayoyin Annabwa har zuwa yau xin nan, kuma yayin da Allah ya cika wannan Addinin, kuma Manzon Allah SAW ya isar da shi matuqar isarwa sai ya yi wafati she, Kuma Manzon Allah karunsa suna Sittin da Uku, kuma aka binne shi a garin Madina SAW Kuma manzon Allah Muhammad SAW shi cika makin Annabawa da Manzanni Allah ya aiko shi da shiriya da Addini na gaskiya don ya futar da Mutane daga duhun Bautar Gumaka da Kafirci da Jahilci zuwa hasken Kaxaita Allah da Imani, da Kuma Allah yai masa shida cewa shi ne ya aiko shi yana mai kira zuwa gare shi da umarnin sa

26. Kuma Shari'ar Musulunci wacce Manzon Allah Muhammad SAW ya zo da ita ita ce cika makin Saqonnin Allah da kuma shari'ar Ubangiji; kuma ita ce Shari'ar cikawa, kuma a cikinta akwai gyaruwar Addinin Mutane da Duniyarsu, kuma tana tsarewa a mataki na farko ga Addinin Mutane da Jininsu da Dukiyar su da Hankulan su da Zuriyarsu, kuma ta shafe kowa ce Shari'a da ta gabace ta na daga Shari'u, kamar yadda ta soke vangaren wasun da suka gabaceta.

27. Kuma Alla SWT baya karvar wani Addini in ba Musulunci ba wanda shi ne wanda Annabi Muhammad SAW ya zo da shi, kuma duk wanda ya riqi wanin Musulunci Addini to ba za'a Karva ba

28. Al-qur'ani Maigirma shi ne littafin da Allah ya aikowa Manzon Allah SAW kuma shi ne zancen Ubangijin Talikai wanda Allah ya qure Mutum da Al-jann kan su zo da kwatankwacin sa, ko Sura kwatankawcinsa, kuma har yau qurewa bata qare ba, Kuma Al-qurani yana bada Amsar Muhimmai masu yawa da Muliyoyin Mutane suka gaza, Kuma Al-qurani Maigirma abun kiyayewa ne har zuwa yau xin nan da yaren larabci da ya sauka da shi, kuma ba'a rage ko harafi xaya ba, kuma yana nan a buge ana yaxa shi, Kuma littafi ne Maigirma Mai gajiyarwa wanda ya dace da a Karanta shi ko a karanta Fassararsa, Kamar yadda Sunnar manzon Allah SAW da koyarwarsa da Tarihinsa ababan kiyayewa ne kuma ababan rawaito ne daidai da tsanin jerin Masu riwaya da aka yarda da su, kuma an buga ta da Larabci wanda Manzon Allah SAW yayi magana da shi kuma an fassara ta a Yaruka da yawa, kuma Al-qur'ani da Sunnar Manzon Allah su ne Tushen qwara xaya na Hukunce hukuncen Musulunci da Shari'un sa, saboda Musulunci, saboda ba'a xaukar Musulunci daga aiyukan xaixaikun Mutane da suke danganta kansu da Musulunci; kawai ana xauka ne daga Wahayin Allah a Al-qur'ani Maigirma da Sunnar Annabi

29. Kuma Musulunci yana Umarni da kyautatawa Iyaye, koda kuwa sun kasance ba Musulmai ba ne, kuma ya na wasiyya da 'Ya'ya.

30. Musulunci yana Umarni da Adalci a cikin Magana da kuma Aiki koda kuwa tare da Abokan gaba ne

31, Kuma Musulunci yana Umarnini da a kyautatawa halitta baki xaya, kuma yana kira zuwa kyawawan Halaye, da kuma kyawawan Ayyuka

32. Kuma Musulunci yana Umarni da kyawawan Halaye Kamar Gaskiya da sauke Amana da kuma kamewa da Kunya da Gwarzanta da Karamci da taimakawa Mabuqaci da kai gudun mawa ga wanda yake cikin wani hali, da ciyar da Mai jin yinwa, da kyautata Makwabtaka, da Sadar da Zumunci, da tausasawa Dabbobi

33. Musulunci ya Halatta abubuwa masu daxi na abun ci da sha, kuma yayi umarni da tsarkin Zuciya da jiki saboda haka ya halatta Aure, Kamar yadda ya Umarci Annabawa -Amincin Allah a gare su- da hakan, saboda su suna Umarni ne da dukkan abu mai kyau

34. Musulunci ya haramta dukkan Tushen dukkan Haramun kamar Shirka da bautar Gumaka, da shaci faxi ga Allah bada Ilimi ba, da kashe 'ya'ya. da kashe ran da Allah ya haramta, da varna a bayan qasa, da Sihiri da Al-fasha ta Fili da ta Voye da Zina da Liwaxi, kuma ya haramta Riba, da cin Mushe, da abunda aka yanka ga Gumaka da Dodanni, da kuma cin Naman Alade, da sauran Najasa da Kazanta, kuma ya Haramta cin Dukiyar Maraya da tauye Mudu da ma'auni, kuma ya haramta yanke Zumunci kuma Annabawa -Amincin Allah a gare su- baki xayan su sun haxu kan haramcin waxan nan Abubuwan

35. Musulunci ya hana Munanan Halaye Kamar Qarya da Ha'inci da Yaudara da Ha'inci da Danfara, da Hassada da Mummunan kaidi da Sata da Zalunci, kuma ya na hana dukkan wani Mummunan Hali

36. Musulunci ya hana Muna nan Mua'amalolin kuxi waxanda cikinsu akwai riba ko cutarwa ko kuma garari ko zalunci ko Al-gus, ko kuma yana kaiwa zuwa ga Masifu, ko Cutarwa da zata game baki xayan Kasashe da kuma Mutane da xaixaiku

37. <usulunci ya zo da kiyaye Hankula da Haramta dukkan abunda zai vata shi kamar Shan Giya, kuma Musulunci ya xaga Darajar Hankali kuma ya sanya shi doron dora nauyi, kuma ya 'Yantashi daga dabaibayin Taysuniyoyo da bautar gumaka kuma a Musulunci babu wasu Voyayyun abubuwa ko hukunce Hukunce da suka kevanci Wasu Mutane koma bayan Wasu, kuma baki xayan hukunce Hukuncen sa da Shari'un sa sunyi daidai da hankula Ingantattu, kuma ita ce daidai da Adalci da Hikima

38. kuma Addinann Vata idan Mabiyansu basu gamsu da abunda yake cikinsu ba na kwangaba kwanbaya, da Al-amuran da hankali ba zai xauka ba sai Malaman Mabiya Addinin sai su ruxi Mabiyan da cewa ai Addini sama yake da Hankali. kuma cewa Hankali ai dole sai da shi wajen fahimtar Addini da kuma riqeshi wanda ko Musulunci ya sanya Hankali wani Haske ne da yake Haskawa Hankali Hanya; saboda Ma'abota Addinan Qarya sunason Mutum ne ya bar Hankalin sa ya bi su, kuma Musulunci yana son Mutum ne da ya farkar da hankalinsa, don yasan haqiqanin Al-amura kamar yadda yake

39. Musulunci yana girmama Ingantaccen Ilimi, kuma yana kwaxaitarwa kan binciken Ilimi wanda yake babu son rai a cikinsa, kuma yana kira zuwa Nazari da Tunani cikin Kawunanmu da kuma halittu da suke kewaye da mu, da kuma sakamakon Ilimi ingantacce don Ilimi waxanda basa cin karo da Musulunci.

40. kuma Allah baya Karvar aiki ko ya bada lada akansa a lahira sai daga waxanda sukai Imani da Allah kuma suka gasgata Manzanninsa -Amincin Allah a gare su- kuma Allah baya karvar ibadu sai da abunda ya Shar'anta, saboda mai zai sa Mutum ya kafircewa Allah kuma ya qaunaci ladansa? kuma Allah baya karvar Imani wani Mutum sai idan yayi Imani da Annabawa -Amincin Allah a gare su baki xaya- Kuma yayi Imani da Saqon Annabi Muhammad SAW.

41. Lallai Manufar Sakonnin Allah baki xayansu shi ne: cewa lallai Addinin Gaskiya ya xaukaka Xan Adam, saboda ya kasance tsantsan Bawan Allah Ubangijin Talikai, kuma ya 'Yanta shi daga bautar Mutane ko kuma wani abun Duniya ko kuma Tatsunuyoyi, saboda Musulunci -Kamar yadda kake ganin sa- baya tsarkake Mutane ya xagasu sama da matsayin su, kuma baya sanya su Alloli ababan bauta.

42. Allah ya Shar'anta tuba a Musulunci wanda shi ne Maida komai da komai xin Xan Adam zuwa ga Ubangijinsa, da barin Zunubai, kuma Musulunci yana rushe abunda yake kafinsa na zunubai, kuma tuba yana wanke abunda ya gabace shi na zunubai, saboda haka babu wata buqata mutum ace sai ya bayyana laifukansa a Mutane.

43, Saboda a cikin Musulunci dangantaka tsakanin Mutum da Allah kai tsaye ta ke, saboda haka baka buqatar wani Mutum da zai kasance tsani tsakaninka da Allah, saboda Musulunci ya hana Mu sanya Mutane su zamanto Alloli ko kuma suna tarayya da Allah cikin Allantakar sa da Bautar sa.

44. a qarshen wannan littafin muna tunsarwa cewa Mutane duk da savanin Zamaninsu da Qabilunsu, da garuruwan su kai baki xayan Duniyar Mutane sun sava a wajen Tunanisu da Manufofin su, sun yi hannun riga wajen garuruwansu da Ayyukan su, saboda haka suna da buqatar wani Mai shiryarwa da zai xorasu kan Turba, da wani tasri da haxe kansu, da wani Jagora da zai kare su, kuma Manzanni -Amincin Allah a gare su- sun jivanci hakan da Wahayi daga Allah Maxaukaki suna shiryar da Mutane zuwa Hanyar Al-kairi da Shiriya, kuma ya haxa su akan Shari'ar Allah kuma suna Hukunci da Gaskiya a tsakaninsu, saboda Al-amuran su su tafi daidai dai dai da yadda waxan nan suka amsawa Manzannin, da kuma kusancinsu da waxan nan lokutan na Saqonnin Allah, kuma Allah ya cika Saqonin Manzancin da Manzo Annabi Muhammad SAW kuma ya Hukunta mata Wanzuwa, kuma ya sanyata Shiriya ga Mutane da kuma Rahama da Haske da Shiriyarwa zuwa Tafarki Mai isarwa zuwa ga Allah SWT

45. Saboda haka nake roqonka ya kai Xan Adam ka tsaya ga Allah tsayuwa ta gasliya kana mai tsiraita kanka daga Kwaikwayo da Al-ada, kuma kasani cewa kai bayan Mutuwar ka zaka koma ne zuwa ga Ubangijinka, kuma ka kalli kanka, da kuma wasu sassa da suke kewaye da kai, ka Musulunta zaka rabauta a Duniyarka da Lahirar ka, idan kuma kana son shiga Musulunci babu abunda zaka yi sai kawai ka shaida cewa Babu abun bauta da gaskiya sai Allah, kuma cewa Annabi Muhammad Manzon Allah ne, kuma kayi watsi da duk abunda ake bautawa koma bayan Allah, kuma kayi Imani cewa Allah zai tashi waxan da suke cikin Qabari kuma cewa Hisabi da sakamako gaskiya ne, to idan ka shaida da Wannan Shaidawar to haqiqa ka zama Musulmi, saboda haka bayan haka zaka bautawa Allah da abunda ya Shar'anta na Sallah da Zakka da Azumi, da kuma Hajjatar Xakin Allah idan ka samu Iko yin hakan,

Kwafi a ranar 19-11-1441

Wanda ya Rubuta shi Shi Farfesa Muhammad Bn Abdullahi Al-Suhaim

Babban Malamin koyar da Aqida a Vangaren koyar da Darussan Musulunci (a da can)

Tsangayar Koyo da koyarwa, na jami'ar Sarki Su'ud

Ritadh, Kasar Saudi Arabia

MUSULUNCI

Taqaitaccen Saqo game da Musulunci kamar yadda ya zo cikin Al-qur'ani da Sunnanr Annabi

معلومات المادة باللغة العربية