Description
Yayi Magana ne akan abubuwan dake karya alwala , wanda wasu daga cikin musulmai sun jahilcesu
wasu fassarori 3
ABUBUWAN DAKE KARYA ALWALA
[Hausa هوسا-]
Malan Aliyu Muhammad Sadisu
2014 - 1435
نواقض الوضوء
[Hausa هوسا-]
الشيخ : علي محمد السادس
2014 - 1435
ABUBUWAN DAKE KARYA ALWALA
Shinfida: Lalle wannan babi yana da matukar muhimmanci, domin bayan da kasan alwala to ya kamata kasan abin da ke warwareta, akan haka ya ka yiwa kanka hukunci idan zaka yi sallah ko abinda dole sai da alwala ake yinsa, saboda haka yana da matukar kyau mu kula da wadannan hukunce-hukunce. Allah ya yi mana jagora.
Abubuwan da suke bata alwala sunkasu kashi biyu; Hadasi da Sababinsa. Abin nufi anan shine, akwai abinda shi karankan sa yake bata alwala to wannan shi ake kira Hadasi (Al'ahdaas). Akwai kuma wanda shi karankan sa bai warware alwala amma zai kai ka ga abinda yake warware alwalar to wannan shi ake kira, Sabuban Hadasi (Asbabul Ahdas).
To shi hadasin wato abinda yake karya alwala da karankansa, abubuwane guda shidane, hudu daga cikinsu suna fitane ta gaba, sune kuma; Fitsari, Maziyyi, Wadiyyi da kuma Maniyyi. Wadannan idan suka faru ko dayansu ya faru to tsarki kawai za'a yi a sake alwala in banda maniyyi, Wanda shi maniyyi bayan ya bata alwala sai kuma anyi wanka.
Sai kuma guda biyu da suke fita daga dubura, sune kuma; Bayangida da kuma tusa. Amma shi bayan-gida tsarki za'a yi sai a sake alwala, sabanin tusa wacce take ita ba'a yi mata tsarki alwala kawai za'a sake.
Sai kuma abubuwan da suke sabubbane na hadasin wadanda yake suna da wasu bayanai, amma su wadancan da zarar ya diga komai kankantarsa to ya karya alwala inbanda mai fama da cutar yoyon-fitsari, wadannan abubuwa sune;
(1) Bacci: Shi bacci a nan ya kasu kashi hudu;
(a) Dogon bacci mai nauyi, kai tsaye wannan ya karya alwala.
(b) Takaitaccan bacci mai nauyi, shi ma ya karya alwala.
(c) Takaitaccan bacci mara nauyi to shi bai karya alwala ba.
(e) Dogon bacci mara nauyi, bai karya alwala amma anfi so a sake ta.
Ma'aunin da ake auna bacci da shi domin a gane yana da nauyi ko ba shi da nauyi shine; Idan ka san wanda ya zo da wanda ya tashi to baccinka bai yi nauyi ba, amma idan baka san wanda ya zo ba ko wanda ya tashi ba to baccin ya yi nauyi. Kenan idan kuna fira sai amma kana gyangyadi sai da ka farka sai kace; ina wane? Ko; wane yaushe ka zo? To kasan baccinka ya yi nauyi, Allah ya sa mu dace.
(2) Gushewar Hankali: Idan hankalin mutun ya gushe ta hanyar hauka ko farfadiya ko suma ko maye to mu sani alwalarsa ta karye. Kenan idan mutum ya yi alwala sai ya hau iska ko kuma suka yi hadari kawai sai ganinsa ya yi a asbiti ko kuma ya sha ta yi Marisa-ta sha kafso to alwalar ko wannensu ta karye.
(3) Shafar Azzakari: Idan mutum ya shafi al'aurarsa kai tsaye tafin hannunsa ya taba al'aurarsa bawai ta samani riga ko wandoba ko kuma wani kyalleba to malamai sun karawa juna sani kan makomar al'walarsa, wadansu suke ce kawai alwalarsa ta karye, wasu kuma suka ce idan ya tabane domin ya ji dadi to ta karye amma idan ba wai ya yi hakanne domin ya ji dadi ba alwalarsa nanan, wannan maganar kuwa tana da karfi. Amma dukkanin malamai sun yi ittifaki kan cewa idan ya taba al'aurarsa ba kai tsayeba ko dai ta saman wando ko saman riga ko saman wani kyalle to alwalarsa nanan daram.
(4) Shafar Mace/Namiji: Idan namiji ya shafi mace domin ya ji dadi to ko ya ji dadin ko bai ji ba alwalarsa ta karye, haka kuma al'amari yake idan mace ta taba namiji domin ta ji dadi to ta ji dadin ko bata ji ba alwalarta ta karye, malamai sun kasa shafar zuwa gida hudu;
(a) Idan ya taba domin ya ji dadi kuma ya ji dadin to alwalar ta karye.
(b) Idan ya taba ba don ya ji dadi ba sai kuma ya ji dadin to ta karye.
( c) Idan ya taba domin ya ji dadi sai bai ji da din ba to alwalar ta karye.
(d) Idan ya taba ba domin ya ji dadi ba kuma bai ji dadinba to alwalarshi tanan daram. Wadannan bayanai haka mai Ashmawi ya kawosu. Mu sani wadannan bayanai sun shafi macema idan ita ta yi.
Akwai wadansu da malamai suka karawa juna sani akan suna karya alwala ko basa karyawa?, wadannan kuma sune:
(5) Shakka Akan Hadasi: Idan mutum ya tabbatar da alwalarsa sai kuma yake kokwanto ya yi hadasi ko bai yi ba? Kenan bashi da tabbas? Wasu malamai sukace; Ai da ya yi kokwanto alwalarsa ta karye domin ba'a sallah da wani abu na shakku. Wasu malaman kuma suke: Idan ya tabbatar da yana da alwala sai daga bayane yake shakka to ai shakka bata ture abinda yake dahir, saboda haka sukace alwalar nanan, Allah shine masani.
(6) Ridda: Shine mutum musulmi ya kafirta (Allah Ya tsaremu). Wadansu malamai sukace da zarar ya bar musulunci to da zarar alwalar ta karye, wasu malaman kuma sukace; A'a, ai ayyukansa da ya yi ba za su baciba sai in ya mutu bai dawo musulunci ba, wadda alwala na cikin wadannan ayyukan. Mafi kyawu ga wadannan abubuwa mutum ya sake alwalar shi yafi.
Alwala bata baci idan mutum ya yanke farce (Kunba), ko ya taba marenansa ko duburarsa ko anyi masa kaho ko ya yi dariya ko amai ko kuma tuntube har jini ya fita duk alwala bat abaci saboda wadannan, ko mace ta shafi gabanta amma idan ta sa yatsa a ciki to wasu sunce alwalar ta karye. Idan mutum yana jin fitsari ko tusa ko bayan gida abinda musulunci ya karantar shine mutum ya je ya biya wannan bukatar ta shi tukunna, maimakon ya matse.
Kammalawa: Alwala tana da muhimmanci matuka saboda haka a kiyayeta a san kuma abinda yake warwareta, kuma wannan yake nuna mana cewa tunda har alwala za'a ce akwai abubuwan da suke warwareta dudda ga laima a jikin mutum amma ace alwalarsa ta warware to lalle yana da kyau musan kuma abubuwan da suke warware musulunci domin kullun mutum ya dinga ba addininsa kariya ta yadda kada ya warware, Allah yak are mana addinimmu, amin.
Rbutawa :
Malan Aliyu Muhammad Sadisu