الوصف
كتاب نواقض الإسلام مترجم إلى لغة الهوسا، للإمام المجدد محمد بن عبد الوهاب - رحمه الله -، يعرض فيه بعض النواقض التي عدها الشيخ - رحمه الله -، ونص على إجماع أهل العلم على اعتبارها هادمة للإسلام، وناقضة له، وهى من الأمور التي يجب على المسلم الحريص على دينه تعلمها ومعرفتها؛ ليسلَمَ له دينه، ويبقى عقد إيمانه.
ترجمات أخرى 4
[الهوسا- Hausa]
Wallafar:
Shaikhul Islam Muhammad bn Abdulwahhab.
Fassarar: Aliyu Muhammad Sadisu.
Dubawar: Attahiru Bala Dukku
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga ma’aikin Allah, da iyalanshi da kuma sahabbanshi baki daya.
Bayan haka: Hakika wannan littafi yana da matukar falala da daraja da matsayi a zukatan al’ummar musulmi, wannan ko ya kasance ne lura da abinda littafin ya kunsa na wayar da kan al’umma akan tsadar da wannan addini na musulunci yake da shi, domin dukkanin wanda ka ganshi musulmi to zabin Allah ne, sai shi musulmin ya tashi tsaye ya yi riko da wannan addini ya kuma godewa Allah da ya yi mishi dace da kasancewa musulmi.
Mawallafin wannan littafi ya zayyano wadansu abubuwa guda goma (10) da suke warware musulunci, bawai don suke nan ba sai domin musansu kuma mu nisance su, sannan kuma suna cikin abubuwan da mutane suke yawan aukawa.
Abinda yasa malam ya lissafosu dudda basu Kenan ba saboda kai musulmi ka nisancesu kuma ka gujesu ka nisantar da ‘ya’yanka da iyalanka baki daya, haka nan kuma makwafta a gida ko a wurin aiki ko ma a kasuwa.
Idan akace ‘Nawaqidhul Islam’ ana nufin abubuwan da suke warware musulunci, kenan kamar yadda kasan akwai abubuwa da suke warware alwala, zaka ga mutum da laima a hannunsa amma yace maka zai sake alwala saboda ya san ya aikata daya daga cikin abubuwan da suke warware alwala. Haka kuma akwai abubuwan da suke bata sallah da wanda suke suke bata azumi da kuma masu bata Hajji da abubuwan da suke bata sadaka, to haka nan akwai abubuwan da suke bata musulunci (Allah ya tsare mu).
Anan kamata ya yi mutum ya sansu ba ya yi fada ba, domin mutane sun kasu kashi uku awannan Magana:
(1) Musulunci Bai Warwarewa: Anan akwai mutanen da suke ganin kwata-kwata babu yadda za’a yi ace wai mutum musulincinsa ya warware, wannan Magana kuwa cike take da kuskure, sannan kuma ta rusa ayoyi masu tarin yawa da ingantattun hadisan ma’aikin Allah.
(2) Manyan Laifuka Na Fitarwa: Haka kuma akwai wadanda suke ganin ai da zarar mutum ya aikata babban laifi (Kabeerah) to ya fita daga musulunci, wannan Magana itama makare take da kuskure domin ta sabawa karantarwar Alkur’ani da kuma ingantattun hadisan ma’aikin Allah.
(3) Mutum Na Fita Amma… : Sai Magana ta uku wacce itace ta daidai, wacce take tabbatar da mutum yana fita daga musulunci bayan da yana ciki, sabanin maganar farko, kuma ba kowanne aiki ne da ya yi da ya kafirta ba sabanin Magana ta biyu. Ayoyi da yawa da hadisai masu tarin yawa sun fayyace cewar mutum yana fita daga musulunci bayan da yana ciki (Allah ya sawwake), akan hakane malamai suka wallafa litattafai da babi-babi akan hukunce-hukuncen masu ridda.
1. Za mu kawo takaitaccen tarihin mawallafin wannan littafi na ‘Nawaqidhul Islam’ wato ((Abubuwan da suke warware musulunci)).
2. Za mu kawo gundarin bakin littafin da larabcinsa.
3. Sannan sai fassararshi.
Muna rokon Allah da sunayansa kyawawa da kuma siffofinsa madaukaka da ya yi mana jagora ya yi mana muwafaka, ya kuma sanya albarka a wannan aiki, ya anfanar da mu baki daya.
Mai fassara:
Aliyu Muhammad Sadisu.
Minna, Nigeria.
Shi ne: Muhammad dan Abdulwahhab dan Sulaiman dan Aliyu dan Muhammad dan Ahmad, daga kabilar Tamim. Ana mishi lakabi: Shehul Islam, ko kuma; Mujaddadi.
An haife shi a garin Uyaina dake arewa maso gabas da birni Riyadh, a shekara ta 1115, (bayan hijira), kuma anan ya tashi, a gidan na su da yake cike da ilimi da kuma kulawa.
Ya kammala haddace Alkur’ani mai girma alokacin shekarunsa na haihuwa ba su kai goma ba, a hannun mahaifinsa. Ya yi fice a fannoni da dama, kamar; Fikihu da Hadisi da Tauhidi da kumaTafsiri.
Ya yi tafiye-tafiye da dama domin neman ilimi, ya je birnin Makkah domin yin aikin hajji kuma ya yi anfani da wannan tafiya ya yi karatu awurin manyan malaman Makkah na wannan lokacin, kuma ya je birnin Madina ya kuma jima a wannan birni domin neman ilimi, haka nan kuma ya je kasar Iraki ya kuma jima a Basrah, ya kuma yi karatu a gaban malaman wannan gari, haka nan kuma ya je Ahsah, ya yi anfani da wadannan tafiye-tafiye domin neman ilimi da kuma isar da sakon Allah madaukakin sarki (wato Da’awah).
Ya yi karatu a gaban malamai da dama, ga kadan daga cikin su:
1. Mahaifinsa Shehun malami Abdulwahhab dan Sulaiman.
2. Shehun malami Shihabuddin Alkalin Basrah.
3. Shehun malami Abdullah dan Muhammad dan Abdulladif.
4. Shehun malami Muhammad dan Hayatu Sindi.
5. Shehun malami Abdullah dan Ibrahim dan Yusuf.
Haka kuma yana da dailibai masu tarin yawa, daga cikinsu akwai:
1. Shehun malami Ahmad dan Suwailim.
2. Shehun malami Aliyu dan Muhammad dan Abdulwahhab.
3. Shehun malami Abdurrahman dan Hasan dan Muhammad.
4. Shehun malami Imam Abdul’aziz dan Muhammad dan Sa’ud.
5. Shehun malami Husain dan Ganam.
Wannan shehun malami mawallafin wannan littafi ya karar da rayuwarsa ne wurin karantarwa da fadakarwa da kiran mutane akan su kasance a asalin karantarwar musulunci da Allah ya aiko manzan Shi da ita, akan haka ake kiran shi da mujaddadi, domin ya samu jama’a da yawa ana tafiya ne akan tatsunuyoyi da neman bukatu a kabarurruka da kiran matattu akan su kawo a gaji dadai sauran su.
Ya wallafa littafai da dama, daga cikin su akwai:
1. Takaitaccan Tarihin Ma’aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi), (Mukhtasaru Siratur Rasuli Sallallahu Alaihi wa sallam).
2. Munanan Dabi’un Maguzawa (Masa’ilul Jahiliyya).
3. Ladubban Tafiya Sallah (Aadabul Mashyi Ilas Salah).
4. Tushen Imani (Usulul Iman).
5. Ginshikai Uku. (Usulus Salasa).
6. Ka’idoji Hudu (Alkawa’idul Arba’ah).
7. Abubuwan da suke warware musulunci (Nawaqidhul Islam)
8. Littafin Tauhidi (Kitabut Tauhid). Da wasu littafan masu tarin yawa.
Ya rasu a shekara ta: 1206. (bayan hijira), bayan ya shafe kusan shekaru (91), Allah ya ji kansa da gafara ya kuma rahamshe shi, in ta mu ta zo Allah ya sa mu cika da Imani, amin.
قاَلَ اَلشَّيْخُ اَلإِمَامُ مُحَمَّدُ بنُ عَبْدِ اَلوَهَّابِ – رَحِمَهُ اَللهُ تَعَالَى -:
Shaikh Muhammad dan Abdulwahhab Allah ya yi masa rahama ya ce:
اِعْلَمْ أَنَّ نَوَاقِضَ اَلإِسْلاَمِ عَشَرَةُ نَوَاقِضَ:
اَلأَوَّلُ: اَلشِّرْكُ فِي عِبَادِةِ اَللهِ تَعَالَى.
قَالَ اَللهُ تَعَالَى: ﴿لَقَد كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُواْ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلمَسِيحُ ٱبنُ مَريَمَ وَقَالَ ٱلمَسِيحُ يَبَنِي إِسرَءِيلَ ٱعبُدُواْ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبَّكُم إِنَّهُ مَن يُشرِك بِٱللَّهِ فَقَد حَرَّمَ ٱللَّهُ عَلَيهِ ٱلجَنَّةَ وَمَأوَىهُ ٱلنَّارُ وَمَا لِلظَّلِمِينَ مِن أَنصَار٧٢﴾ المائدة: ٧٢.
وَمِنْهُ اَلذَّبْحُ لِغَيْرِ اَللهِ، كَمَنْ يَذْبَحُ لِلْجِنِّ أَوْ لِلْقَبْرِ.
Na Daya: Shirka a cikin bautar Allah madaukakin sarki; Allah madaukakin sarki yana cewa: ‘’ Lalle Allah ba ya gafartawa idan aka hada Shi da wani, Ya na gafarta abinda bai kai haka ba ga wanda ya so’’. Suratun Nisa’i, aya ta: 116.
Kuma Allah y ace: ‘’ Lalle yadda lamarin yake duk wanda ya hada Allah ya yi wa Allah shirka (ya hada shi da wani) to tabbas Allah ya haramta masa aljanna kuma makomarsa wuta ce, azzalumai ba su da mataimaka’’. Suratul Ma’idah, ya ta: 72.
Yana kuma daga cikin shirka: Yanka domin wanin Allah, kamar wanda zai yanka domin aljan ko domin kabari.
اَلثَّانِي: مَنْ جَعَلَ بَيْنَهُ وَبَيْنَ اَللهِ وَسَائِطَ يَدْعُوهُمْ وَيَسْأَلُهُمْ وَيَتَوَكَّلُ عَلَيْكُمْ، كَفَرَ إِجْمَاعًا.
Na Biyu: Duk wanda ya sanya tsani tsakaninsa da Allah, yana kiran wannan tsanin yana rokonsu yana kuma dogara akansu, (to wannan) ya kafirta, babu wani sabani.
اَلثَّالِثُ: مَنْ لَمْ يُكَفِّرِ اَلْمُشْرِكِينَ أَوْ شَكَّ فِي كُفْرِهِمْ أَوْ صَحَّحَ مَذْهَبَهُمْ كَفَرَ.
Na Uku: Duk wanda bai kafirta mushirikai ba ko kuma ya yi kokwanton kafircinsu ko kuma ya inganta ra’ayinsu (to wannan shi ma) ya kafirta.
اَلرَّابِعُ: مَنِ اَعْتَقَدَ أَنَّ غَيْرَ هَدْيِ اَلنَّبِيِّ ﷺ أَكْمَلُ مِنْ هَدْيِهِ، أَوْ أَنَّ حُكْمَ غَيْرِهِ أَحْسَنُ مِنْ حُكْمِهِ، كَالَّذِي يُفَضِّلُ حُكْمَ اَلطَّوَاغِيتِ عَلَى حُكْمِهِ، فَهُوَ كَافِرٌ.
Na Hudu: Duk wanda ya kudurce azuciyarsa cewar sabanin karantarwar Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) shi ne abu mafi kyau akan shiriyarsa, ko kuma hukunce-hukuncen waninsa su ne mafi kyau akan hukunce-hukuncensa, kamar dai wanda ya ke fifita hukunce-hukuncen dagutai akan hukunce-hukuncen ma’aikin Allah.
اَلْخَامِسُ: مَنْ أَبْغَضَ شَيْئًا مِمَّا جَاءَ بِهِ اَلرَّسُولُ ﷺ وَلَوْ عَمِلَ بِهِ كَفَرَ.
Na Biyar: Duk wanda ya yi fishi da abinda ma’aikin Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya zo da shi, ko da ko ya yi aiki da shi to ya kafirta.
اَلسَّادِسُ: مَنِ اَسْتَهْزَأَ بِشَيْءٍ مِنْ دِينِ اَلرَّسُولِ ﷺ أَوْ ثَوَابِ اَللهِ أَوْ عِقَابِهِ كَفَرَ. وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: ﴿ قُل أَبِٱللَّهِ وَءَايَتِهِ وَرَسُولِهِ كُنتُم تَستَهزِءُونَ٦٥ لَا تَعتَذِرُواْ قَد كَفَرتُم بَعدَ إِيمَنِكُم إِن نَّعفُ عَن طَائِفَة مِّنكُم نُعَذِّب طَائِفَةَ بِأَنَّهُم كَانُواْ مُجرِمِينَ٦٦﴾ التوبة: ٦٥ – ٦٦.
Na Shida: Duk wanda ya yi izgili da wani abu na addinin (musulunci) da manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya zo da shi, ko (izgili da) ladan da Allah zai bayar (akan wani aiki) ko ukubar da Allah ya tanada, to shi ma ya kafirta, dalili kuwa Allah madaukakin sarki yana cewa: ‘’ Kace; Yanzu Allah da ayoyinsa da kuma manzansa kuka kasance kuna izgili (da su)* Kada ku bada wani hanzari tabbas kun kafirce bayan imanin ku’’. Suratul Taubah, aya ta: 65-66.
اَلسَّابِعُ: اَلسِّحْرُ، وَمِنْهُ اَلصَّرْف وَالْعَطْفُ، فَمَنْ فَعَلَهُ أَوْ رَضِيَ بِهِ كَفَرَ. وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: ﴿ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِن أَحَدٍ حَتَّى يَقُولَا إِنَّمَا نَحنُ فِتنَة ﴾ البقرة: ١٠٢.
Na Bakwai: Asiri, kuma yana daga cikin nau’ukan asirin ‘Kautarwa’ wato a kautar da mutum daga abinda yake so yake bukata, kamar dauke hankalinsa daga ‘ya’yansa ko daga iyayansa ko daga mijinta ko daga matarsa. Haka kuma yana daga cikin nau’ukan sihiri ‘Kimsawa’ wato kimsawa mutum abinda bai so asa mishin son sa, to duk wanda ya aikata wannan ko ya yarda da shi to ya kafirta, dalili kuwa shine fadin Allah maigirma da daukaka: ‘’ Kuma basa koyawa kowa (sihiri) ballantana su ce abin sani kawai mu fitina ce kada ku kafirta’’. Suratul Bakarah, aya ta: 102.
اَلثَّامِنُ: مُظَاهَرَةُ اَلْمُشْرِكِينَ وَمُعَاوَنَتُهُمْ عَلَى اَلْمُسْلِمِينَ. وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى : ﴿ بَعضُهُم أَولِيَاءُ بَعض وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُم فَإِنَّهُ مِنهُم إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهدِي ٱلقَومَ ٱلظَّلِمِينَ٥١﴾ المائدة: ٥١.
Na Takwas: Taimakawa mushirikai da agaza musu akan musulmai, dalili kuma fadin Allah mai girma da daukaka: ‘’ Sashinsu masoyane ga sashi, duk kuma wanda ya jibincesu daga cikinku to lalle shi yana daga cikinsu, lalle Allah baya shiryar da mutanan da suke azzalimai’’. Suratul Ma’idah, aya ta: 51.
اَلتَّاسِعُ: مَنِ اَعْتَقَدَ أَنَّ بَعْضَ اَلنَّاسِ يَسَعُهُ اَلْخُرُوجُ عَنْ شَرِيعَةِ مُحَمَّدٍ ﷺ كَمَا وَسِعَ اَلْخَضِرُ اَلخْرَوُجُ عَنْ شَريِعَةِ مُوسَى ﷺ فَهُوَ كَافِرٌ.
Na Tara: Duk wanda ya kudurce cewa; yana yiwuwa ga wasu daga cikin mutane su fita daga shari’ar Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi), kamar yadda ya yiwu ga Khidr (Halliru) fita daga shar’ar Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) to wannan kafiri ne.
اَلْعَاشِرُ: اَلإِعْرَاضُ عَنْ دِينِ اَللهِ تَعَالَى، لاَ يَتَعَلَّمُهُ وَلاَ يَعْمَلُ بِهِ.
وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: ﴿وَمَن أَظلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بَِايَتِ رَبِّهِ ثُمَّ أَعرَضَ عَنهَا إِنَّا مِنَ ٱلمُجرِمِينَ مُنتَقِمُونَ٢٢﴾ السجدة: ٢٢.
وَلاَ فَرْقَ فِي جمِيعِ هَذِهِ اَلنَّوَاقِضِ بَيْنَ اَلْهَازِلِ وَالْجَادِ وَالخَائِفِ إِلاَّ اَلْمُكْرَهَ، وَكُلُّهَا مِنْ أَعَظَمِ مَا يَكُونُ خَطَرًا، وَمِنْ أَكْثَرِ مَا يَكُونُ وُقُوعًا فَيَنْبَغِي لِلْمُسْلِمِ أَنْ يحْذَرَهَا وَيَخَافَ مِنْهَا عَلَى نَفْسِهِ.
Na Goma: Kaudakai daga addinin Allah madaukakin sarki, (shi) baya koyo ba kuma ya aiki da abinda addini ya koyar, dalili kuwa fadin Allah madaukakin sarki: ‘’Ba wanda ya kai girman zalunci kamar wanda aka fadakar da shi da ayoyin Ubangijinsa sannan ya kaudakai daga barinsu. Lalle mu dangane da fandararru muke daukar fansa’’. Suratus Sajdah, aya ta: 22.
Anan ba banbanci akan dukkanin wadannan abubuwa tsakanin wanda ya yi su da wasa da kuma wanda yake da gaske da kuma mai tsoro saidai kawai wanda aka tilasta masa, dukkanin wadannan suna da matukar hadari, kuma suna cikin abinda ake yawan aukawa cikinsu, saboda haka ya kamata ga dukkanin mutum musulmi ya kiyayesu kuma ya ji tsoronsu akansa.
نَعُوذُ بِاللهِ مِنْ مُوجِبَاتِ غَضَبِهِ وَأَلِيمِ عِقَابِهِ.
وَصَلَّى اَللهُ عَلَى خَيْرِ خَلْقِهِ مُحَمَّدٍ وَآلِهِ وَصَحْبِهِ وَسَلَّمَ.
Muna neman tsarin Allah ya tsaremu daga abubuwan da suke haifar da fushinsa, da kuma zazzafar ukubarsa.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittarsa Annabi Muhammad da iyalanshi da kuma sahabbanshi.