الوصف
كتاب مترجم إلى لغة الهوسا، فيه بيان بعض أحكام الفقه بأسلوب سهل ميسر، مع بيان مكانة التراث الفقهي وتأصيل احترامه في نفـوس المسلمين.
DR. Salihu Ibnu Ghanim Assadalan.
Translator's name: Ibrahim Abdullah
Reviser's name: Aliyu Muhammad Sadisu.
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mabuwayi, tsarkkaken sarki. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyan halitta Annabin karshe Annabi Muhammad ﷺ, da alayensa da sahabban da kuma wadanda suka bi su da kyautatawa har ranar sakamako.
Wannan littafin mai suna Fikhul Muyyasar ya kunshi ibada da mua'amala a shari'ar musulunci ta hanya mai sauki. Ya fara tun daga tsarki har zuwa zamantakewa tsakanin al'ummah. Allah ya sa wa wannan aiki albarka, ya kuma sa iklasi a ciki, amin.
Ibrahim Abdullahi.
Minna, Nigeria.
Matsayin fikhu da girmansa a cikin zukatan musulmi.
Muhammancin matsayin fikhu.
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah shi kadai, tsira da aminci su tabbata ga Annabin da babu wani Annabi bayan shi, lalle yana daga cikin zance mai amfani mu kara tabbatar da cewa ilimin fikhu yana daga cikin mafi matsayin ilimomi addinin musulunci, da haka ne za mu gane cewa fikhu tushe ne da ya kasance musulmi yake auna aikin shi da shi, game da abin da aka halasta ko aka haramta, ingantacce ko batacce, kuma musulmai gaba daya suna kwadayi wajan neman sani halas da haram, ingantacce ya shafi alakar su da Allah ko bauta masa, na kusa ko na nesa, makiyi ko aboki, shugaba ko wanda ake shugabanta, musulmi ko wanda ba musulmi ba, kuma babu wata hanya ta sanin haka sai ta ilimin fikhu.
Wanda ke bincike game da hukuncin Allah akan bayi gaba daya, na umurni ko na zabi ko kuma wanda aka tilasta.
Lokacin da ilimin fikhu ya kasance daban daga sauran ilimomi, ya ta fadada ta hanyar anfani da shi, kuma muhimmancin shi ya ta girmama, da haka ya hada hanyoyin ci gaba da bunkasa kuma ya tattara abubuwan more rayuwa, sa'anan ya tabbatta shi mai tafiya da zamani ne, da haka ya hada hanyoyin ci gaba da bunkasa, sa'annan bunkasar ta sa ta tsaya ko ta kusa tsayawa, kodai da gangan ko kuma domin lalle shi ya nisanci barin dogaro ko riko da wani bangare na rayuwa (kamar yadda wasu suke ganin ya takaitune da tsarki da sallah, alhalin bah aka ba ne), domin neman sauyin na daular musulunci wanda aka sanya shi batare ba da al'adunsu da dabi'unsuba, tare kuma da sadar da shi akan abin mamaki da haskaka sai ya bata musu rayuwa, kuma ya sanya musu mishikiloli kuma da kwadayi don amfani da wannan ilimin ba tare da an yi ba, watsi da shi ba domin shi ne ilimin mai girma ba, sai don karfin ginshikin shi da kuma hukunce-hukuncen da ya ginu akai, wanda ba ya gushewa akan tubalin shi daram a tsawo lokaci mai tsawa.
Hakika Allah madaukakin sarki ya yi umurni game da wannan al'umma da su inganta fannin sa kuma su karantar da yadda za'a yi amfani da shi a karance da kuma a aikace.
Sai muka ga mafi yawan kungiyoyin musulunci suna ta kokarin komawa zuwa ga Shari'ar Allah, har ya zo ya kasance babu wata kungiya da zata yi amfani da wani tsari sai dai 'yan kadan wadanda suke ganin rayuwarta hade yake da rayuwarsa, kuma karuwar arzikinta hade ya da wanzuwarsa. Amma dai Allah zai bayyanar da addinin shi koda mushirikai sun ki.
Sai, ai yaushe aka fara amfani da fikhu? Menene sababin amfani da shi? Da me fikihu ya kebanta da me kuma ya yi fice? Meke zama wajibi akan musulmi wajan kokarin aiki da shi? Da bayanin kamar haka.
An fara amfani da fikhu ne a sannu-sannu a zamanin Annabi ﷺ da kuma lokacin sahabbai, kuma sababin amfani da shi tare da bayyana shi a farkon lokaci a tsakanin sahabbai shi ne, matsananciyar bukatar da mutane suke da ita na sanin hukunce-hukuncen sababbin wadanda suke ta aukuwa, da haka ne bukatuwar fikhu ta mamaye kowanne zamani, domin tsara alakar zaman-takewar mutane da kuma jawo abubuwan gyara da kuma kore abubuwa cutarwa, da barin barna kai tsaye tare da matsayin ilimin fikhu da abin da yake da shi.
Fikhu na musulunci ya sami banbanci ne da abubuwa masu kayatarwa masu yawa, da kuma muhimman abubuwa da ya kebanta da su, kamar haka:-
(1)Hakika tushansa shi ne wahayi ne na Allah: Haka fikihun musulunci ya banbanta ne, saboda tushen shi shine wahyin Allah ta'ala wanda yake gashi a cikin Alkur'ani da Hadisin Annabi ﷺ, saboda wannan duk mai ijitihadi ya takaita istinbadi (fitar da hukunce-hukunce,) shi ne akan wadannan tushen abu biyu, (wato Alkur'ani da Hadisi), da abin da yake zama rasa daga garesu kai tsaye, da kuma abinda ke nuni zuwa ga ruhun Shari'ah, da manufarta baki daya, da cika ka'idodin ta, da samar da ainihin sako a cikin lokacin manzanci, da bayan daukewar wahayi daga Annabi ﷺ. Allah madaukakin sarki ya ce:
﴿ الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا فَمَنِ اضْطُرَّ فِي مَخْمَصَةٍ غَيْرَ مُتَجَانِفٍ لِإِثْمٍ فَإِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَحِيمٌ٣﴾
Ma'ana: “A yau na cika muku addininku, kuma na cika muku ni'imata, kuma na yardar muku da musulunci shi ne addini". (Ma'idah, aya ta: 3).
Bayan haka babu wani abinda ya rage saida aka tabbatar da shi a aikace, da kuma inganta rayuwa wacce aka ginata akan manufofin Shari'ah.
(2) Kasancewarsa ya mamaye dukkan abinda rayuwa ke bukata.
Fikhul islami ya ban-banta ne da sauran ilimi saboda lalle ya kunshi alakoki uku na mutum;
(a) Alakar mutum da Ubanijin shi.
(b) Alakar mutum da shi kanshi.
(c) Alakar mutum da zamantakewar shi.
Domin shi musulunci addinine na rayuwar duniya da lahira, kuma shi addinine kuma tsarin gudanar da kasa ne, haka kuma addini ne na mutane bakidayansu har zuwa ranar kiyama, dukkan abin da ke cikin fikihun musulunci Akidah da Ibada da rayuwa da ma'amala, domin tabbatar da abubuwan boye da na sarari da girmama hakkoki wajan samun yarda, natuswa, imani, rabo, da neman tabbata akan haka, tare da kuma tsarin rayuwa kebantattu ko gaba-daya, don samun rabon ilimi dukkanin shi baki daya.
Kuma saboda wannan manufa, hukuncin aiki da fikhu na musulunci shi ne wanda rataya ga abinda ake dorawa baligi na zance da ayukka da akidodi da kuma gamammiyar hanya wacce ta rabu gids biyu:
NA DAYA: Hukunce-hukuncen Ibadah: Na abinda ya shafi tsarki, sallah, azumi, hajji zakka, alwashi, rantsuwa da makamantan haka. Na daga cikin abinda ake nufi da shi na alakar mutum da Ubangijinsa.
NA BIYU: Hukunce-hukuncen ma'amala na kuduri, da ayyuka da ukuba da hukunci da kuma abinda ake nufi da shi na tsarin alakar mutane sashinsu da sashi, shin ya kasance shi kadai ne ko a kungiyance ne, kuma wannan hukunci ya rabu kamar haka.
(a) Hukunce-hukuncen da a yu ake kiransu 'Zamantakewa a rayuwar mutum' sune hukunce-hukuncen iyali na abinda yake kasancewa tun farkon kafuwar gida har zuwa karshe, kamar aure, saki, dangantaka, ciyarwa da gado. Kuma anan ana nufin samun tsarin rayuwa dake kullawa tsakanin ma'aurata, da kuma 'yan'uwa sashi da shi.
(b) Hukunce-hukuncen Zaman Tare: shi ne abin da rataya da daidaikun mutane, da kuma canje-canje kamar hurda ta cinikayya da kodago da jingina raino da da hulda a matsayin kamfani da bashi da cika abinda yake dole. Anan ana nufin tsara alakar dukiyar daidaikun mutane da kuma hakokinsu.
(c) Hukunce-hukuncen Manyan Laifuka: Shi ne kuma abun da ya ta'allaka daga abun da mukallafi (wanda aka dorawa hukunce-hukuncen shari'a), na laifuka, da kuma abinda ya cancanta ayi masa na hukunci. Kuma anan ana nufin tsare rayuwa mutanene da dukiyoyinsu da kuma mutuncin su da hakkokinsu, da kuma iyakance alakar mai laifi da wanda aka yi wa laifi da sauran al'umma, kana da tabbatar da aminci.
(d) Hukunce-hukuncen Shigar Da Kara ko na zaman tare ko manyan laifuka, shi ne wanda ya ta'allaka da hukunci da kai kara da hanyoyin bi wurin tabbatar da shaidu da ranstuwa, da wadansu alamu da kan iya zama shaida. Kuma wadannan su ake nufi don kawo tsarin tabbatar da adlci a tsakanin al'umma.
(e) Hukunce-hukuncen Tsarin Mulki; Shi ya ta'allaka ne da tsarin mulki da tushen shi. Wannan shi ne ke bayyana alakar shugabanni da wadanda ake shugabanta, tare da tabbatar da hakkokin daidaikun mutane da kongiyoyi, da kuma abun da yake zama wajibi akan su.
(h) Hukunce-hukuncen Kasa-Da-Kasa; Shi ne wanda ke da alaka da tsarin kasar musulunci da wasu kasashen, a halin zaman lafiya ko na yaki, da kuma alakar wadanda ba musulmai ba masu zama a kasar musulmi, wannan kuwa ya kunshi jihadi da yarjeniyoyi. Wannan yana nufin fayyace nau'in alaka da taimakekeniya da kuma girmamawa wanda ke kasancewa a tsakanin kasashe.
(i) Hukunce-hukuncen da suka ta'allaka da Tattalin arziki Da Kuma Dukiya; Shi ne wanda ya ta'allaka da hakkokin daidaiku dukiya da kuma abin da ya lizimcesu wajan tsarin dukiya, ta wajan bada hakkin kasa da kuma abin dake zama wajibi akanta kasar, da tsarin abinda ke shiga “Baitulmali" da kuma abinda ake kashewa.
Wannan shi yake nufin tsara alakar dukiya tsakanin mawadata da talakawa, haka kuma tsakanin kasa da daidaikun mutane.
Gaba daya abunda muka ambata sun kunshi dukiyar kasa ta gaba-daya da kuma wadda aka kebance; Kamar ganimomi da anfali da tsarin daya cikin 10 (na jami'an kwastam), da harajin kasa, da ma'adinan kasa daskararru (karma gwal) da masu ruwa (kamar fetur, kalanzir …) da kuma abubuwa na dabi'a da Allah ya halitta (kamar kifi….). Da kuma dukiyoyin al'umma ta zaman tare; kamar zakka, sadaka, da alwashi, rance. Da kuma dukiyar iyali; kamar ciyarwa, gado, wasiyyah, da kuma dukiyar daidaikun mutane kamar; ribar da ake samu a kasuwanci, ladan aiki (kwadago), da kamfaninoni da duk abin da suke na halal. Haka kuma ukubar dukiya kamar; Kaffara, Diyya da kuma Fannssa (fidya).
(j) Dabi'u Nagari da kuma Ladubba; Shi ne abun da ke kara kulla alakar zamantakewar mutane da kuma kyawawan dabi'u da taimakon juna da kuma tausayi tsakanin mutane.
Kuma sababin da ya sa fikhu ya fadada shi ne abin da ya zo a cikin Hadisan Annabi ﷺ masu tarin yawa, a kan ire-iren wadannan babi-babi.
(3) Na daga cikin abunda yake bayyana ilimin Fikfu na Musulunci yadda ya siffantu da da bayyana halas da haram.
Ilimin fikihu ya bam-banta da sauran dokokin da mutane suka dorawa kawunan su, ta yadda dukkan wani aiki ko motsi a kicin al'umma na mu'amalar yau da kullum to siffantu da wata babbar ka'ida akan halas ko haram akan sa ta yadda yake nuni akan siffantuwar hukunce-hukuncen mu'amala (zamantakewa) ya kasu kashi biyu:
1. Aikin duniya abinda yake a bayyane ko wanda ake da wani tasarrufi a ckin, wanda baida alaka da w abo yayyan umarni (wato hukuncin alkali), domin alkali yana amfani da hukunci ne game da abinda da yake da iko kai.
Kuma hukuncin shi baya sanya bunda karya ne ya zama gaskiya, kuma baya mayar da gaskiya ta zama karya a asalin yadda abun yake, haka kuma ba ya halasta haram, kuma ba ya haramta halal a asalin yadda suke. Sa'annan abin da yake hukunci ne to shi dole ne sabanin fatawah.
2. Hukunci na lahira yana ginuwa ne akan hakikanin yadda abu yake faruwa ne, ko da ya kasance ya boyu ne ga sauran mutane, wanda yake aikatawa tsakanin shi da Ubangijin shi, wannan kuwa shi ne hukuncin addini, kuma shi ne abnda mai fatawa zai dogara da shi a fatawar shi.
4. Na daga cikin abunda Fikuhun Musulunci ya yi fice akan shi; shi ne yadda yake damfare da kyawawan dabi'u.
Fikhu ya saba daga sauran dokokin kasa, wajan tasirantuwa da ka'idojin zamantakewa na gari, dokokin kasa ba su da wata manufa saidai kawai amfanuwa, wato aiki domin kare dokoki da kuma kiyaye zamantakewa, koda ka jera shi da wasu daidaikun abubuwa da ya fara karantarwa, da kuma karantar da kyawawan halaye.
Saidai shi wannan Fikhun yana kokarin mutunci da kyakkywar siffa da dabi'un da suke daidaitattu, saboda haka aka shar'anta ibada domi tsarkake zuciya da nisantar da ita daga abubun ki, kuma aka haramta riba da nufin yada ruhin taimako da tausayi tsakanin mutane, da kuma tsare mabukata wajan banbadannci ga ma'abota dukiya, aka kuma hana yaudara da algusu a alkawura da cin dukiya ta hanyar karya. Aka kuma shar'anta bata ciniki da sababin jahiltar kayan sayarwa, da makamantan su ta hanyoyin da suke cin karo da yarda, wadanda suke aibi ne ga yarda (da yake sharadine a kasuwanci), domin tabbatar da soyayya da bayyana gamsuwa da mutum, da kuma hana jayayya tsakanin mutane, da kamewa daga barin fadawa laifi da girmama hakkokin sauran mutane.
Idan addini da dabi'u suka kankama kuma ga kyakkyawar mu'amala, to za'a sami tabbatuwar gyaran daidaikun mutane da kuma al'umma kuma za'a rabauta baki daya, da kuma samar da hanyar shiga aljannah mai ni'ima a lahira, da haka ne babbar manufan fikhu ita ce rabauta a yanzu da nan gaba, da kuma samun tsira a duniya da lahira.
Da haka ne fikhu ya zama abunda ya yi daidai da kowanne zamani, kuma ya dace ayi aiki da shi har'abada. Saboda haka fikhun sanin ka'idodi na asali ba ya canzawa kamar yadda yarda a ciknikayya, da kuma biyan cutarwa da hana barna da kare hakkoki, da kuma nauyin da yake kanka ba sa canzawa. Amma shi fikhu da ake ginawa akan kiyasi da kuma lura maslahohi da al'adun mutane (da ba su sabawa musulunci ba) to yana bkarbar canji da habbaka gwargwadon bukatar hakan da kuma zamani, da abunda yake alherine ga dan'adam da wurare mabanbanta matukar hukunci ya kasancene akan mahanga ta Shari'ah da ingantattun asalinta.
Wannan kuma yana tabbatane a cikin halin tafiyar da rayuwa ( wato mu'amala), ba'a cikin akida ba da kuma ibada ba, wannan kuma shi ne abin nufi da ka'idar da take cewa: “Hukunce-hukunce na canzawa ne da sauyin zamani".
Kenan aiki da fikhu wajibi ne dole:
Na'am, haka ne kan;
Domin mujtahidi yana aiki ne da abinda zai taimaka mishi ga ijtihadin sa, kuma shi ne abinda yake a gare shi hukuncin Allah Ta'ala ne, haka kuma wanda ba mujtahadi ba ne dole ya yi aiki da fatawar mujitahidi, domin ba shi da wata hanya ta daban domin sanin hukuncin Shari'ah in banda neman fatawa:
﴿ فَاسْأَلُوا أَهْلَ الذِّكْرِ إِنْ كُنْتُمْ لَا تَعْلَمُونَ٧﴾
Ma'ana: “Ku tambayi ma'abota zikiri (sani) in kun kasance ba ku sani ba". (Anbiya, aya ta: 7).
Musanta wani hukunci daga cikin hukunce-hukunce Shari'ah wanda ya tabbata garau, ko kuma ganin wani hukunci ya yi tsanani misali kamar haddi, ko da'awar cewa Shari'ah ba ta dace ba a yi aiki da ita a wanna zamanin to wannan riddance kuma fita ne daga musulunci.
Amma musanta wasu hukunce-hukunce da suka tabbata ta hanyar ijitihadi akan mafi rinjaye zato, to wanna laifi ne kuma zalunci ne (mutum ya zalinci kan shi), domin mujitihidi ya sanya dukkanin kokarin shi wajan sanin hakikanin gaskiya, da kuma bayanin hukuncin Allah Ta'ala, nesa da son zuciya irin ta mutum, ko wani amfani na daban, ko kuma neman a san shi ko don ya shahara. Abun sani dai madogararsa ita ce dalili na Shari'ah, kuma jagoransa ita ce gaskiya, sa'annan taken sa kuma shi ne amana da gaskiya da yi domin Allah.
Mawallafi.
Dr. Salihu Ibnu Ganim.
Ya kumshi abubuwa kamar haka:
1. Tsarki.
2. Sallah.
3. Zakkah.
4. Azumi.
5. Aikin hajji.
6. Layya da yanka na suna.
7. Jihadi.
Rukuni na daya daga cikin rukunnan musulunci shi ne: Tsarki.
Ma'anar tsarki a yaren larabci da malamman fikhu.
Tsarki a yare shi ne: Tsafta da tsarkakewa
A wajan malamman fikhu shi ne: Gusar da abunda ya taba jiki wanda ke hana sallah da sauransu.
Nau'in Ruwa: Ruwa nada nau'i uku, su ne;
NA DAYA: Ruwa mai tsarkakewa shi ne kuma wanda ya tabbata akan sifarsa wadda aka halicce da ita, kuma shi ne wanda ke dauke hadasi ya kuma gusar da najasa, wadda ta yadu a wuri mai tsarki, Allah Ta'ala ya ce:
﴿ وَيُنَزِّلُ عَلَيْكُمْ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً لِيُطَهِّرَكُمْ ١١﴾
Ma'ana: “Kuma yana saukar wa a gareku daga sama ruwa domin ya tsarkake ku da shi". (Anfal:11).
NA BIYU: Ruwa mai tsarki, shi ne wanda ya gauraya a kalarsa ko a dandanon sa, ko kamshin sa da duk abun da ba najasa ba, kuma shi ne ruwa mai tsarki akaran-kansa, saidai shi baya gusar da hadasi, domin gaurayar da ya yi na siffa daga cikin siffofin sa.
NA UKU: Ruwa mai najasa, shi ne wanda ya gauraye da najasa kadan ko mai yawa.
- Ana iya tsarkake ruwa mai najasa ta hanyar cire najasar da ta gauraya da shi, ko zuba ruwa a ciki domin gusar da ruwa mai najasa.
- Idan mutum musulmi ya yi kokwanto game da ruwa, mai najasa ne ko mai tsarki ne, to zai yi gini akan yakini ne, kuma shi ne asalin abunda ya tabbata na tsarkin ruwa.
- Idan wani abu ya yi kama da abunda ya halatta ayi tsarki da shi da wanda bai halatta ba, to sai abarshi, sai ayi taimama.
- Idan tufafi ya yi kama da mai najasa ko abunda ya haramta, sai ayi gini akan yakini, sai mutum ya yi sallah guda daya da shi.
NAU'UKAN TSARKI.
Tsarki kashi biyu ne; Ma'anawiyya da Hissiyyah.
Ma'anawiyya: Shi ne tsarkin zuciya, daga cututtukan zunubi. Shi kuma Hissiyya shi ne wanda ake aikatawa da nufin yin sallah a zahirance, yana da nau'i biyu:
Tsarkin Hadasi da kuma Tsarkin Khabasi.
Tsarkin Hadasi ya kasu kashi uku ne: Akwai babba, shi ne wanka. Akwai kuma karami shi ne alwala. Canji wadannan (wato na uku kenan), game da abinda ya yi tsananta wajan samun ruwa shi ne kuma Taimama.
Tsarkin Khabasi uku ne: Akwai wankewa, shafawa, yayyafawa.
(Abinda za'a yi alwala ko wanka da shi).
A yaran larabci kwanuka jam'i ne na kwano: kwanukan abinci da sha, gamamman jam'i da ake cewa: Awani, azarfu.
Malaman Fikhu ba sa fita daga barin amfanin da wannan lafuza na yare.
Nau'un kwanukka.
Idan muka dubi zatin su kwanukan, nau'ukan su za su kasance ne kamar haka:
1. Kwanukan zinari da azurfa.
2. Kwanukan tangaran.
3. Kwanukan haloko.
4. Kwanuka wadanda ake amfani da su ta wasu hanyoyi.
5. Kwanukan fata.
6. Kwanukan kashi.
7. Kwanukan kamar na roba, ita ce (akushi), tasa da wasu kwanuka na al'ada.
Hukuncin Shari'ah game da kwanuka: Ko wanne kwano mai tsarki ne, ya kasance mai tsada ne ko mara tsada ne, wanda aka halasta aiki da shi, saidai kwanukan zinari da na azurfa da wadanda suke biye da su, kamar yadda huzaifa ya ruwaito gada Annabi (ﷺ) ya ce:
“Kar ku sha a cikin kwanukan azurfa da zinare, haka kuma kar ku ci a cikinsu, domin na su ne a duniya, ku kuma na ku yana lahira". (Bukhari da Muslim suka ruwaito).
Kuma duk abinda aka haramta amfani da shi kamar; ganga da jita to an haramta daukar shi, kuma hanin da aka yi ya game mata da maza saboda gamewar Hadisin. Kuma babu abin da yake zama najasa akan kokwanto matukar ba'asan najasarshi ba akan yakini, domin asali shi ne tsarki.
Kanukan wadanda ba musulmi ba.
1. Kwanukan ma'abota littafi (Wato Yahudu da Nasara).
2. Kwanukan mushirikai.
Hukuncin wadannan a shari'ah halas ne a yi amfani da su matukar tsarkin su ya tabbata, domin asali shi ne tsarki.
- Tufafin wanda ba musulmi ba mai tsarki ne matukar najasar sa ba ta tabbata ba.
- Ana tsarkake fatar dabba wadda ake ci ta hanyar hanyar jima.
- Duk abinda aka cire daga jikin rayayye to matacce ne (mushe ne, wato najasane), amma kumba, gashi, hakori na abun da aka cire daga jikin rayayye mai tsarki ne.
- An sunnanta a rufe kwanuka da randa, domin Hadisin Jabir t ya ce: “Lalle Annabi (ﷺ) ya ce “Ka rufe randarka ka ambaci sunan Allah, ka lullube kwanukannka ka ambaci sunan Allah, ko da zaka gitta masa da sanda ne". (Bukhari da Muslim).
- Istinja'u shi ne gusar da abinda ke fita daga mafitan nan biyu (ta gaba da ta baya) da ruwa.
- Istijmaru shi ne gusar da abinda ke fita daga mafita biyu da dutse ko ganye da makamantan su.
- Anso lokacin shiga bandaki a gabatar da kafar hagu, sai a ce:
بِسْمِ اَللهِ، اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ اَلْخُبُثِ وَالْخَبَائِثِ.
Ma'na: “Da sunan Allah, ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidanun aljannu maza da mata".
- Anso lokacin fitowa sai a gabatar da kafar dama, sai a ce:
غُفْرَانَكَ، اَلْحَمْدُ للهِ اَلَّذِي أَذْهَبَ عَنِّى اَلأَذَى وَعَافَانِي.
Ma'ana: “Ina neman gafararka ya Allah, godiya ta tabbata ga Allah wanda ya tafiyar mun da cuta kuma ya bani lafiya".
- An so ga wanda zai biya bukata ya dogara akan kafarsa ta hagu, kuma in ya kasance a fili ne to an so ya nisanci idon mutane, ya yi sutura ya kange kansa a wani wuri domin yin fitsari, don kar ya samu najasa a tufafin shi ko jikin shi.
- An hana masa shiga bandaki da wani abunda akwai sunan Allah a jikin shi, saidai in bukata ta kama, haka kuma an hana ya da tufafinsa kafin ya duka wato tun yana tsaye, da Magana a cikin bandaki, da fitsari a rami, da kuma rike al'aurarsa da hannun dama, haka ma yin istijmar da shi.
- An haramta masa fuskantar alkibla da juya mata baya a lokacin biyan bukata, amma yana halasta idan a cikin makewayi ne, saidai kauracewa fuskantar alkiblar ko a makewayi ne ya fi.
- An haramta masa yin fitsari da bayan-gida akan hanya, da inuwa mai amfanarwa, da saman bishiya mai kayan marmari da makamantan haka.
- An so ya yi istijmaru da dutse mai tsarki guda uku masu tsarkakewa, idan ba su tsarkake ba sai ya kara, kuma an so sunnan ta yin amfani da su akan wutiri uku ko biyar da makamantan haka.
- An haramta yin istijmar da kashi, da abinci da abu mai alfarma, (kamar kudi …), kuma ya halasta a gusar da abunda ya fito daga mafita biyu da ruwa, kyalle, da ganye, kuma hadda dutse, saidai a hada ruwa da wanin cikinsu ya fi falala akan amfani da ruwa kadai.
- Ya wajaba a wanke tufafi da ruwa, in kuma wurin ya baci sai a wanke tufafin duka.
- Yana daga cikin sunnah mutum ya yi fitsari a tsugunne, amma ba'a karhanta mishi yi a tsaye ba, in ya aminta daga watsuwar fitsari.
a. Ma'anar fitri: Shi ne hanya mikakkiya kuma dabi'a fararriya. Fitr: Shi ne abunda ya wajaba mutum ya kasance rayuwarsa ta tafi a kai.
b. Daga cikin sunanul fitri.
1. Asuwaki: Shi ne sunnah a kowane lokaci, tsarki ne ga baki abun yarda ne kuma ga Ubangiji, amfi karfafa yin asuwaki a wurin alwala da sallah da karatun Alkur'ani, da shiga masallaci da gida da kuma lokacin farkawa daga bacci da kuma yayin canjin kanshin baki.
2. Askin: Gashin gaba, tsige gashin hammata, yanke kumba da kuma wanke kogunan gabbai.
3. Aske: Gashin baki, cika gemu da tsefewa.
4. Wanke gashin kai, shafa masa mai da tsefe shi. A karhanta yin KAZA'ﷻ wato aske wani sashin kai kuma a bar wani sashin, domin haka yana kama da canza halitta.
5. Sanya turare na almiski ko waninsa.
6. Kaciya: Ita ce yanke fatar da ta rufe kan azzakari, domin kar fitsari da dauda su taru a cikin shi, wannan ga namiji kenan. Amma kaciyar mace ita ce yanke wani bangare na fatar da ke saman farjinta, domin samun wajan shigar azzakari, shi kuma yana kama da tozon zakara, likitoci masu kaciya ne suka san haka, ita kaciya tsarki ce kuma tsafta ce ga maza tana da falla mai yawa, daga sunnah ce ga namiji, kuma girmamawa ce ga mace.
(a) Ma'anar alwala; Ita ce amfani da ruwa mai tsarki akan gabobi huda akan kuma wata siffa kebantacciya a Shari'ah'.
(b) Falalar alwala: Abin da aka ruwaito daga Annabi (ﷺ) yana nuna falalar alwala hakika ya ce; “Babu daya daga cikinku da zai yi alwala ya kuma kyautata alwalarsa sa'annan ya ce; “Ina shaida babu abin bauta wa da cancanta sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, kuma ina shida wa lalle Annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne, take an bude masa kofofin aljannah guda bakwai ya shiga ta inda ya keso". (Muslim ya ruwaito).
Abun nufi da kyautata alwala a gabbai shi ne, yin amfani da ruwa ba tare da barna ba, wanda hakan yake tabbatarwa masu yin haka su kasance masu hasken fuska da gabubuwa masu walkiya ranar kiyama, akan fadin Manzon Allah (ﷺ) cewa: “Lalle al'ummata za su zo ranar tashin alkiyama suna masu hasken fuska, da walkiyar gabbai na daga alamar alwala, saboda haka duk wanda ya samu ikon tsawaita hasken sa sai ya aikata". (Bukhari da Muslim).
(a) Sharuddan alwala guda goma ne:
1. Musulunci.
2. Hankal.
3. Wayo.
4. Niyya, tare da kyautata hukuncinta tare da niyyar ba zai yanke ta ba har sai ya kammala alwalar.
5. Daukewar abunda ke hana alwala (Jinin al'ada da jinin biki).
6. Istinja'u ko istijmaru.
7. Ruwan ya kasance mai tsalki.
8. Ruwan ya kasance na halsta.
9. Gusar da abunda zai hana shigar ruwan fata.
10. Shigar lokaci ga wanda ke da hadasi a kowani lokaci.
(b) Abubuwanda ke wajabta alwala. Abunda ke wajabta shi ne samuwar hadasi.
(c) Farillan arwala. Farillan alwala shida ne.
1. Wanke fuska da baki da hanci wadanda ke furkar.
2. Wanke hannaye zuwa guiwar hannu.
3. Shafar kai tare da kunne.
4. Wanke kafafuwa.
Allah madau ya ce:
﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا قُمْتُمْ إِلَى الصَّلَاةِ فَاغْسِلُوا وُجُوهَكُمْ وَأَيْدِيَكُمْ إِلَى الْمَرَافِقِ وَامْسَحُوا بِرُءُوسِكُمْ وَأَرْجُلَكُمْ إِلَى الْكَعْبَيْنِ وَإِنْ كُنْتُمْ جُنُبًا فَاطَّهَّرُوا وَإِنْ كُنْتُمْ مَرْضَى أَوْ عَلَى سَفَرٍ أَوْ جَاءَ أَحَدٌ مِنْكُمْ مِنَ الْغَائِطِ أَوْ لَامَسْتُمُ النِّسَاءَ فَلَمْ تَجِدُوا مَاءً فَتَيَمَّمُوا صَعِيدًا طَيِّبًا فَامْسَحُوا بِوُجُوهِكُمْ وَأَيْدِيكُمْ مِنْهُ مَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيَجْعَلَ عَلَيْكُمْ مِنْ حَرَجٍ وَلَكِنْ يُرِيدُ لِيُطَهِّرَكُمْ وَلِيُتِمَّ نِعْمَتَهُ عَلَيْكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ٦﴾
Ma'ana: “Ya ku wadanda sukayi Imani! Idan kun tashi za ku yi sallah, to sai ku wanke fuskokinku da hannaye zuwa guiwar hannu, kuma ku shafi kawunanku da kafafuwa zuwa idon sawu". (Ma'idah:5).
5. Jerantawa, domin Allah maigirma da daukaka ya sanya jerantawar hakan sai ya sanya shafa tsakanin wankewa.
6. Jerantawa kamar yadda Annabi ﷺ ya aikata.
(d) SUNNONIN ALWALA.
Daga cikin sunnonin alwala akwai;
1. Asuwaki
2. Wanke tafin hannu sau uku.
3. Kurkurar baki da shaka ruwa.
4. Tsefe gemu mai yawa da yatsun hannu da kafafuwa.
5. Damantarwa. (fara gabatar da dama).
6. Wanki na biyu da na uku. (idan na farko ya game).
7. Debo ruwa domin wanke kunne.
8. Addu'ah bayan alwala.
9. Sallar nafila raka'a biyu bayan ta.
(e) Daga cikin makaruhan alwala.
1. Yin alwala a wurin da ba shi da tsarki, domin tsoron abinda k iya taba jikinsa na najasa.
2. Kari akan wanki uku, domin abinda aka ruwaito lalle Annabi ﷺ ya yi alwala sau uku-uku ne, sai ya ce duk wanda ya yi kari hakika ya munana, kuma ya yi zalunci. (Nasa'i ne ya ruwaito).
3. Barna da ruwa wajan alwala, ka tuna lokacin da Annabi ﷺ ya yi alwala da mudin Nabiyy, shi ne kuma kanfatar hannu. Barna aba ce da aka hana a komai.
4. Barin sunnah daya ko fiye da haka, daga cikin sunnonin alwala, lalle kuma barinta rashin lada ne, kuma bai kamata ba ya bari lada ya wuce shi.
(f) Abubuwanda ke warware alwala. Abubuwa masu warware alwala bakwai ne;
1. Abubuwan dake fitowa daga mafita biyu (ta gaba ko ta dubura).
2. Abinda ke fitowa daga sauran jiki.
3. Gushewar hankali ta hauka ko farfadiya ko maye.
4. Shafar azzakarin mutum ko shafar gaban mace ba tare da shamaki ba.
5. Namiji ya shafi mace domin jin sha'awah ko mace ta yi hakan.
6. Cin naman rakumi.
7. Duk abunda ke wajabta wanka yana wajabta alwala, kamar shiga musulunci da fitowar maniyyi da makamancin haka, saidai mutuwa lalle shi yana wajabta wanka ne banda alwala.
(a) Ma'anar wanka; A yare da kuma wurin mallaman fikhu, Alghuslu (غُسل) da wasalin dumma ruwan da ake wanka da shi ne, amma da wasalin fataha (غَسل) aiki ne (wato yin wankan) da wasalin kasra (غِسل) kuma shi ne darasin mu, watau tsarkakewa.
Ma'anar shi a shari'ah: shi ne zuba ruwa a dukkan jiki, daga tsakiyar kai har zuwa kasan diddige da ruwa mai tsarki akan sifa kebantacciya. Mace da namiji wajan siffar wankan su dayane, saidai ga mace a lokacin da take wankan daukewar jinin al'ada ko na biki, to yana kamata a gare ta da ta wanke alamar jinin domin tsarkaketa da kuma kauda warin jinin.
(b) Abubuwan dake wajabta wanka. Abubuwan dake wajabta wanka guda shida ne:-
1. Fitar maniyyi kai tsaye, ta hanyar jin dadi daga mace ko namiji.
2. Boyewar kan azzkari a cikin farji.
3. Idan mutum ya mutu ya wajaba ayi masa wanka, saidai in shahidi ne.
4. Musuluntar kafiri ko wanda ya yi ridda.
5. Jinin al'ada.
6. Jinin biki (wato jinin haihuwa).
(c) Daga cikin wankan da suke an so a yi su a musulunci.
1. Wankan jumu'ah.
2. Wankan shiga harami (da hajji ko da umarah).
3. Wanka ga wanda ya yi wa mamaci wanka.
4. Wankan idi biyu (na zuwa karamar sallah da babbar sallah).
5. Idan mutum ya farfado daga hauka ko farfadiya.
6. Wankan shiga Makkah.
7. Wanka domin sallar kisfewar wata ko kuma rokon ruwa.
8. Wanka na mai istiha a kowacce sallah.
9. Ga kowanne jima'i an so a yi wanka.
(d) Sharuddan wanka:
1. Daukewar abinda ke wajabta wanka, (kamar al'ada…).
2. Niyya.
3. Musulunci.
4. Hankali.
5. Wayo.
6. Ruwa mai tsarki kuma halstacce.
7. Gusar da abunda ke hana shigar ruwa zuwa ga fatar jiki.
(e) Wajiban wanka:
Wajiban wanka su ne yin Basmalah, an dauke wa mutum idan ya manta, amma ba'a barinta da gangan ba.
(f) Farillan wanka:
Niyya, da game jiki da ruwa gabadaya, da cikin bakin sa, da hancin sa, amma yana wadatar da shi kan mafi galibin zato. Duk wanda ya yi niyyar wanka na Sunnah ko wajibi, to daya daga cikin su ya wadatar da shi akan dayan, (kamar wankan janaba ya wadatar da na juma'a).
Wanka daya ya wadatar ga mai al'ada da janaba lokacin da ta yi niyya daya.
(g) Sunnonin wanka:
1. Basmallah (wato fadin:بسم الله ).
2. Farawa da wanke kazanta.
3. Wanke tafukan hannu.
4. Alwala kafin wanka.
5. Damantarwa.
6. Jerantawa.
7. Goga hannu a sauran jiki, (cuccudawa).
8. Mai-maita wanke kafafuwa a wuri na daban.
(h) Makaruhan wanka:
1. Barnata ruwa.
2. Wanka a wuri a wuri mai najasa.
3. Wanka ba tare da wani shamaki ba ko wani abu makamancin haka.
4. Wanka a ruwa mai gudana.
(i) Abubuwan da ke haramta ga mai janaba. An haramta mishi;
1. Sallah.
2. Dawafi.
3. Daukar Alkur'ani ko shafashi, sai dai in bango ne.
4. Zama a masallaci
5. Karatun Alkur'ani.
(a) Ma'anarta a yaran Larabci da kuma shari'ah.
Najasa a yaran Larabci ita ce; Kazanta, kuma abu mai najasa kazanta ne, wannan abun ya zama najasa kuma ya gauraya da najasa.
Ita najasa a mahangar Shari'ah aba ce wadda aka kaddara, tana hana jiki yin sallah kamar fitsari, jini da giya.
(b) Nau'ukan najasa biyu ne;
I. Ayyana (Bayyananniya).
II. Hukmiyya, (wato a hukunce).
- Ayyana: Ita ce abinda yake shi karankanshi najasa ne, kamar kare da alade. Wanda ba'a tsarkaketa da wankewa a wannan halin.
- Hukmiyya: Najasa ce wacce ta afkawa wuri mai tsarki.
(c) Rabe-raben Najasa:- Najasa ta rabu kashi uku.
1. Kashin da yake an yi ittifakin najasar sa.
2. Kashin da yake an yi sabani akan najasarta.
3. Kashin da yake najasar ne amma an yi afuwa akai.
1. Kashin da yake an yi ittifakin najasar sa.
1. Mataccan duk abinda yake rayuwa a bayan kasa. Amma wanda ke rayuwa a ruwa to mai tsarki ne kuma halal ne.
2. Jinin yanka, wato wanda ya kwarara a lokacin da ake yanka dabbar da take mai rayuwace a bayan kasa.
3. Naman alade.
4. Fitsarin mutum.
5. Kashin mutum.
6. Maziyyi.
7. Wadiyyi.
8. Naman abinda bai halatta a ci ba cikin dabbobi.
9. Da abunda aka yanke ko aka cire daga jikin dabbar tana lokacin tana raye.
10. Jinin al'ada.
11. Jinin haihuwa. (wato jinin biki).
12. Jinin istihala. (wato jinin cuta, wanda ba na al'ada ba, ba kuma na biki ba).
2. Kashin da yake an yi sabani akan najasarta.
1. Fitsarin dabbar da ake cin naman ta.
2. Kashin dabbar da ake cin naman ta.
3. Maniyyi.
4. Yawun kare.
5. Amai.
6. Mataccan abun da ba shi da jini a cikinsa, kamar zuma, kenkyaso, da kudin cizo da kuma makamantan su.
3. Kashin da yake najasar ne amma an yi afuwa akai.
1. Ruwan dagwalon kan hanya.
2. Jinin da yake kadan.
3. Jini da ruwan kurji na mutum ko dabba, wacce ake cin naman ta.
(d) Yadda ake tsarkake najasa.
Tsarkake najasa yana tabbata ne da wanke ta, ko yayyafa ruwa, ko kuma cudawa da shafawa.
* Tsarkake tufafi mai najasa; Idan najasar ta kasance ta daskare to sai a kankareta sannan a wanketa, idan kuma danya ce sai a wanke kawai.
* Tsarkake fitsarin yaro: Ana tsarkake fitsarin yaro ne ta hanyar yayyafa masa ruwa, idan bai fara cin abinci ba. Ana tsarkake najasa dake akan kasa, ta hanyar gusar da ita, sai azuba ruwa akan najasar. Kuma ana tsarkake takalmi ta hanyar goge shi a kasa ko da tafiya a wuri mai tsarki, kuma ana tsarkake abubuwa kamar kwalba, wukake da ire-iren su ta hanyar gogesu, kuma idan kare ya yi lallago (wato ya sa baki) a kwarya ana wankewa ta ne sau bakwai daya daga ciki za asa turbaya.
1. Ma'anarta, a harshen Larabci da kuma Shari'ah.
a. Ma'anarta, a harshen Larabci, shi ne: Nufi da dogara.
b. Ma'anarta, a Shari'ah; shafar fuska da hannuwa da turbaya mai tsarki akan a siffa kebantacciya. Kuma yana daga cikin abun da Allah ya kebanci wannan al'umma da shi, wato madadin amfani da ruwa.
2. Wanda aka yardar wa ya yi Taimama?.
1. Rashin ruwa ko nisansa.
2. Idan mutum yana da ciwo ko rashin lafiya, kuma yana tsoron cutarwa idan ya yi amfani da ruwa.
3. Idan ruwa ya kasance mai sanyi sosai kuma bai samu abun da zafafa shi ba, (wato zai dunduma).
4. Idan ya bukaci ruwan sha ko waninsa, kuma yana tsoron kishi zai iya yi masa illa ga kuma ruwan kadan ne, to sai ya yi taimama.
3. Sharuddan wajabcin taimama.
a. Balaga.
b. Ikon samun amfani da turbaya.
c. Samuwar hadasi wanda ya warwara alwalar.
4. Sharuddan ingancin taimama.
1. Musulunci
2. Yankewar jinin al'ada ko biki.
3. Hankali.
4. Samun wuri mai tsarki.
5. Farillan taimama.
1. Niyya.
2. Wuri mai tsalki.
3. Bugu na farko.
4. Shafar fuska da tafikann ha nnuwa.
6. Sunnonin taimama.
1. Bismillah. بسم الله
2. Fuskantar alkibila.
3. Ta kasance ayi ta a lokacinda za'ayi sallah.
4. Bugun kasa na biyu.
5. Jerantawa.
6. Tsattsefe yatsun hannu.
7. Abubuwan dake warware taimama.
1. Samun ruwa.
2. Abubuwan dake warware alwala da wanka to suna warware taimama, domin ita taimama abar musanyawarsu ce, kuma abunda ya warware na asali (wato alwala da wanka) to yana warware na biye da shi.
8. Yadda ake taimama.
Sai mutum ya yi niyya, ya ambaci sunan Allah (ya ce: بسم الله), sai ya bugi kasa da hannuwansa, sa'annan fuskar shi da tafikan hannuwansa da turbayan a jere.
9. Taimama ga mai dauri ko ciwo.
Duk wanda akwai karaya ko ciwo ko kurji a jikinsa, kuma yana tsoron cutuwa idan ya wanke wajan da ruwa, ko kuma zai sa shi damuwa idan ya shafa, to sai ya yi taimama bayan haka sai ya wanke sauran.
Duk wanda ya rasa ruwa ko turbaya a kowanni hali to sai ya yi sallah gwargwadon halin kuma ba zai sake ta ba.
1. Dan Mubarak ya ce: Babu sabani akan shafar huffi. Imamu Ahmad ya ce, babu wani abu a zuciya ta wacce na hardace fiye da hadisai arba'in sai akan shafar huffi wanda yake daga manzon Allah (ﷺ) shi Imam Ahmad ya ce, shi shi shafa akan huffu shi ne abinda ya fi wankewa, domin Manzon Allah (ﷺ) da sahabbansa suna neman abunda yake mafifi ci ne.
2. Iyakar lokutan sa: Ya halasta rana guda ga mutumin da ke zaune ba tafiya yake ba, shi kuma matafiyi kwana uku, kuma zai fara ne daga lokacin da ya yi tsarkin hadasi (wato alwala) bayan ya yi shafa.
3. Sharuddansa:- Ya kasance abun da za'a shafa halas ne, mai tsarki ne wajan amfani da shi, mai rufe abunda aka iyakance, tabbatacce ne a karan kansa, kuma an sanya shi a lokacin da ake da tsarki (wato alwala).
4. Siffan yadda ake shafa a kan huffi:- Mutum zai sanya hannun shi a cikin ruwa, sai ya shafi saman kafar, zai fara ne daga yatsu zuwa kwaurin sa, sau daya, banda kasan huffin kuma diddigen.
5. Abubuwan dake bata shafa akan huffi: shafa akan huffi yana baci ne da daya daga cikin abubuwa hudu:
(1) Idan ya cire huffinsa daga kafansa.
(2) Idan wankan janaba ya zama wajibi akan sa.
(3) Idan huffin ya yage, yagewa mai girma.
(4) Idan lokutan shafa suka cika.
kuma akan karan dori yana halasta akan duk wani abun da ke da siffar safa ko da lokacin ya yi tsawo ko janaba ta same shi.
-Hukunce-hukunce da suka rataya da sallah.
- Sallar jam'i.
-Sallar Kasru. (Sallar matafiya).
- Hada salloli biyu.
- Sujjadar rafkannuwa (Kabaliyya da Ba'adiyya).
- Sallar nafila.
- Sallar juma'a.
- Sallar Idi biyu.
- Sallar rokan ruwa.
- Sallar kisfewar rana ko wata.
- Jana'iza da hukunce hukuncenta.
(1) Ma'anarta a yararan Larabci da kuma Shari'ah.
Sallah a yare:- ita ce addu'ah, Allah ta'ala ya ce:
﴿ وَصَلِّ عَلَيْهِمْ إِنَّ صَلَاتَكَ سَكَنٌ لَهُمْ ١٠٣﴾
Ma'ana: “Kuma ka yi musu addu'ah, lalle addu'ar ka natsuwa ce a gare su". {Taubah:103}.
Sallah a Shari'ah:- ita ce 'zancene da ayukka kebanttu, wacce ake bude ta da kabbara, kuma a rufeta da sallama tare da sharuddan ta kebabbu.
(2) Tarihin Wajabta sallah.
An farlanta sallah ne a daren Isra'i kafin hijra, kuma da ya ce daga cikin rukunnan addinin musulunci, bayan imani da Allah da manzonsa ita ce farko, domin ta kunshe su, wacce Manzon ﷺ Allah ya shardanta ta bayan Tauhidi, mai tsira da aminci ya ce: “Kan dukkan al'amari shi ne musulunci, gimshikinsa kuma ita ce sallah, kuma kololon gimshi kuma shi ne jihadi domin daga Kalmar Allah". {Tirmizi ya ruwaito}.
(3) Hikimar Shar'anta ta.
Sallah godiya ce ga ni'imomi masu girma, wace Allah ya ni'imata ga bayinsa, kamar yadda take daga cikin ababan dake bayyana kadaituwar Allah, ta yadda take bayyanar da fuskanta ga Allah madaukakin sarki da kusanci, kankanta da kai a gaban shi, da kuma ganawa da shi madaukakin sarki, ta hanyar karatu, da zikiri, da addu'ah. Kamar yadda ta kasance hanyar da take hada bawa da Ubangijinsa, kamar yadda take daukaka shi akan wasu abubuwa na kyalekyali zuwa inda zai samu natsuwa a ransa da kwanciyar hankali, saboa haka duk wanda ya nitse wajen tunanin rayuwa mai daurewa to sallarsa ta kasance tabbatacciya ta hakika daga barin gafala daga ita. Hakika abin dake nuni da akwai abun dake da girma fiye da wannan, ita rayuwa kuma bai kamata a tafiyar da ita akan wannan tsari ba, kuma tana juya mutum don yayi ruyuwa akan ta, amma yana shiga cikin wata rayuwa zuwa wata rayuwar.
(4) Hukuncin sallah da adadinta.
Sallah nau'i biyu ce; ta farilla da ta nafila. Amma farilla ta rabu kashi biyu: farali wanda ke kan kowa da farali wanda wasu na dauke wa wasu. Farali wanda ke kan kowa; shi ne wajibi akan kowanne musulmi mukallafi na miji ko mace. Sune kuma salloli biyar, Allah ta'ala ya ce:
﴿ إِنَّ الصَّلَاةَ كَانَتْ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ كِتَابًا مَوْقُوتًا١٠٣﴾
Ma'ana: “Lalle sallah ta kasance wajibi abun yi wa lokaci ga muminnai". (Nisa'i: 103). Kuma ya kara cewa;
﴿وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ٥﴾
Ma'ana: “Kuma ba a numurce su da komai sai don su bauta wa Allah, suna masu tsarkake addini gareshi, kuma suna masu karkata zuwa ga addinin gaskiya su tsaida sallah kuma su bada zakkah, wannan shi ne addini tsayayye". {Bayyana:5 }.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “An gina musulunci akan abubuwa biyar ne: Shaidawa babu abin bauta wa da cancanta sai Allah, kuma Annabi muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne, da tsaida sallah da bada zakka". {Bukhari da Muslim, suka ruwaito}.
Nafi'u dan Azrak ya ce Dan Abbas t shin ana samu sallah biyar a Akur'ani kuwa sai ya ce: “Eh", sa'annan sai ya karanta fadin Allah madaukakin sarki:
﴿فَسُبْحَانَ اللَّهِ حِينَ تُمْسُونَ وَحِينَ تُصْبِحُونَ١٧ وَلَهُ الْحَمْدُ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَعَشِيًّا وَحِينَ تُظْهِرُونَ١٨﴾
Ma'ana: “Tsarki ya tabbata ga Allah da maraice da kuma safiya, goiya ta tabbata a gareshi a cikin sammai da kassai lokacin dare da rana". {Rum:15-16}.
Haka hadisin wani balaraben kauye, wanda ya zo wurin Manzon Allah ﷺ ya ce masa: Menene Allah ya wajabta mini na sallah?. Sai ya ce: Salloli biyar". Sai ya ce; Ko akai wasu a kaina bayansu?, sai Ma'aikin Allah ﷺ ya ce: A'a, saidai idan nafila ka yi". {Bukhari da Muslim}.
(5)Yaushe ake umurtar yara da sallah?.
Ana umurtasu da sallah idan suka kai shekara bakwai, ana kuma bugun su game da kin yin sallah idan sun kai shekara goma, amma duka mara mara karfi, saboda Hadisi mai cewa:
“Ku umurci yaran ku da yin sallah idan sun kai shekara bakwai, kuma ku buge su akanta idan sun kai shekara goma, ku raba musu wurin kwanciya". [Abu Dauwd da Tirmizi suka ruwaito}.
(6) Hukuncin wanda ya musunta wajabcin sallah:-
Duk wanda ya musunta wajibcin sallah to kafiri ne, idan ya kasance cikin wadanda ba sa jahiltar sallar kuma kuma ko da ya yi sallar, domin ya zama wanda ya karyata Allah da Manzonsa da kuma ijma'in al'umma. Haka kuma wanda ya barta kawaida don wulakantar da ita ko kawai saboda kasala, ko da ya tabbatar da wajibcin ta, domin fadin Allah ta'ala:
﴿فَإِذَا انْسَلَخَ الْأَشْهُرُ الْحُرُمُ فَاقْتُلُوا الْمُشْرِكِينَ حَيْثُ وَجَدْتُمُوهُمْ وَخُذُوهُمْ وَاحْصُرُوهُمْ وَاقْعُدُوا لَهُمْ كُلَّ مَرْصَدٍ فَإِنْ تَابُوا وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَآتَوُا الزَّكَاةَ فَخَلُّوا سَبِيلَهُمْ إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَحِيمٌ٥﴾
Ma'ana: “To ku yaki mushirikai a duk inda kuka samesu". Har zuwa inda Allah ya ce: “To idan suka tuba, kuma suka tsaida sallah suka bada zakka to ku sakar musu hanya". {Tauba:5}.
Kuma an ruwaito daga Jabir t ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
“(Abinda ke) Tsakanin mutam da shirka da kuma kafirci (to shi ne) barin sallah". {Muslim ne ya ruwaito shi}.
(7) Rukunan sallah:-
Rukunan sallah goma sha biyar ne, ba'a barin su dagangan ko da mantuwa ko da jahilci.
1. Tsayuwa cur a sallar farilla ga mai iko.
2. Kabbarar harama, ita ce kuma: “Allahu Akbar". babu wani lafazin sai wannan.
3. Karatun fatiha.
4. Ruku'u.
5. Dagowa daga ruku'u da daidaituwa a tsaye.
6. Sujjada.
7. Dagowa daga sujjada.
8. Zama tsakanin sujjada biyu.
9. Natsuwa, ita ce kuma kamewa.
10. Tahiyar karshe.
11. Zama domin tahiyar karshe.
12. Salati ga Annabi ﷺ.
13. Sallama.
Ita ce kuma mutum ya fada sau biyu, “Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah". Ta farko kar ya kara da “Wabarakatuhu". Domin hadisin Abdullahi dan Mas'ud, lalle Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance yana sallama daga damansa: “Asalamu alaikum Wa Ramatullah". Daga hagu kuma: Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah". {Muslim ne ya ruwaito shi}.
14. Jerantawa tsakanin rukunnai.
(8) Wajiban sallah.
Wajibanta takwas ne, sallah na baci da barisu dagangan amma ba ta baci da mantuwa ko kuma da rashin sani.
1. Kabbara, banda ta harama.
2. Fadin “Sami Allahu Liman hamidahu", ga liman da mai sallah shi kadai.
3. Fadin “Rabbana Wa Lakal Hamdu".
4. Fadin “Subhana Rabbiyal Azim". Sau daya a ruku'u.
5. Fain “Subhana Rabbiyar A'ala Wabi Hamdihi". Sau daya a sujudah.
6. Fadin “Rabbigh Firli". Tsakanin sujjada da sujjada.
7. Tahiyyar farko.
8. Zama domin tahiyar.
(9) Sharuddan sallah.
Sharadi a yaran Larabci shi ne: Alama. A Shari'ance shi ne; Abunda ba'a samin abun da aka shardanta idan aka rasashi, kuma ba ya lizimtar samunsa idan aka same shi.
Sharuddan sallah su ne; niyya, musulunci, hankali, wayo, shigar lokacin sallah, tsarki, fuskantar alkibla, suturta al'aura, da kawar a najasa.
(10) Lokuttan sallaloli biyar:-
Sune abun da aka cirato daga taukit, kuma shi ne iyakancewa, lokacin sallah sababine game da wajibcin ta, kuma sharadi daga cikin sharuddanta.
Hakika Annabi ﷺ ya iyakance lokutan sallaloli biyar a hadisai masu tarin yawa. An karbo daga Dan Abbas Allah t, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: “Jibril ya limanceni a daidai Ka'abah sau biyu". Sai ya ambaci lokutan salloli biyar, sa'annan ya Manzon ﷺ Allah ya ce; “Sai Jibril ya juya sai ya ce dani; Ya Muhammad wannan shi ne lokucin Annabawa kafin kai, kuma lokuci shi ne abinda ke tsakanin wadannan lokutan biyu". {Abu Dawud}.
Hakika lokutan salloli biyar sun zo ne a yadda suka raba yini da dare. Idan mutgum ya yi barci gwargwadon iko to hakika zai say a sami hutu, dab da asubahi kum lokacin kokari da kuma aiki, lokacin sallar asubahi kuma ya yi, domin mutum ya ji ya iya banbace shi da sauran hlittu, ka ga sai ya fuskanci yininin nasa da guzurin imani.
Kuma lokacinin da ya fuskanci yini sai ya sake tsayawa domin ya yi lura da sha'anin Ubangijinsa a sallar azahar, tare da inganta aikin sa a farkom yinin sa, sa'annan idan la'asar ta zo sai ya sallace ta, yana mai fuskantar sauran yinin sa, sa'annan magaribi domin fuskantar dare da kuma isha'i a tsakiyar daran yana dauke da su a cikin darensa, wanda yake wurine na boye haske da shiryawa ga hanya madaidaciya. Kamar yadda sallah ta kasance tana da lokuta mabanbanta, wannan zai taimaka wa mutum domin yin tunani a cikin mulkin Allah madaukakin sarki da kum kyauta ta ga duk abunda yake kiyaye shi mutum na dare da yini.
Lokacin Sallar Azahar.
Farkon lokacin zuhur yana farawa ne daga zawali ne, shi ne kuma gushewar rana daga tsakiyar sama. Karshen lokacinta, idan inuwa ta yi daidai da tsawon kowannne abu bayan inuwar da ta karu ta gushewar rana (alokacin azahar).
Lokacin sallar Lasar.
Farkon lokacin sallar lasar, daga kaiwa karshen lokacin azahar ne. lokacin da inuwa ta yi daidai da tsawon kowanne abu bayan inuwar da ta karu alokacin azahar wato inuwar gushewa. Karshen zabbaben lokacita kuwa shi ne lokacin da inuwa ta ninka kowanne abu sau biyu. Lalurin su shi ne faduwan rana.
Lokacin sallar magariba.
Farkon lokacin sallar magariba shi ne faduwau rana. Karshen lokacin magariba kuwa shi ne bayyanar taurari, karshen lokacin halascin sallatar magariba kuwa tare da karhanci shi ne boyewar jan shafaki.
Lokacin sallar isha'i.
Farkon lokacin sallar isha'i shi ne boyewar jan shafaki. Amma karshen lokacin shi ne tsakiyar dare.
Lokacin sallar asubahi.
Farkon lokacin sallar asubahi shi ne lokacin fitowar alfijir. Karshen kuwa shi ne fitowar rana.
(11) Tsarin lokutan sallah ga birane masu tsawon ginegine.
Birane masu tsawon, sun kasu kashi uku;
1. Birane wadanda aka yi akan lambar 45 da 48 arewa da kudu, alamar lokutan sallah tana bayyana dare da rana, koda lokuta sun tsawaita ko akasin haka.
2. Birane wadanda suka kasance akan lambar 48 da 66 arewa da kudu wasu alamomi na lokuta ba sa bayyana a cikin gidayayyun kwanaki a shekara, kamar shafaki ya ki bacewa har ya yi kusan shiga juna shi futowar alfijir.
3. Birane wadanda suke saman lambar 66 arewa da kudu zuwa “Katbin", suna rasa wasu alamomi na lokutan sallah a lokaci mai alamomi na lokutan shekara a dare ko rana.
Dangane da kashi na daya yana wajaba akan mazaunin wurin ya kasance ya sallaci sallah a lokutan ta da aka ambata a bayanin da ya gabata, amma kashi na uku babu shakku akan lokutan sallah na wadannan biranen ana kaddarawa ne hakikanin kaddarawa, wannan ko kiyasi ne akan kaddarawar da ta zo wacce aka ruwaito a cikin hadisin Jujal: “Muka ce; Ya Mazon Allah (ﷺ) ya zamansa zai kasance a kasa?. (watan shi Dujjal din kenan idan ya bayyana) sai Ma'aikin Allah ﷺ ya ce: “Wata ranar kamar shekara take". sai muka ce; Ya Ma'aikin Allah wannan yinin kamar shekara, zai iya wadatar da mu sallar yini da dare?. Sai ya ce; “A'a, sai dai ku kaddara mi shi gwargwadonsa". (Muslim).
Hakika anyi sabani akan yadda za'a kaddara, wasu suka ce lalle za'a kaddara shi da lokuta masu daidai, sai a kaddara yini akan awa koma sha biyu haka ma dare, wasu suka ce: za'a kaddara ne da lokutan Makkah ko Madinah. Amma dangane da kashi na biyu to lalle shi in banda lokcikin isha'i da alfijir to yana nan kamar yadda kashi na daya yake, saidai alfijiri da ishai lokutan na daya zai zama kamar kashi na uku ne.
a. Hikimar Shar'anta sallar jam'i tana daga cikin manyan ibada da biyyana ga Allah na daga cikin abun da ya bayyana na sauki, jin kai, da kuma daidaitawa tsakanin muslmi, ta yadda suke haduwa a wuri karami domin sallatar salloli biyar a yini da dare, akan abin yabo tare da jagoranci guda daga cikin su, kuma a fuskanci wuri guda, sai zukata su hadu su kara haske suna masu jinka juna da saduduwa da juna kuma abin dake raba kai ya kau.
b. Hukuncin sallar jam'i.
Sallar jam'i: Wajibi ce akan maza da suke 'ya'ya (ba bayi ba), masu iko, mazauna a gida da kuma matafiya, domin fadin sa Allah madauka kin sarki;
﴿وَإِذَا كُنتَ فِيهِم فَأَقَمتَ لَهُمُ ٱلصَّلَوةَ ١٠٢﴾
“Kuma idan ka kasance a cikin su sai ka tsayar musu da sallah, a samu wasu bangare su tsaya tare da kai, (a wajan yaki). (Nisa'i:102).
Shi umarni yana da'idar da wajibci ne, to idan ya kasance haka za'a yi alokacin yaki to ai alokacin aminci ya fi cancanta.
c. Abunda yake da shi ake samun a sallar jam'i.
Ana la'akari da liman da kuma mamu, koda kuwa mutane biyu, ko da ko mamun macece saboda hadisin Abu Musa wanda ya kai ga Manzon Allah ﷺ: “Mutane biyu zuwa sama to su jama'ah ne". (Ibnu Majah).
d. Wurin da ake sallar jam'i.
An sunnata ta a masalaci tare da jama'ah, kuma tana halasta a yi ta a wani wurin da ba masallaci ba idan akwai bukatar yin hakan.
Su kuma mata sun sami damar hakan idan sun kebanta ga maza, domin aikin Nana Aisha da Ummu Salama, wanda Darul-kutuni ya ambata: Kuma Manzon Allah ﷺ ya umarce Ummu Waraka da ta jagoranci mutanan gidanta. (Abu-Dawud).
(SALLAR MATAFIYA).
a. Ma'anan sallar Kasru.
Sallar kasru a halin tafiya: Ita ce rage sallah mai raka'a hudu zuwa biyu. Kuma wannan akwai ma'ana mai girma wacce Shari'ar Musulunci ta kunsa na daga abin da zai kiyaye rayuwar musulmi, da kuma tabbatar da sauki a gareshi. Kasru ya tabbata ne ta Akur'ani da Hadisi, kuma ya halasta akan ittifaki na malamai.
b. Kasaru ana yin shi ga duk tafiya ta aminci ko wani ta.
Ana kasaru ne a halin tafiya cikin aminci ko tsoro, tsoro wanda ya tabbata a ayar da ta gabata, ya zo ne a galibin lokaci, domin hakika abin da yake shi ne mafi rinjaye a tafiyetafiyan Annabi ﷺ ba'a rasa tsoro a ciki, domin ganin sallar bata kubucewa akan tsoro Sayyidina Aliyu ya ce wa Sayyidina Umar (Allah ya kara musu yarda) : za mu yi kasaru alhali mun aminta, sai Sayyidina Umar ya ce masa: “Na yi mamakin abin ka yi mamakin sa, sai na tambayi Manzon Allah tsira da aminci Allah su tabbata a gareshi ya ce: “Sadaka ce da Allah ya yi muku ita, saboda haka ku karbi sadakarsa". (Muslim ya ruwaito shi).
c. Nisan dake sawa a yi sallar kasaru.
Amma nisan dake sa wa a yi sallar kasaru to shi ne duk abunda aka ambace shi a matsayin tafiya wacce aka sani, kuma ana daukar masa guzuri da abin gusuri.
d. Inda ake fara sallar kasaru.
Matafiyi yana fara yin kasru ne idan ya bar gidajan garin sa, na abunda za'a kira shi da sunan mararraba a al'adance, domin Allah madaukakin sarki ya sanya sallar kasaru idan ana tafiya a bayan kasa, tafiya kuma bata kasancewa har sai matafiyi ya rabu da gidajan garinsa.
Hada sallaoli biyu sauki ne da yake bijirowa a lokacin bukata shi, hakika mafi yawan malamai sun so barin hada salloli biyu sai dai a lokacin bukatawa wacce take bayyananna, domin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai hada tsakanin sallah da sallah ba sai lokuta kadan. Kuma duk wanda ya halasta ya yi kasaru to ya halasta a gareshi ya hada salloli biyu, amma kuma ba duk wanda ya halasta ya hada salloli ba yake halasta a gareshi ya yi kasaruba.
Hada a farkon lokaci da kuma karshen lokaci.
Abin da yafi falala shi ne mutum ya aikata abin da ya fi sauki a gareshi na hada sallolin kodai a farkon lokaci (Jam'u Taqdee) ko kuma a karshen lokaci (Jam'u Ta'akheer), domin abun nufi anan shi ne sauki da saukakawa. Amma idan jam'in suka yi daidai (wato kowanne aka yi babu takura) to abunda ya fi shi ne a jinkirta zuwa lokacin sallah ta biyu(wato: Jam'u Ta'akheer), idan kuwa ya kasance ya isa to abunda ya ke shi ne Sunnah ya yi kowacce sallah a lokacinta.
***** ****** ******
(Kabaliyyah da Ba'adiyyah).
Rafkannuwa a sallah ita ce mantuwa a cikin ta, ta tabbata a Shari'ance da ittifakin malamai, domin aikin Annabi ﷺ da kuma umurni da ya yi da ita. Ana sujjadar rafkannuwa domin kari (sai ayi ba'adiyya), ko domin ragi (sai a yi kabaliyyah), ko kokwanto, kuma wurin da ake yin ta kafin sallamewa ko bayan sallamewa, sujjuda biyu ba tare da tahiya bam za'a yi kabbara a kocce sujjuda kuma ayi salama bayan ta.
***** ****** ******
a. Hikimar shar'anta ta.
Daga cikin ni'mar Allah da ya yi akan bayin sa shi ne ya sanya musu ibada wace za ta kewaye dukan jikin su, kuma ta tabbatar musu da abun da suke nufi wajan ba da ayyuka ta fuskoki ingantattu, kuma har mutum kuskure ko kazawa za ta gitta masa to sai Allah maigirma da daukaka ya Shar'anta wani abu zai cika hakan ya zama makwafinsa, sallar nafila kuwa tana daga cikin haka, domin hakika ya tabbata daga Ma'aikin Allah ﷺ cewa lalle sallar nafila nata cika sallar farillla, idan mai sallar bai kasance cika ta ba.
b. Abinda ya fi da za'a yi nafila da shi.
Shi ne kokarin daukaka Kalmar Allah, sa'annan ilimi da ilmantarwa na shari'ah, Allah ta'ala ya ce;
﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ إِذَا قِيلَ لَكُم تَفَسَّحُواْ فِي ٱلمَجَلِسِ فَٱفسَحُواْ يَفسَحِ ٱللَّهُ لَكُم وَإِذَا قِيلَ ٱنشُزُواْ فَٱنشُزُواْ يَرفَعِ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنكُم وَٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلعِلمَ دَرَجَت وَٱللَّهُ بِمَا تَعمَلُونَ خَبِير١١﴾
Ma'ana: “Allah na daukaka wadanda suka yi imani daga cikinku da kuma wadanada aka bai wa ilimi da darajoji". (Mujadalah: 11).
Sa'annan sai sallah ita ce mafificiyar ibadar jiki, domin fadin Manzon Allah ﷺ: “Ku tsayu kuma kada ku gaji, ku sani da cewa mafi alherin ayyukan ku ita ce sallah". (Ibnu-Majah).
Daga cikin salloli na nafilfili akwai: -
a. Sallar dare:
Sallar dare ita ce mafi girman lada akan sallar yini (sallar rana), kuma sallah a rabin dare na karshe ya fi (a rabin dare na farko) domin fadin Manzon Allah ﷺ: “Ubangijin mu wanda albarkarsa ta daukaka, yana sauka zuwa saman duniya a kowanne karshen rabin dare da ya wuce". (Muslim ne ya ruwaito).
Ita kuma sallar tahajjud wacce ake yin ta bayan an yi bacci an tashi, Sayyida Aisha Allah ya kara mata yarda ta ce “Abunda ake nufi da: “Annashi'a". ita ce tsayuwa bayan bacci".
b. Sallar duha (Walaha).
An sunnata yin sallar duha a wasu kwanaki banda wasu kwanakin, domin hadisin Abi said; “Manzon Allah ﷺ ya kasance yana sallar duha har sai mun ce; baya barinta. Kuma wata rana zai barta har sai mun ce; baya sallah tar ta". (Ahmad da Tirmizi suka ruwaito.) Kuma (Tirmizi) ya ce hadisin Gharibi ne.
Karancin ta (ita sallar walaha) shi ne raka'a biyu, kuma Manzon Allah ﷺ ya sallaceta raka'a hudu kuma ya sallaceta raka'a shida, mafi yawan ta shi ne raka'o'i takwas, ba'a sharadanta yin ta kulum ba.
c. Sallar gaisuwan masallaci. (Idan an shiga masallaci).
An sunnan ta sallar gaisuwar masallaci, domin hadisin Abi Mikdad lalle Annabi ﷺ ya ce: “Idan dayan ku ya shiga masallaci to kar ya zauna har sai ya yi sallah raka'a biyu". (Malaman Hadisi suka ruwaito).
d. Sujudar Tilawa.
An sunnan ta yin sujjudar tilawa ga mai karanta Alkur'ani da kuma mai sauraro, zai yi kabbara lokacin yin sujjudar, kuma ya yi sallama idan ya dago, kuma zai fada ne a cikin sujjudar ta shi:
سبحان ربي الأعلى.
Ma'ana: “Tsarki ya tabbata ga Ubangiji na madaukaki." Ko kuma duk abinda ruwaito.
e. Sujudus – Shukur. (Sujjadar godiya).
An sunnanta sujudus-shukur lokacin da mutum ya samu wata sabuwar ni'ma ko kaucewa wani bala'i, saboda hadisin Abibakata t ''Lalle Annabi ﷺ ya kasance idan wani lamari mai farhanta masa rai ya zo sai ya fadi yana mai sujjada". (Abu dawud, Tirmiz, Ibn majah suka ruwaito).
“Kuma Sayyidina Aliyu t ya yi sujjadar a lokacin da ya samu Zul Sudayya wanda ke cikin Kawarijawa". (Ahmad ne ya ruwaito). Kuma “Ka'ab bin Malik ya yi sujjadar lokacin da aka yi mishi bushara ta karbar tubansa ga Allah". Kuma kissarsa tabbatacciyace. Siffar sujjadar godiya ga Allah da hukunce-hukuncenta kamar na sujjudar tilawa ne.
f. Sallar Tarawih. (Asham).
Tarawihi Sunnah ce mai karfi, wace Annabi ﷺ ya sunnan ta, ana yin ta a jam'i a cikin massalaci bayan sallar isha'i a watan Ramadan. Hakika Manzon ﷺ ya sunnan ta ta, kuma Umar dan Khatah t ya rayar da ita a zamanin halifancin sa. Abunda ya fi mutum ya yi ta raka'a goma sha daya (11), amma ba laifi in ya kara akan haka, duk abunda ya kara ya zama kokarinn sa ne, kuma ya kara a goman karshe na Ramadan ya kara abubuwa kamar kara salloli da zikiri da addu'o'i.
g. Sallar Wutiri.
Wutiri Sunnna ne mai karfi manzon Allah ﷺ, ya aikata shi kuma ya yi umurni da yin shi, mafi karancinsa raka'a ta uku ne, kuma ma fi yawansa raka'a goma sha daya (11).
Lokacinsa: Tsakanin sallar isha'i da fitowar alfijir, ana kunutu a cikin sa bayan an dago daga ruku'I amma mustahabi ne.
Siffofin sa.
1. Mutum ya sallace shi (shi wuturin) gaba-daya ba tare da ya zauna yin tahiya ba har sai ya kawo raka'ar karshe.
2. Ya zauna a raka'ar kusa da karshe ya yi tahiya ba tare da sallama ba, sai ya mike ya kawo raka'a daya ya yi tahiya sai ya sallame.
3. Ya sallame bayan ya kawo raka'a biyu, sa'annan ya cika da karo raka'a daya, ya yi tahiya ya salllame. Wannan siffar ita ce mafificiya daga sauran siffofin, domin ita ce Manzon Allah ﷺ ya aikata kuma yafi yawan aikata ta.
h. Sunanu Rawatib.
Mafifici a cikin sui ta ce ta alfijiri (wato raka'o'i biyu kafin sallah asuba), domin hadisin Sayyidah Aisha Allah ya kara mata yarda, wanda ya kai ga manzon Allah: “Ya ce: Raka'o'i biyu na alfijir sun fi duniya da abin da ke cikin ta".(Muslim, tirmizi kuma ya ingantashi).
Kuma Rawatib masu karfi raka'o'i goma sha biyu ne: Hudu kafin azahar biyu bayanta, da biyu bayan magariba, da kuma biyu bayan isha'i sai kuma raka'atal fijir (wato biyu kafin asuba).
Kuma an sunnanta rama wadannan nafilfilin (wato sunanu rawatib) idan suka kubucewa mutum, haka kuma rankon wutiri tare da sha'i, saidai idan ya kubuce tare da faralinsa kuma ya yi yawa, to abinda ya fi sai a barshi saboda samuwar kuntata idan akce za a yi shi, saboda haka sai ayi raka'oi biyu na nafilar alfijir ita zai biya bashin ta kai tsaiye, domin karfatata. Kuma yin wadanan a gida yafi falala ba kamar sallar farilla ba, da kuma duk sallar da aka shar'anta yenta cikin jam'i.
a. Falalar ranar juma'a.
Ranar jumuah na daga cikin ranaku masu falala matuka, Allah madaukakin sarki ya kebance wannan alumma da wannan rana, kuma ya shari'anta musu haduwa a cikin wannan rana, daga cikin hikimar haka shi ne samar da fahimtar juna a tskanin al'ummar musulmai da tausayawa, jinkai da taimakon juna. Ranar juma'ah idi ce na mako, kuma shi ne mafi alherin yini da rana zata bullo a cikin sa.
b. Hukuncin Sallar Juma'ah.
Sallar juma'ah wajibi ce, domin fadin Allah Ta'ala;
﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَوةِ مِن يَومِ ٱلجُمُعَةِ فَٱسعَواْ إِلَى ذِكرِ ٱللَّهِ وَذَرُواْ ٱلبَيعَ ذَلِكُم خَير لَّكُم إِن كُنتُم تَعلَمُونَ٩﴾
Ma'ana: “Ya ku wadanda suka yi Imani, idan akayi kiran sallah na ranar juma'ah, to ku yi gaggawa zuma ga ambaton Allah kuma ku bar ciniki……". (Jumuah:9). kuma raka'a biyu ce.
An sunnanta wanka domin ita, da kuma zuwa akan lokaci.
c. Wanda juma'a ta wajaba akansa?.
Ta wajaba ne akan dukkan Musulmi na miji mukallafi (wanda hukunce-hukunce shari'a suka hau kansa, wanda bai da uzuri.
d. Lokacin ta.
Tana inganta kafin gushewar rana, da bayan gushewar ta kuma shi ya fi falala, domin shi ne lokacin da Manzon Allah ﷺ ya fi sallatar ta kenan.
e. Dame ake kullla sallar jumuah.
Tana kulluwa ne da abinda mutane suka sani su ne jama'ah a al'adance.
f. Sharuddan ingancinta. Abubuwa ne biyar.
1. Lokaci.
2. Niyya.
3. Yinta a halin zaman gida.
4. Halartar mutane wadanda ake la'akari da yawansu.
5. Hudubobi biyu su gabaceta, wadanda suka shafi: godiya ga Allah madaukakin sarki, da salati ga Annabi ﷺ, da kuma karanta ayoyi daga littafin Allah madaukakin sarki, da yin wasiya da tsoron Allah, da kuma bayyanawa ta yadda mafi yawan mutane za su ji. An haramta magana a lokacin da limami yake huduba, da kuma tsattsalaka mutane, yin sallar juma'a yana wadatarwa da ba sai an yi sallar azaharba, duk wanda ya riski raka'a guda to hakika ya samu jumu'ah. Idan kuma ya sami abinda baikai azahar ba sai ya yi niyyar azahar sai kuma ya sallace azahar raka'o'i hudu.
***** ****** ******
HIKIMAR SHAR'ANTA TA.
Sallar idi na daga cikin alamomin addinin musulunci bayyanannu wadda Allah ya kebance alummar Annabi Muhammad ﷺ da su, wajan tabbatar da godiya ga Allah majibanci akan kammala azumi watan Ramadan (A karamar sallah kenan), da kuma ziyartar dakin Allah mai alfarma (A babbar sallah kenan), kamar yadda ya kasance a idi, akwai kira zuwa ga tausayi da jinkai tsakanin al'ummar musulmi da haduwarsu a wuri daya, da kuma daidaita zukata.
HUKUNCINTA.
Sallar idi farilla ce ta kifaya, Manzon Allah ﷺ da Halifofi na bayan sa sun kasance suna aikata ta, kuma sunnah ce mai karfi akan kowanne musulmi na miji ko mace, kuma an shar'anta ta ga mazauna banda matafiya.
SHARUDDAN TA.
Shurudanta kamar juma'ah ce, saidai banda kutuba hudubobi biyu, domin su sunna ne a sallar idi, kuma ana yin su ne bayan sallah, (ita kuma juma'a kafin sallah).
LOKACINTA.
Daga dagowar rana da safe gwargwadon tsawon mashi, har zuwa zawali (wato gushewar rana daga tsakiya). Idan ba'a san da idi ba har bayan zawali sai a sallace ta gobe a matsayin ranko na lokacin ta.
YADDA AKE SALLAR IDI.
Sallar idi raka'a biyu ce, domin fadin Sayyidina Umar t: “Sallar Fitri (wato karamar sallah) da Adha (babbar sallah) raka'o'i biyu ne cikakku ba tare da ragi ba, a kan harshen Annabin ku ﷺ, duk wanda ya kirkiro to ya tabe". {Ahmad}.
Ana sallar idi ne kafin kutuba, za'a yi kabbara a raka'ar farko bayan kabbarar harama, kuma kafin ta'aewuzi kabba rori shida, a raka'a ta biyu kuma za'a yi kabbara kafin karatu sau biyar.
WURIN DA AKE YIN SALLAR.
Ana sallar idi a fili ne. Kuma ya halasta ayi ta a masllaci idan bukata ta kama.
SUNNONIN SALLAR IDI.
An sunnanta yin kabarbari ba tare da kayyade cewa sai bayan idar da salloliba, da kuma bayyanar da kabarbarin tun a daren sallah din, saboda fadin Allah mai girma da daukaka:
﴿ وَلِتُكمِلُواْ ٱلعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُواْ ٱللَّهَ عَلَى مَا هَدَىكُم وَلَعَلَّكُم تَشكُرُونَ١٨٥﴾
Ma'ana: “Kuma domin ku cika lissafi, kuma ku girmama Allah (wato ku yi mishi kabarbari) akan abinda ya shiryar da ku". (Bakara: 185).
Imamu Ahmada ya ce: Abdullahi Dan Umar –Allah ya kara musu yarda- ya kasance yana kabarbari a duk idunan guda biyu.
A goman Zul Hijja kuma sai Allah madaukakin sarki ya ce:
﴿ وَيَذكُرُواْ ٱسمَ ٱللَّهِ فِي أَيَّام مَّعلُومَتٍَ٢٨﴾
Ma'ana: “Kuma su anbaci Allah a wadansu kwanuka sanannu". (Hajji :28).
Amma kabarbari da aka kayyade sune wadanda suka kebanci bayan salloli, wannan ko ya kebanci babbar sallah ne kadai, sai a fara ga wanda bai aikin hajji daga sallar asuba ta ranar arafa, har zuwa karshen kwanakin babbar sallah.
An so mamu ya isa masallacin idi da wuri, amma shi liman sai ya jinkirta har sai lokacin sallah ya yi, kuma an so mai tafiya sallar idi ya tsafta domin halartar ta, ya kuma sanya mafiya kyawun tufafinsa, kuma mata kada su bayyanar da adonsu.
SUNNONIN IDI.
An so a gabatar da ita a babbar sallah da wuri, kuma a jinkirta ta a karamar sallah.
An sunnanta cin abinci kafin a fita a karamar sallah, kodai dabino dabino, da kuma kame baki daga barin cin abinci a lokacin babbar sallah, domin a ci daga abin da aka yanka.
a. Hikiomar sharanta ta.
Alllah ya halicci mutum kuma ya kagi halittar sa akan yadda zai maida tamari gareshi da neman mafaka a gareshi a lokacin saukar bukatun sa. Ko lokacin da fituntunu suka kawaye shi, rokon ruwa abune wanda yake bayyane daga cikin abubuwa wadanda suke a bayyane a cikin tunanin mutum wanda Allah yasa musulmi ke maida lamarin sa gareshi don neman ruwan sama.
b. Ma'anar ta.
Shi ne neman shayar wa daga Allah madaukakin sarki ga kasa da bayi, hanayar yin sallah da addu'a da kuma neman gafara.
c. Hukuncinta.
Sallar rokon ruwa sannah ce mai karfi, Manzon Allah ﷺ ya yi, kuma ya shelanta ta a cikin mutane, kuma mutane suka fito domin gabatar da sallar a filin idi sallah.
d. LOKACINTA, DA KUMA SIFFARTA DA HUKUNCE-HUKUNCENTA.
Kamar sallar idi take.
An so limami ya sanar da yin ta kafin lokacin da wasu kwanaki.
Kuma ya jawo hankalin mutane zuwa ga tuba daga laifuffuka da kuma mayar da kayan zalunci, da kuma yin azumi da sadaka da kuma barin jiji-da-kai, domin lalle laifuka su ne sababin kawo kunci (fari), kuma kamar yin biyyaya ne shi ne sababin kawo alheri da albarka.
a. Ma'anar kisfewa, Hikimar shar'anta ta.
Kusufi: shi ne bacewar hasken rana ko wata. Kuma yace daga cikin ayoyin Allah Ta'ala inda ke jan hankalin mutum zuwa ga kimtsawa da kuma lura da cewa lalle Allah Ta'ala yana kallon kowa, da kuma neman mafaka a gare shi a lokacin rikicewar yanayi da kuma yin tunani akan girman hukuncin Allah ta'ala ga wadannan halittu.
Kuma da cewa lalle shi ne kadai wanda ya cancanci a bautawa masa.
Idan rana ta kisfe (wato haskenta ya bace) ko wata ta kisfe (wato haskensa ya tafi), sallar kisfewa ta zama Sunnah ga jama'ah.
﴿وَمِن ءَايَتِهِ ٱلَّيلُ وَٱلنَّهَارُ وَٱلشَّمسُ وَٱلقَمَرُ لَا تَسجُدُواْ لِلشَّمسِ وَلَا لِلقَمَرِ وَٱسجُدُواْ لِلَّهِ ٱلَّذِي خَلَقَهُنَّ إِن كُنتُم إِيَّاهُ تَعبُدُونَ٣٧﴾
Ma'ana:“Daga cikin ayoyin Allah akwa dare da yini, rana da wata, kar ku yi sujjuda ga rana ko ga wata, ku yi sujjuda ga Allah wannna da ya halicesu, in kun kasance shi kuke bautawa". (Fusilat: 37)
b. Lokacinta.
Daga lokacin da aka samu kisfewar rana ko wata zuwa wucewar hakan, kuma ba'a ranka ta in lokacin ta ya wuce, kuma ba a ruwaito yin umarni da yinta ba bayan hasken ya bayya, saboda lokacin ya wuce.
c. Siffarta.
Raka'a biyu ce za'a karanta fatiha a raka'ar farko a bayyane da kuma surah mai tsawo, sai ayi ruku'u mai tsawo, sai kuma a dago daga ruku'in sai ayi tasbihi hadi da gode wa Allah, sa'annan a karanta fatiha da kuma surah mai tsawo, sai a sake yin ruku'i, sa'annan kuma a dago, sai ayi sujjuda biyu masu tsawo, sa'annan kuma sai a sake sallatar raka'a ta biyu kammar yadda aka yi ta farko. Amma mafi kasa da ta farko a dukkanin ayyuka (wato raka'a ta biyu ba zata kai ta farko ba), sallar kisfewar rana tana da wata siffar kuma banda wannan wacce ake yi. Saidai amma wannan ita ce wacce ta tabbata kuma tafi ciki, idan kuma ya yi ruku'u uku ko hudu ko biyar babu laifi idan bukatar hakan ta kama.
a. Mutum babu makawa koda ya yi rayuwa mai tsawo sai ya mutu.
Za'a dauke shi daga gidan aiki (wato nan duniya) zuwa gidan sakamako (wato lahira), yana daga cikin hakkin musulmi da ya gai da shi idan bai da lafiya, kuma ya shaidi janazar sa idan ya mutu.
· An sunnanta gaida mara lafiya da kuma tunatar da shi yin tuba da wasiyyah.
· An sunanta a fuskantar da wanda mutuwa ta halarto mishi da ga alkibla, sai a sanya shi maralafiyan a gefen daman sa da fuskar sa, hakanan idan ba zai cutu ba, in bahaka ba sai juya shi ya dubi sama kafarsa na fuskantar alkibla, sai a daga kansa sama kadan don ya fuuskanci alkiblla, sa'annan a lakana masa “Kalmar shahada", sai a zuba masa ruwa a makogwaronsa ko wani abin sha, kuma a karanta masa Suratul Yasin.
· Idan mutum musulmi ya rasu, an sunnanta rufe masa ido, da hada masa gemunsa da hada masa kafafun sa da hannuwansa, a kuma dauke shi daga kasa, a cire masa tufafin sa a kuma rufe masa al'aurasa, a dora shi akan gadon wanka yana kwance gefen dama, kuma yana mai fuskanta alkibla in hakan ya sawwaka in ba haka ba sai a juya kafarsa suna masu fuskantar alkibla.
b. Wankan mamaci.
Mutanen da ya kamata su wanke mamaci su ne wadanda shi mamacin ya yi wasiyya da su, sa'annan baban sa, sa'annan kakan sa, sa'annan na kusa. Ita kuma mace wacce ta yi wasiyyah, sa'annan mahaifiyarta, sa'annan kakarta, sa'annan na kusa da ita, haka kuma kowanne mauraci (miji) zai wanke matar sa, ita kuma ta wanke shi wadanda suke musulmi.
An yi sharadi mai wanka ya kasance mai hankali, mai wayo masani game da hukunce hukuncen wanka.
* An haramta musulmi ya binne kafiri ko ya wanke shi, saidai yana iya tura masa kasa idan babu wanda zai yi hakan.
c. Siffar wanka na sunnsa ga mamaci.
Idan za'a yi wa mamaci wanka, sai a rufe masa al'aura, sa'annan a daga kansa zuwa kwatankwancin yadda zai zauna. Sai a matsa cikin sa kadan-kadan sai a zuba ruwa mai yawa, sa'annan ya sa wani kyalle a hannunsa sai yayi masa tsarki, sa'annan ya yi masa alwala, sa'annnan ya yi niyyar wanke shi, sai ya wanke shi da ruwa da magarya ko sabulu, zai ya fara daga kansa da gemun sa, sa'annan sa'annan gefansa na dama, sai kuma gefansa na hagu, sa'annan ya wanke shi sau biyu zuwa uku kwatankwacin yadda ya yi na farko, in bai tsarkaka ba sai ya ta wanke wa har sai ya tsarkaka, sai ya sanya wankan karshe ya zama ruwa da kafur ko turare, in kuma ya kasance gashin bakin sa ko kunba sa suna da tsawo sai a debe su, sa'annan a tsane shi da tufafin. Ita kuma mace ana yi mata kamu uku na gashin kanta sai a sake su zuwa baya.
d. Likafani.
An sunnanta ayi wa namiji lifafa (likafani) farare guda uku, sa'annan a shinfida su akan juna a sanya musu turaren hamuta, sai kuma a sanya gaurayayyan turare a tsakanin lifafa, sa'annan a sanya mamaci a cikin su. Sai a sanya auduga a ramukan (kamar dubura) sai a daure masa daga sama wani kyalle kamar gajeran wandao don ya rute masa al'auran sa, sai a sa masa turare a sauran jikinsa. Sa'annan a sakko da gefan likafanin dake sama a daga bangaren hagu a maida gefen dama, sa'annan a sakko da gefan likafanin dama akan hagu, sannan shi ma na biyun haka za'a yi shi, hakanan ma na ukun haka za a yi shi, sai a sanya abun da ya sausa a gefan kan sa, sai a daure a gicciya sai kabari za'a kwance.
Za'a iya yi wa karamin yaro lifafa daya, kuma ya halatta a yi masa ukun.
Ita kuma mace ana daura mata zani sa'annan a sanya mata riga, sai kuma a daura mata kallabi (dankwali) da kuma riga, bayan an nade ta a lifafa biyu sai a sanya mata riga a yi mata kallabi kuma da dankwali, sa'annan kuma a nadeta da lifafa biyu. Amma yarinya karama a sa mata riga da lifafa biyu.
- Ya halata a wanke mamci mace ko na miji sau daya, wanda zai game jikin shi gaba daya, haka lifafa daya wacce za ta rufe dukkan jikin shi.
- Bari idan ya cika watanni hudu sannan ya rasu to za ayi masa wanka da sallah, kuma a saya masa suna.
e. Siffar Sallar Jana'iza.
Abin da yake Sunnah shi ne liman ya tsaya a daidai kirjin na miji, ita kuma mace a tsakiyarta, sai ya yi kabba hudu yana mai daga hanun sa a kowacce kabbara.
Kabbara ta farko zai yi Ta'awwuzi, Basmala, sai ya karanta fatiha a sirance, kuma ba zai yi addu'ar bude sallah ba.
Sai ya yi kabbara ta biyu ya karanta Salati ga Anbabi ﷺ (Salatil Ibrahimiyyah), wato ya ce:
اَللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى ءَالِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى ءَالِ إِبْرَاهِيمَ إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ. وَبَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى ءَالِ مُحَمَّدٍ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى ءَالِ إِبْرَاهِيمَ إِنَّك حَمِيدُ مَجِيدٌ.
Ma'ana: Ya Allah Ubangiji! Ka yi dadin tsira ga (Annabi) Muhammad da iyalan (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi dadin tsira ga (Annabi) Ibrahima da kuma iyalan (Annabi) Ibrahima, lalle kai wanda za'a godewa ne kuma mai girma. Kuma ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da kuma iyalan (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi ga (Annabi) Ibrahima da kuma iyalan (Annabi) Ibrhima, lalle kai wanda za'a godewa ne.
Sai ya yi kabbara ta uku, sai kuma ya yi addu'a ga mamaci yana mai cewa:
(( اَللَّهُمَّ اغْفِرْ لِحَيِّنَا وَمَيِّتِنَا، وَشَاهِدِنَا وَغَائِبِنَا، وَصَغِيرِنَا وَكَبِيرِنَا، وَذَكَرِنَا وَأُنْثَانَا، إِنَّكَ تَعْلَمُ مُتَقَلَّبَنَا وَمَثْوَانَا، وَأَنْتَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ. اَللَّهُمَّ مَنْ أَحْيَيْتَهُ مِنَّا فَأَحْيِهِ عَلَى اَلإِسْلاَمِ وَالسُّنَّةِ، وَمَنْ تَوَفَّيْتَهُ مِنَّا فَتَوَفَّهُ عَلَيْهِمَا، اَللَّهُمَّ اَغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ وَعَافِهِ وَاعْفُ عَنْهُ ، وَأَكْرِمْ نُزُلَهُ وَأسِعْ مَدْخَلَهُ، وَاغْسِلْهُ بِمَاءٍ وَثَلْجٍ وَبَرَدٍ، وَنَقِّهِ مِنَ اَلذُّنُوبِ وَالْخَطَايَا كَمَا يُنَقَّى اَلثَّوْبُ اَلأَبْيَضُ مِنَ اَلدَّنَسِ، وَأَبْدِلْهُ دَارًا خَيْرًا مِنْ دَارِهِ وَزَوْجًا خَيْرًا مِنْ زَوْجِهِ وَأَدْخِلْهُ اَلْجَنَّةَ وَأَعِذْهُ مِنْ عَذَابِ اَلْقَبَرِ، وَعَذَابِ اَلنَّارِ، وَافْسَحْ لَهُ فِي قَبْرِهِ وَنَوِّرْ لَهُ فِيهِ.)).
Ma'ana: “Ya Allah ka gafarta wa rayayyun mu, da kuma wadanda suka rasu daga cikin mu, da wadanda suke nan, da wadanda ba sa nan, da manyan mu, mazan mu da matan mu, lalle kai kasan makomar mu da matabbatar mu, kuma kai mai iko ne akan komai.
Ya Allah Ubangiji! Duk wanda ka rayar da shi daga cikin mu to ka rayar da shi akan Musulunci da Sunnah, kuma duk wanda zaka dauki rayuwar shi daga cikin mu to ka dauke ta akan su (wato Musulunci da Sunnah). Ya Allah ka gafarta mishi, ka rahanshe shi, ka yaye masa, ka yafe masa, ka girmama masaukin sa, ka yalwata mishi mashigar sa, ka wanke shi da ruwan kankara da raba, ka tsarkake shi daga zunubai da kurakuran sa kamar yadda ake tsarkake farin tufafi daga dauda, ka canza masa gida wanda ya fi na shi alheri, da mata wacce ta fi matarsa algeri, ya Allah ka ba shi aljanah, kuma ka tsare shi daga azabar kabari da kuma azanbar wuta, ka kyautata mishi a kabarinsa, kuma ka haskaka mishi a cikin kabarin.
- In kuma karamin yaro ne sai ya ce bayan ya fadi: Duk wanda zaka dauki rayuwar sa to ka dauka akan su (Musulunci da Sunnah):
اَللَّهُمَّ اَجْعَلْهُ ذخْرًا لِوَالِدَيْهِ، وَفَرَطًا وَشَفِيعًا ومجابا. اَللَّهُمَّ ثَقِّلْ بِهِ مَوَازِينَهُمَا، وَأَعْظِمْ بِهِ أُجُورَهُمَا وَأَلْحِقْهُ بِصَالِحِ سَلَفِ اَلْمُؤْمِنِينَ، وَاجْعَلْهُ فِي كَفَالَةِ إِبْرَاهِيمَ، وَقِهِ بِرَحْمَتِكَ عَذَابَ اَلْجَحِيمِ.
Ma'ana: Ya Allah ka sayan shi ya zama ajiya da lada da ceto karbabbe ga mahaifansa, ya Allah ka nauyaya mizanin su kuma ka girmama ladan su da shi ka hada su da salihai magabata muminai, kuma ka sanyan shi cikin raino na Annabi Ibrahim, Ya Allah ka tsiratar da shi daga azabar wuta da rahmarka.
- Sa'annan sai ya yi kabbara ta hudu, sai ya yi shiru kadan sannan ya yi sallama daya ta daman sa.
f. FALALAR SALLAR JANAZA.
Duk wanda ya sallaci sallar janaza yana da kwatankwacin lada girman “Kirat" (misalin girman dutsen uhud), in kuma ya bita makabarta har aka binne ta to yana da irin haka biyu.
An sunnata cewa mutane hudu su dauki mamaci, kuma an sunnanta daukar mutum guda a makara ta gefen hannun makarar hudu (wato gaba biyu baya biyu), haka kuma a gaggauta yin janaza, masu rakiya da kafa su shige gaba, masu abin hawa su biyo baya.
g. SIFAR KABARI, BINNEWA DA ABUN DA AKA HANA.
Yana wajaba a zurfafa kabari, idan aka kai kasa sai a fafe inda za'a sa mamaci, ana kiran wannan “Lahad", kuma shi ne mafi falala akan “Shakku" sai mai sa shi a kabarin ya ce: “Bismillahi wa ala millati rasulullahi". (wato: Da sunan Allah, kuma akan addinin Ma'aikin Allah), sai a sanya mamaci a lahad ta gafen daman sa yana fuskantar alkibla, sa'annan a sanya masa hoge (bulo) sosai, sanan a binne shi, akuma tada kasar gwargwadon dani daya, sannan kuma a yayyafa masa ruwa.
- An haramta gini a kabari da kewaye shi da bulo, da yin siminti, da taka shi da yin sallah a inda yake, da maida wurin masallaci, da neman albarka, da shafawa don neman waraka, da sanya fitila, da sanya huranni da kuma yin dawafi.
- An sunnantar da cewa a yi wa wadanda ka yi wa rasuwa abinci a aika musu da shi, an hana su yin girkin domin su rabawa mutane.
- An sunnatar da cewa duk wanda ya ziyarci makabarta ya fadi:
اَلسَّلاَمُ عَلَيْكُمْ دَارَ قَوْمٍ مُؤْمِنِينَ، وَإِنَّا إِنْ شَاءَ اَللهُ بِكُمْ لاَحِقُونَ، يَرْحَمُ اَللهُ اَلْمُسْتَقْدِمِينَ مِنْكُمْ وَالْمُسْتَأْخِرِينَ، نَسْأَلُ اَللهَ لَنَا وَلَكُمُ اَلْعَافِيَةَ، اَللَّهُمَّ لاَ تُحَرِّمْنَا أَجْرَهُمْ، وَلاَ تَفْتِنَّا بَعْدَهُمْ، وَاغْفِرْ لَنَا وَلَهُمْ.
Ma'ana: Amincin Allah ya tabbata a gareku ma'abotan wannan gida wadanda suke muminai, kuma lalle mu in Allah ya so masu riskarku ne, Allah ya jikan wadanda suka gabata daga cikin ku da kuma wadanda suka saura, muna roka mana Allah ya yafe mana mu da ku. Ya Allah Ubangiji! Kada ka haramta mana ladan su, kuma kada ka fitine mu bayansu, kuma ka gafarta mana mu da su.
- An sunnantar da yin ta'aziya ga wanda aka yi wa rasuwa kafin a binne mamaci ko bayan an binnewar, har tsawon kwanaki uku da dareran su, saidai ga wanda ba yanan.
- An sunnanta cewa ga duk wanda jarabta da musiba suka same shi ya ce:
إِنَّا لِلَّهِ وَإِناَّ إِلَيْهِ رَاجِعُونَ، اَللَّهُمَّ أَجِرْنِي فِي مُصِيبَتِي وَأَخْلُفْ لِي خَيْرًا مِنْهَا.
Ma'ana: Lalle mu na Allah ne, kuma lalle mu gareshi za mu koma. Ya Allah Ubangiji! Ka sakanka mini a masifar nan ta wa, ka mayar min da mafi alherinta.
- An halasta yin hawaye ga mamaci, kuma an haramta yaga riga, da bugun kumatu da daga murya don takaici da sauran su.
- Hukunce hukuncen Zakkah.
- Zakkar fiddakai.
Rukuni na uku daga cikin rukunan musulunci.
Zakkah.
a. HIKIMAR SHARANTA TA:
Daga cikin hikimar shar'anta ta ga wasu kamar hak;
1. Tsarkake zukatan mutune daga cutar rowa, da sharrin ta da kuma mako.
2. Yalwatawa ga talakawa, da toshe kofar mabukata da mara shi.
3. Habbaka tsarin lura da bukatun al'ummah wacce rayuwa ta ginu a kanta, da samun rabo mai girma.
Tantance girmana dukiyar da mawadata ke da ita, da wacce take hannun 'yankasuwa da masu hannu-da-shuni, domin kada a kebance dukiyar ta kadaitu a hannun wasu kebantattun mutane, ko ta kasance tana kyakkyawayawane a tsakanin mawa data kadai ne kawai.
b. Ma'anar Zakkah.
Zakkkah ita ce “Wani gwargodo ne da ya zama wajibi a fitar da shi na dukiya a kuma bada shi ga wadanda suka cancanta idan dukiyar ta kai nisabi sananne da sharudda kebantacce".
Zakkah tsarkaka ga dukiya kuma haka kuma ga zukiya, Allah madaukakin sarki ya ce:
﴿خُذ مِن أَموَلِهِم صَدَقَة تُطَهِّرُهُم وَتُزَكِّيهِم بِهَا وَصَلِّ عَلَيهِم إِنَّ صَلَوتَكَ سَكَن لَّهُم وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ١٠٣﴾
Ma'ana: “(Ya Manzon Allah) Ka karbi wani abu daga cikin dukiyar su a matsayin sadaka (zakkah), wacce zata tsarkake su da zukatansu". (Taubah: 103).
d. MATSAYIN ZAKKKAH A MUSULUNCI.
Ita daya ce daga cikin rukunan musulunci biyar, wacce aka gwama ta da sallah a wurare da dama a cikin Littafin Allah mai girma.
e. HUKUNCI ZAKKAH.
Zakkah farillace wace Allah ya wajabta ta akan duk musulmi wanda ya mallaki wani abu daga cikin dukiya tare da cika sharuddan ta “Allah ya wajabta ta a littafin sa, Annanbi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya yi umarni da ayi riko da ita ga duk wanda ta wajaba akan shi, babba ne ko karami, na miji ko mace, mai lafiya ko mara lafiya koda mahaukaci ne, Allah madaukakin sarki ya ce:
﴿خُذ مِن أَموَلِهِم صَدَقَة تُطَهِّرُهُم وَتُزَكِّيهِم بِهَا وَصَلِّ عَلَيهِم إِنَّ صَلَوتَكَ سَكَن لَّهُم وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ١٠٣﴾
Ma'ana: “(Ya Manzon Allah) Ka karbi wani abu daga cikin dukiyar su a matsayin sadaka (zakkah), wacce zata tsarkake su da zukatansu". (Taubah: 103).
Kuma ya ce:
﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ أَنفِقُواْ مِن طَيِّبَتِ مَا كَسَبتُم وَمِمَّا أَخرَجنَا لَكُم مِّنَ ٱلأَرضِ ٢٦٧﴾
Ma'ana: “Ya ku wadanda suka yi imani! ku ciyar daga cikin daddan abu ku ka nema kuma (ku ciyar) daga abinda mu ka fitar muku daga kasa …….". (Bakara: 268).
Kuma Allah mai girma da daukaka ya ce:
﴿ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوةَ ٢٠﴾
Ma'ana:“Kuma ku tsaida sallah ku bada zakkah". (Muzamil: 20).
Manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “An gina musulunci akan abubuwa biyar ne: Shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammad ﷺ Manzon Allah ne, da tsaida sallah, da kuma bada zakkah, da kuma ziyartar daki (wato aikin hajji), da azumin Ramadan". (Bukhari da Muslim).
Dukiya wace ta wajaba a cire mata zakkah nau'uka hudu ne:
1. KUDADE: Sune kuma Zinari, Azurfa da kuma takardun kudade. Zakkah tana wajaba a zinari idan ya kai nauyi mithqali ashirin, to sai a cire daya bisa arbai'n.
- Zakkah tana wajaba ne a azurfa, idan ta kai dirhami dari biyu, to ita ma sai a cire daya bias arba'in, (wato a kasa dukiyar gida arba'in a fitar da daya).
- Ana kimanta takardun kudi da ake da su a yanzu (kamar Naira, Riyal, Dollar …) a na kimanta su da manyan kudi na asali da ake da su (Zinari da Azurfa) idan kudin da ake da shi ya kai nisabin daya daga cikin wadannan kudade biyu (zinari da azurfa) to zakkah ta wajaba, kuma abinda za'a fitar shi ne daya cikin arba'in, idan shekara ta jiyo musu.
2. Zakkar Dabbobi: Zakkah tana wajaba ga rakuma, shanu, da kuma awaki. idan sun ka sance ana kiwon su ko mafi yawansu a sahara ko dazuzzuka halattattu har suka kai shekara. To idan shekara ta zagayo musu kuma suka kai nisabi sai a fitar da zakkarta, saboda hantsa da kuma hayayyafa: dangane da irin dabban kamar haka;
1. Nisabin Awaki/Tumakai: Ana bada akuya daya idan sun kai 40 – 120, Daga, 121 – 200 akuya biyu ake bayarwa, amma daga 201 zuwa sama akuya uku, sa'annan a ko wanne dari akuya ce.
2. Nisabin Shanu: Daga gwargwodon abin da aka kimanta 30 – 39 za'a bada dan maraki ko maraka 'yar shekara daya mace ko namiji. Daga 40 – 59 za'a bada 'yar shekara biyu. Daga 60 kuma 'yar shekara daya guda biyu, haka a kowacce 30 'yar shekara daya a kuma kowacce 40 'yar shekara biyu.
3. Nisabin Rakuma: Daga 5 – 9 za'a bada akuya, daga kuma 10 – 14 akuya biyu, sannan daga 15 – 19 akuya uku, kana kuma daga 20 – 24 akuya hudu. Amma daga 25 – 35 rukuma yar shekara daya, daga 36 – 45 rukuma 'yar shekara biyu. Amma daga 46 -60 rukuma ce mai shekaru uku za'a bayar. Daga 61 – 75 rukuma mai shekaru hudu. Daga 76 – 90 rakuma biyu masu shekaru uku guda uku, sa'annan daga kowacce 40 za'a bada 'yar shekara biyu, haka kuma a kowacce 50 'yar shekaru uku.
- Lalle ne game da dabbobi (Rukuma, shannu, Awaki) wadanda aka rike su domin kasuwanci da habbaka (kamar na gidan gona) to idan shekara ta zagayo kansu za'a kimanta kimar su ne, sai a fitar da zakkar a kimar wato daya cikin arba'in (kamar zakkar kudi kenana), idan kuma ba na kasuwanci ba ne to ba'a bada zakkah akansu.
- Ba'a bada zakkah a kowanne sai macen dabba. Kuma baya halatta a bada namiji sai a zakkar shanu ko ta rakuma a maddadin mace, ko kuma idan nisabin duk maza ne.
4. Zakkar Abunda Ke Fitowa Daga Kasa (Amfanin gona); Yana wajaba a bada zakkar dukkan hatsi da ke fitowa daga kasa, haka kuma dukkanin 'ya'yan itatuwa da ake aunawa ko kae ajiyewa kamar dabino da zabibi. Kuma ana lura da nisabi da kuma gwargodon da aka tsara idan sun kai sa'i 300 watau abin ya kai kimanin kilogram 624.
- Ana hada anfanin gona na shekara guda a hada sashin shi da sashi domin cika nisabi, idan ya kasance jinsi daya guda ne, kamar dabino mai nau'uka daban–daban a msali.
Abun da za'a bada na zakkar 'ya'yan itatuwa:
a. Daya bisa gama; ake cirewa ga abun da aka shayar ba tare da wahala ba kamar ruwan sama ne ya shayar da shi, (wato noman wanda aka yi da damina).
b. Daya bisa ashirin; idan aka shayar da shuka da wahala, kamar wanda aka shayar da ruwan rijiya da sauransu (wato kamar noman rani).
c. Kashi na uku cikin kashi hudun, daya bisa goma za'a cire ga abin da aka shayar a wani lokaci ruwan sama a wani lokacin kuma da ruwan rijiya.
- Zakkah tana wajaba ne idan kayan gona suka nuna sosai, ko ya fara nuna.
- Babu zakka ga abin da bai nuna ba na hatsi da kayan lambu, sai dai idan an tanada ne domin kasuwanci to nan sai acire daya bisa arba'in, idan shekara ta zagayo kuma bayan ta ya nisabi.
- Abunda ake cire wa a teku kamar lu'ulu'u, murjani kifi, wannan babu zakka a kai game da su. Amma ida an tanada ne domin kasuwanci to za'a fitar da daya arba'in idan shekara ta zagayo kuma in sun kai nisabi.
- Tsuntuwa wato abinda ake nufi anan shi ne abunda aka binne a kasa, wato wanda ake hakowa a cikin kasa, to abunda ke wajabi da za'afitar kadan ne ko yana da yawa to shi ne daya bisa biyar wanda zai bada su inda ake sarrafa arzikin kasa, sauran kuma na shi ne.
4. Zakkar kayan kasuwanci: Kuyan kasuwanci shi ne abinda aka ajiye domin saye da sayarwa saboda samun riba kamar gidaje da dabbobi da abin ci da abin sha, kayan alatu da sauran su.
Kyan kasuwanci idan suka kai nisabi kuma shekara ta zagayo za'a cire abunda ya wajaba na zakkah, sai a kimanta kaso mafi tsoka da za'a ba talakawa. Za'a cire daya bisa arba'in daga cikin kimar da aka yiwa asalin dukiyar. Ya halatta kuma a fitar da zakkar kayan kudin daga asalin kayan ba daga kudin ba.
· Idan kuwa mutum ya yi niyyar amfani da kayan kasuwanci ne akaran kansa (kamar motar shiga…) to babu zakkah a cikin ta.
· Kanan dabbobi da ka Haifa da riba da kasuwanci shekararsu to shi ne shekarar asalin su idan ya kai nisabi.
Zakka tana wajaba ne akan dukkan wanda yake:
1. 'Da
2. Musulmi.
3. Wanda ya mallaki nisabi
4. Cikakkiyar mallaka.
5. Kuma shekara ta kewayo a kan su. Wannan idan ba'a abinda aka tono a kasaba.
a. Lokkkaci fitar da zakka.
Yana wajaba a fitar da zakkah da wuri kamar alwashi da kaffara, domin sakakken umarni yana fa'idantar da yi shi cikin gaggawa. Allah madaukakin sarki ya ce: “Ku bada zakka". (Bakarah: 277).
Kuma ya samu ya jinkirta bada ita domin lokacin bukata ko wani dangi na kusa ko kuma makwabta.
b. Hukucin wanda ya ki bada ita: Duk wanda ya yi jayayya game wajibcin zakkah dagangan yana sane to ya kafirta, koda ya bada zakkar, domin ya karya Allah madaukakin sarki da kuma Manzan sa ﷺ da ijmain malamai. Sai dai za'a nemi ya tuba, to idan ya tuba shi kenan idan kuma ya ki sai a kashi shi. Kuma wanda ya hanata don saboda rowa da sakaci za'a kwaceta daga hannun kuma a raba wa mabukata, domin hawa kujerar na ki da ya yi, yara da mahaukata waliyan su ne ke cire musu zakkah.
c. Abun da aka sunnanta wajan fitar da zakkah.
1. An sunnanta bayyanar da ita don ta kawar da rudani.
2. Ya raba ta da kan shi domin ya tabbatar ta isa ga mabukata.
3. Ya fadi wajan rabawa; “Ya Allah ka sanya ta ganima, kada ka sanyata bashi".
4. Ya kamata ga wanda aka ba ya ce; “Allah ya baka lada akan abinda ka bayar, ya kuma sanya albarka a abunda da ya rege na dukiyar, ya kuma sanya shi ya zama mai tsarka ke wa".
5. An sunnanta ya baiwa talakawa na kusa da shi wadanda ciyar da su ba ta kan shi.
Mutanen da ya halasta a baiwa zakkah su kwasne, sune kuma wandanda Allah ya madaukakin sarki ya ambata cewa:
﴿إِنَّمَا ٱلصَّدَقَتُ لِلفُقَرَاءِ وَٱلمَسَكِينِ وَٱلعَمِلِينَ عَلَيهَا وَٱلمُؤَلَّفَةِ قُلُوبُهُم وَفِي ٱلرِّقَابِ وَٱلغَرِمِينَ وَفِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱبنِ ٱلسَّبِيلِ فَرِيضَة مِّنَ ٱللَّهِ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيم٦٠﴾
Ma'ana: “Lalle abin sani kawai ana bada zakkah ne ga talakawa, miskinci, ma'aikatan zakkah, da sabbin shiga addin musulunci don a lalle she su da bayi don a fanshe su, da mai bashi, da mai jihad don daukaka kalmar Allah da matafiyi. Umurni ne daga Allah, kuma Allah mai cikakken sani kuma gwani ne". (Tauba: 60)
1. Talatakawa: sune wadanda ba su da abun da zai wadatar dasu.
2. Miskinai: Sune wadanda ba su da abun sa zai wadatar da su ko da rabi ne.
3. Ma'aikatan zakkah: sune masu daukarta da kiyayeta idan babu masu yi.
4. Wadanda ake rarrashin zukatan su: sune shugabanni daga cikin mutanen su, wadanda suke son musulunci ko son kamewa daga aukawa cikin sharrin su ko, suke son taimakawa don ci gaban addainin musulunci.
5. Domin 'yanta bayi: wadanda suka yi yarjejeniya zasu fanshi kansu daga wajan shugabannin su.
6. Masu bashi: nau'i biyu ne:
i. Masu cin bashi don kawo maslaha tsakanin al'ummah.
ii. Masu cin bashi don su tara amma ba su da abin biya.
7. Masu aiki don daukaka Kalmar Allah: sune wadanda suke yaki don tabbatar da Kalmar Allah da kuma masu da'awah zuwa ga hanyar Allah.
8. Matafiyi: shi ne matafiyi wanda guzurin sa ya yanke, kuma bai samu abin komawa gida ba.
***** ****** ******
1. Hikimar ta:
Daga cikin hikimarta: ita tana tsarkake zukatan masu azumi ne daga abinda ya aikata, kamar yadda ta ke wadatar wa ga talakawa da miskinai da barin roko a ranar idi.
2. Gwargodon abin da ake cirewa da irin abinda ake fitarwa na abin ci.
Gwargodon ta shi ne sa'i daya, sa'i kuma shi ne mudun Nabiyi hudu, kuma ana kadara sa'i da “kilo wat" uku. Ana kuma fitar wa ne da mafi rinjayan abincin da mutanan garin suka fi ci a wannan lokacin, kamar su alkama da bino, shinkafa ko zabib da sauransu.
1. Lokacin da aka wajabta fitar da ita.
Tana wajaba ne da zarar daren idi ya shiga (wato da zarar an ga watan karamar sallah). Lokaci bayarwa kuma yana halasta ne tun kafin ranar sallah da kwana daya ko biyu, domin aikin Abdullahi Dan Umar Allah ya kara musu yarda. Kuma lokaci bayarwan da yake shi ne ya fi daga fitowar alfigir na ranar idi har zuwa dab da sallar idi, domin umurnin Manzon Allah ﷺ da a bada ita ga mutane kafin fita zuwa sallah.
2. Waddanda zakka ta wajaba a kansu.
Ita zakkar fiddakai tana wajaba ga dukkan mutum musulmi 'da ko bawa, mace ko na miji, babba ko karami, wanda Allah ya a zurta da a bincin da ya rage bayan na yini da dare, kuma yana halasta a fitar wa 'dan da ke cikin mahaifa cikin mahaifiyarsa.
3. Wadanda ake ba zakka.
Zakkar kono (fiddakai) ana bada ta ne ga duk wanda ya cancanci a ba shi sauran zakkah daga cikin mutane takwas din nan, amma talakawa da miskinnci sun fi cancanta daga sauran da aka anbata domin fadin Ma'aikin Allah ﷺ : “Ku wadatar da su daga barin roko na wannan ranar".
· Hikimarsa.
· Da kuma hukunce-hukuncensa.
RUKUNI NA HUDU A CIKIN RUKUNAN MUSULUNCI.
1. Ma'anar azumi da lokacin wajibcin sa.
a. Ma'anar Azumi a yaren larabci shi ne; “Kamewa", Amma a Shar'ance: Shi ne kamewa da niyyar bauta daga barin ci da sha da saduwa da kuma sauran abubuwan masu karya azumi, daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana.
2. Tarihin wajabta azumi.
Allah madaukaki ya wajabta shi ne ga al'ummar Annabi ﷺ kamar yadda ya wajabta shi ga sauran al'umman da suka gabata, domin fadin sa Allah madaukakin sarki:
﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيكُمُ ٱلصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبلِكُم لَعَلَّكُم تَتَّقُونَ١٨٣﴾
Ma'ana: “Ya ku wadanda suka yi imani! an wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi ga wadanda suka gabace ku, tsammani zaku samu takwa". (Bakara: 183). Kuma wannan ya kasance ne a watan Sha'aban shekara ta biyu bayan hijira mai albarka.
Azumi na da fa'idoji na zuciya, zamantakewa, da na lafiya. Sune kuma kamar haka:
- Daga cikin fa'idar shi ta ziciya (Ruhi): shi ne yana taimamaka wa wajan samun hakuri, da kuma karfafuwa a kan haka. Yana samar da kamewar kai da kuma taimakawa kai, haka kuma yana samar da kiyaye zuciya daga saba wa Allah mai girma da daukaka da kuma dorata akan tarbiyyar hakan.
- Daga cikin fai'dar zamanta kewa kuwa, yana sabarwa mutane tsari da kokari, da son adalci da daidaituwa akan gaskiya, yana kimsawa mumuni tausayi da dabi'u masu kyau, kamar yadda mutane ke kamewa daga sharri da kuma abin da yake barana ne.
- Daga cikin fa'idar samun lafiyar jiki: yana tsarkake kayan ciki, kuma yana gyara hanji, yana kyauta jiki daga cututtuka kuma yana tsane jiki daga yawan mai (kitse) da nauyin jiki.
Shugowar watan Ramadan yana tabbata ne da dayan lamri biyu: Na farko: Cikkar watan da ya gabace shi (kwana talati) wato Sha'aban. Idan sha'aban ya cika kwana talatin, rana ta talatin da daya yini ne na Ramadan kai tsaye.
Na Biyu: Ganin jinjirin watan Ramadan, idan aka ga jinjirin watan Ramadan a daren talatin na wannan wata. Domin fadin Allah madaukakin sarki:
﴿ فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ ٱلشَّهرَ فَليَصُمهُ ١٨٥﴾
Ma'ana: “Duk wanda ya shaidi (shigar) watan Ramadan to ya azumce shi". (Bakara 185).
Haka kuma da fadin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; “Idan ku ka ga jinjirin wata to ku yi azumi, kuma idan ku ka ganshi ku aji ye, idan kuma an boye muku ta (dalilin giragizai) ku cika shi talatin". (Bukhari, Muslmi).
Idan mutanen wani gari suka ga watan azumi ya wajaba gare su. Kamar yadda yake fitar wata yana sabawa, fitar wata a yakin Asiya daban yake da yadda fitar shi take a yankin Turai da Afrika bah aka yake ba a latin Amirka misali. Da haka ne ko wanne yanki da bangare na duniya suke da hukuncin da ya kebance su. Idan kuma al'ummar musulmai suka yi azumi da ganin wata daya to wannan shi ne abin da ya fi kyautatuwa da bayyana hadin kai da kuma 'yan uwantaka.
Ganin watan mutun daya adali ya wadatar ko biyu, kamar lokacin da Manzon Allah ya halasta ganin watan mutum daya na Ramadan (Muslim ne ya ruwaito). Amma na ajiye azumi (wato watan sallah) sai da ganin adalai biyu, kamar yadda Manzon Allah ﷺ bai halatta ganin adili daya ba a lokacin ajiye azumi.
An wajabta azumin a cikin Alkur'ani ne da Hadisai da kuma Ijma'in malamai, kuma daya ne daga cikin rukunen musulunci, Allah Ta'ala ya ce:
﴿شَهرُ رَمَضَانَ ٱلَّذِي أُنزِلَ فِيهِ ٱلقُرءَانُ هُدى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَت مِّنَ ٱلهُدَى وَٱلفُرقَانِ فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ ٱلشَّهرَ فَليَصُمهُ ١٨٥﴾
Ma'ana: “Watan Ramadan shi ne wanda aka saukar da Alkur'ani a cikin sa, yana mai shiyarwa ga mutane da kuma bayyanar da shiriya da kuma bambamce wa (tsakanin karya da gaskiya), to duk wanda ya shaidi watan daga cikin ku sai ya azumce shi…". (Bakara: 185).
Kuma Manzon Allah ﷺ ya ce: “An gina musulunci ne akan abubuwa biyar: Shaidawa da babu abin bauta wa da cancanta sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, da tsaida sallah, da bada zakkah, da ziyartar daki (wato Hajji), da kuma azumin Ramadan". (Bukari, Muslim).
1. Niyya: ita ce kuduri a cikin zuciya akan kamewa domin bin umarnin Allah, da neman kusanci zuwa gare shi, domin fadinsa ﷺ: “Dukkan aiki na ibada saida niyya …..". (Bukari, Musulim).
2. Kamewa: Shi ne nisanta da duk abin da zai karya azumi na ci ko sha ko saduwa.
3. Lokaci: Abin nufi shi ne yini, shi ne kuma daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana.
Sharudan wajibcin azumi hudu ne:
1. Musulunci.
2. Balaga.
3. Hankali.
4. Iko.
Kuma sharadin ne mace ta tsarkaka daga al'ada jinin haihuwa.
1. Musulunci.
2. Daukar niyya da dadare.
3. Wayo.
4. Yankewar jinin al'ada.
5. Yankewa jini haihuwa (wato jinin biki.
1. Gaggauta bude baki, shi ne kuma bude-baki da zarar an tabbatar da faduwar rana.
2. Abin bude baki ya kasance danyen dabino ko busasshen dabinon ko kuma ruwa, wanda ya fi a cikin ukun wadanan shi ne na farko da na karshe kuma shi ne na karshen su, mai bi musu kuma shi ne na biyun, an so a bude akan wutiri, (wato mara).
3. Addu'a yayin bude bakin, Manzon Allah ﷺ ya kasance yana cewa a lokacin bude-bakinsa: “Ya Allah don kai muka yi azumi, kuma da arzikin ka muka bude baki, saboda haka ka karba mana. Lalle kai ne mai ji kuma masani". (Abu-Dawud).
4. Cin sahur, har zuwa kashe karshen dare, da niyyar azumi.
5. Jinkirta sahur, har zuwa tsagin dare na karshe.
An karhantawa mai azumi wasu al'amura wadanda ke iya jawo lalacewar azumi, amma da yake ita akarankanta ba sa karya azumi kai-tsaye, su ne:
1. Kai makura wajan kurkurar baki da shaka ruwa a hanci lokacin alwala.
2. Sumbata, ita tana tasiri ta janyo sha'awa wanddaa ke bata azumi ta dalilin fitowar maziyi ko ta saduwa ta yadda za ta wajabta kaffara.
3. Yawan kallon mata don jin sha'awa.
4. Tunani a wajan sha'anin saduwa.
5. Shafa mace da hannu ko rungumarta.
1. Ya wajaba ga mai al'ada da mai jinin haihuwa su ajiye azumi.
2. Wanda ke so ya tsamo wani daga halaka da suransu.
3. Matafiyi an halasta masa yin kasru kuma an sunnan ta masa ajiye azumi.
4. Maralafiya wanda ke tsoron cutuwa.
5. Mazaunin gida wanda ya yi tafiya da rana, abunda ya fi shi ne ya yi azumi don fita daga cikin sabani.
6. Mai-ciki da mai shayarwa, wadanda suka ji tsoron cutarwa a karankansu ko a dan su, koda sun ajiye azumi don tsoran 'ya'yan su, waliyan su za su ciyar da miskini a kowanne yini bayan haka za su ranka azumi.
1. Ridda.
2. Mutuwa.
3. Niyyan karya azumi.
4. Kokonto game da azumi.
5. Amai da gangan.
6. Yin allura mai sa koshi.
7. Fitowar jini al'ada ko na haihuwa.
8. Hadiye kaki idan ya kawo baki.
9. Kaho: mai yi da wanda aka yi ma.
10. Fitara maniyyi ta dalilin kallo mai yawa.
11. Fitar maniyi ko maziyi ta sumbanta ko shafa ko istimna'i ko runguma ba tare da saduwa ba.
12. Duk abun da ya isa zuwa makoshi ko makogoro ko kwakwalwa na wani abu mai ruwa ko waninsa.
Wanda ya sadu da matarshi a acikin watan Ramadan ta ga ko ta baya, ranko da kaffara sun wajaba a kanshi, idan dagangan ya aikata. In kuma ya mance ne azumin shi bai baci ba, kuma babu ranko balle kaffara akansa.
Idan aka tilasta wa mace saduwa da rana cikin watan Ramadan ko ta jahilci hukuncin haka, ko ta mance to azumin ta yanan, in kuma an tilasta mata ne to ranko ya wajaba akan ta kawai, in kuma da gangan ta aikata to kaffara da ranko sun wajaba a kanta.
Kaffara: ita ce 'yanta baiwa, idan kuma babu sai a yi azumi na tsawon wata biyu a jere, in kuma ba ya yuwa sai ya ciyar da miskinai sittin, in kuma baida iko to an dauke masa.
Idan mutunm ya sadu da matar sa ta dubura, ranko ya wajaba akansa da kuma tuba zuwa ga Allah.
A sunnanta rankon Ramadan cikin gaggawa kuma ayi shi a jere, in kuma ya jinkirta har wani Ramadan ba tare da wani uzuri ba, to ranko da ciyarwa sun wajaba a gare shi a kowanne yini.
Duk wanda ya mutu kuma yana da bashin azumin alwashi ko alwashin Hajj, waliyan sa su ranka mishi.
- Abubuwan da aka so, ko aka karhanta ko aka haramta na azumi.
a. Abubuwan da aka so na azumi.
An so azumin ranaku kamar haka:
· Ranar arafa ga wanda ba mahajjaci ba. Ita ce ranar tara ga watan Zul hajji.
· Azumin tara da goma, ko goma da sha-daya na watan Muharram.
· Azumi shida na shawwal. (Sittu Sawwal).
· Rabin farkon watan Sha'aban.
· Goman farko na watan zul hajji.
· Watan Muharram.
· Ranakun tsakiya na kowanne wata su ne; sha-uku da sha-hudu da sha-biyar.
· Ranakun litinin da alhamis.
· Azumin kwana daya da hutun kwana daya.
· Azumi ga wanda baida karfin yin aure.
b. Azumin da aka karhanta.
· Ranar Arafa ga mai aikin hajji.
· Ranar juma'a kawai. (wato ba tare da alhamis ko asabar ba).
· Karshen Sha'aban
· Azumin a wadannan ranaku an hana ne hani na karhanci.
Wadanda za'a kawo an hana ne hani na haramci, su ne;
1. Dore: shi ne hada azumin kwana biyu ba tare da shan ruwa ba.
2. Azumin ranar kokwanto.
3. Azumin shekara ba tare da hutawa ba.
4. Azumin mace ba tare da izinin mijinta ba, alhali yana gida.
1. Azumi ranar bukuwan sallah karama ko babba.
2. Ranakun shanya nama (yanyane, ranakun 11, 12, 13 na Zul hajji). ga wanda ba mai tamattu'i da bai sami fidiya ba.
3. Ranakun al'ada da jinin haiuwa.
4. Azumin mara lafiya rashin lafiya mai tsanani wadda yake ji wa kansa tsoron halaka.
- HUKUCE-HUKNCENSA.
- NA'UKANSA.
- SHARUDDANSA.
ITIKAFI.
Ma'anar sa a yaran Larabci: Zama, lizimta, tsayuwa da kamewa a wuri guda.
A sharance: Shi ne lizimtar zama a cikin masallaci domin ibada da wata niyya kebantacciya a yanayi kebantacce.
Hikimar Shar'antuwarsa.
1. Acikin itikafi akwai dauke zuciya daga tunanin duniya, tare da fiskantar da ita ga bantawa Allah da ambaton sa.
2. Sallamwa ga majibincin shi ne Allah madaukaki sarki tare da maida lamari ga Allah da kuma tsayuwa domin samun falala da rahamar sa.
Itikafi ya rabu kashi biyu:
1. Wanda yake wajibi: Shi ne wanda aka yi alwashi, kamar mutum ya ce in na yi nasara a aikina zan yi itikafi na kwana uku. Ko kuma ya ce in Allah ya sa na samu aiki zan yi itikafi.
2. Wanda yake Sunnah mai karfi: Mafifici shi ne mutum ya yi shi a goman karshe na Ramadan.
1. Mai itikafi: Domin itikafi babu makawa saida mai yin shi.
2. Zama a masallaci: Saboda fadin Manzon Allah ﷺ: “Babu itikafi sai a masallacin da ake jam'i". Domin mai itikafi idan ya kasance a masallacin da ake a sallar jam'i zai zama mai shiri da ya cika abunda yake wajibi a kansa, na sallah a cikakkiyar fuska.
3. Wurin yin itikafi: Shi ne wurin da mai itikafi ya kebance ya kuma tabbata domin itikafi.
1. Mai itikafi ya zama musulumi, baya iganta ga kafiri.
2. Ya zama mai wayo, baya iganta ga mahukaci ko karamin yaro.
3. Ya zama a masallaci wanda ake sallar jam'i a ciki, wannan ga maza kenana.
4. Ya zama ya tsarkaka daga janaba, al'ada dajini haihuwa.
1. Saduwa koda babu inzali, domin fadin Allah Ta'ala:
﴿ وَلَا تُبَشِرُوهُنَّ وَأَنتُم عَكِفُونَ فِي ٱلمَسَجِدِ ١٨٧﴾
Ma'ana:“Kuma kada ku rungume su alhali kuma masu itikafi a masallaci". (Bakarah: 18).
2. Tattaunawa game da jima'i, (wato saduwa).
3. Farfadiya da hauka (bukgun aljani) ta hanyar maye ne ko wanin sa.
4. Riddah, fita daga mulunci.
5. Fita daga massallaci ba tare da uzuri ba.
Uzurin da ke sa mai itikafi ya fita daga masallaci naui'i uku ne;
1. Uzuri Na Shari'ah: Kamar uzurin zuwa masallacin juma'ah da idi in ya kasance masallacin ba'a jumu'ah da idi a inda yake itikafi.
Amma dalili anan shi ne: lalle itikafi ana lura ne da yin ya domin neman kusanci zuwa ga Allah madaukakin sarki ta hanyar barin laifi da kuma nesa da laifukan. Shi kuma barin sallar juma'ah da idi laifi ne, wanda ke nisantar da mutum daga Allah.
2. Uzuri Na Dabi'ah: Kamar fitsari, bayan-gida, wankan janaba ta hanyar mafarki, damin ba zai yi wu ya yi wanka a cikin masallaciba. Amma dai da sharadin ba zai dade ba a wajen masallacin, saidai gwargwadon biyan bukatar sa.
3. Uzuri Na Larura: Mutum ya kasance yana tsoron dukiyar sa kar ta lalace, ko kayansa kada su bace, ko kansa idan ya ci gaba da itikafin.
- HUKUNCE HUKUNCEN HAJJI.
- UMARAH.
- DA HUKUNCE-HUKUNCENTA.
RUKUNI NA BIYAR DAGA CIKIN RUKUNEN MUSULUNCI:
1. Ma'anar Hajj.
2. Matsayin Hajj a musulunci.
Aikin Hajj shi ne rukuni na biyar daga cikin rukunan musulunci, wanda shi aikin hajjin aka wajabta shi a shekara ta tara bayan hijira, Allah Ta'ala ya ce:
﴿ وَلِلَّهِ عَلَى ٱلنَّاسِ حِجُّ ٱلبَيتِ مَنِ ٱستَطَاعَ إِلَيهِ سَبِيلا ٩٧﴾
Ma'ana: “Kuma Allah ya wajabta wa mutane ziyartar daki ga mai iko hanya ce madai-daiciya". (Ali Imran: 97).
Manzon Allah ﷺ ya ce: “An gina musulunci akan abubuwa biyar; Shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammad Manzon Allah ne, da tsaida sallah, da bada zakkah, da aikin hajji, da kuma azumin Ramadan". (Bukari da Muslim).
3. Hukuncin Hajji: Aikin hajjii Allah madaukakin sarki ya wajabta shi shi a kan bayin sa sau daya a rayuwa, domin Manzon Allah ﷺ ya ce: “Aikin hajji wajibi ne sau daya a rayuwa, duk wanda ya kara ya zama nafila". (Nasa'i, Da Abu-Dawud suka ruwaito shi).
Kuma Aikin Hajjui shi ne nufin zuwa Makkah domin aiki kebantacce a lokaci kebantacce.
4. Umarah: Ma'anar ta a yaran larabci: Shi ne ziyara.
A Shar'ance: Shi ne ayyuka ne kebabbu wanda aka ambata wurin da ake bayaninta.
Hukuncin ta: Wajibi ce a rayuwa sau daya.
4. Hikimar shar'anta Hajji da Umrah.
Daga hikimar shar'anta su, akwai tsarkake zukata daga zunubai domin ta koma tana maraba da karamcin Allah madaukakin sarki a gidan lahira, domin fadin Manzon Allah ﷺ ya ce: “Duk wanda ya ziyarci wannan daki kuma bai maganganun sha'awar mace ba, kuma bai yi fasikanci ba, to zai koma (gida) kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi". (Bukari, Muslim, Tirmizi da Ahmad).
5. Sharuddan Wajibcin Hajji Da Umrah.
1. Musulunci.
2. Hankali.
3. Balaga.
4. Samun iko, shi ne kuwa kasancewa gurzuri abun hawa maikyau ga irinsa.
5. Cikakken 'yanci, wato ya kasance wanda ba bawa ba.
6. An kara wa mace sharadi daya, shi ne samun muharrami. Idan ta yi hajji ba tare da muharrami ba ta yi laifi, hajjin ta kuma ya yi.
· Idan yaro ya yi niyyar hajji, to hajjin ya inganta a matsayin nafila. Amma zai yi aikin hajji idan ya balaga.
· Idan mutum ya mutu aikin hajji kuma ya wajaba gare shi (wato ya mallaki abin hajjin sai bai yi ba, ko ya yi alwashi) sai a diba daga cikin kudin sa a yi masa aikin hajj da shi.
· Bai halatta wanda bai yi hajjinsa ba ya yi wa wani, amma yana inganta ya wakilta wani ya yi masa a matsayin nafila hajji ne ko umrah.
1. Umarah kadai.
2. Hajj kadai.
3. Hajji da umrah a hade.
4. Aikin umrah da na hajji tare, amma da hutu a tsakani (Tamattu'i).
- Amma yin umurah kadai a sauran kwanaki Sunnah ne, mafi falalar umrah ita ce wacce aka yi tare da hajji ko a Ramadan.
- Amma hajji kadai, shi ne mutum ya yi niyyar hajji kadai babu wata umurah da ta gabace shi ko ya gwama su tare.
- Amma Kirani shi ne ya yi haramin yin hajji da umrah lokaci guda, wanda zai yi aikin sau daya. Watau tawafi daya, da sa'ayi shi ne na hajji shi ne kuma na umrah.
- Amma Tamattu'i shi ne mafi falalar aikin hajji: shi ne kuma mutum ya yi niyyar umurah a cikin watannin hajji, sai ya yi mata sa'ayinta ita umurar, ya yi mata tawafinta, daga nan kuma sai ya cire ihrami daga jikin sa. A ranar takwas ga watan zulhajj sai ya yi niyyar hajji, adai wannan shekarar da ya yi umurar, sai ya kawo aikin hajji na tawafi da sa'ayi da tsayuwa a arafa da sauran su. Hadaya na wajaba ga mai tamatu'i da kitani.
- Hajj na da rukune hudu; ne su ne kuma kamar haka:
(1) Ihrami (Niyyah).
(2) Da Dawafi.
(3) Da Sa'ayi (Safa da Marwa).
(4) Da Tsayuwar Arafah.
Da za'a rasa daya daga cikin rukunan ana to aikin hajji ya baci.
- Umurah kuma na da rukunai ne guda uku, su ne:
(1) Ihrami (Niyya).
(2) Da Dawafi.
(3) Da Sa'ayi (Safa da Marwa). Umurah ba ta cika sai da su. Ga bayanan wadannan rukunan kamar haka:
(1) Ihrami (Niyyah): shi ne niyyar shiga daya daga cikin ayyukan hajj ko umurah, baya ya shiraya tsaf ya cire dukkan kayan jikinsa. (ya yafa tufafin harami idan yana da iko).
Wajiban Harami.
Wajiban harami uku ne, su ne kamar haka:
1. Harami daga mikati: shi ne wuri wanda shari'ah ta iya kance domin yin harami, kamar yadda ya kasance bai halatta ga wanda zai yi hajji ko umurah ya wuce shi ba tare da ya yi niyyah gana nan ba.
2. Cire duk abin da aka dinka: Namiji ba ya sanya tufar da aka dinka ko riga ko wando koda hulace ko rawani, kuma ba zai rufe kansa da komai ba. Kamar yadda ba zai sa huffi ba sai dai in bai samu takalmi ba, haka kuma mace ba za ta sa nikabi ba kuma ba za ta sa safar hannun ba.
3. Talbiya: Ita ce kuma fadin;
لَبَّيْكَ اَللَّهُمَّ لَبَّيْكَ، لَبَّيْكَ لاَ شَريِكَ لَكَ لَبَّيْكَ، إِنَّ اَلْحَمْدَ وَالنِّعْمَةَ لَكَ وَالْمُلْكَ، لاَ شَرِيكَ لَكَ.
Ma'ana: “Ya Allah Ubangiji! Na amsa kiranka, Ya Allah Ubangiji!, na amsa kiranka, ba ka da abokin tarayya, na amsa kiran ka, dukkanin godiya da ni'ima na ka ne da mulki, baka da abokin tarayya".
Mai harami zai fadeta ne lokacin da ya sanya harami, kuma yana mikati tun kafin ya motsa daga wajan da yake. An so ya maimaita ta tare da daga murya da ita wannan Talbiyyar idan namiji ne, da kuma sabuntawa (maimaitawa) a wurin ko wani hawa ko sauka, wajan tsaida sallah ko sallame wa ko lokacin haduwa da yan'uwa maniyyata.
Talbiya tana yankewa ne a lokacin da za'a yi tawafin umurah, kuma ana dakatar da yin ta a lokacin hajji idan ya fara jifa a jamrah.
2. RUKUNI NA BIYU: DAWAFI
Dawafi shi ne zagayan dakin Ka'abah sau bakwai. Kuma yana da sharudda bakwai.
1. Niyya a lokacin farawa.
2. Tsakakuwa daga hadasi da khabasi.
3. Suturta al'aura, domin Dawafi kamar sallah ne fa.
4. Dawafi ya kasance a cikin masallaci koda daga nesa ne da dakin.
5. A sanya dakin gefen hagu.
6. Dawafi ya kasance ya cika bakwai.
7. Ya jeranta tawafin ba tare da rabe su ba, kada y araba tsakanin dawafi idan ba da wata bukata ba (kamar tsaida sallah).
1. Sassarfa (sassaka): Sunnah ce ga namiji banda mata, ita ce mai dawafi ya yi dan sauri yana mai hadawa da gudu kadan a tafiyar sa, (wannan a ukun farko).
Ba'a sunnan wannan sassarfar ba sai a dawafin shigowa Ka'abah kadai, a kuma zagayen ukun farko daga cikin bakwai.
2. Bude kafadar dama: Ba'a Sunnan ta hakan ba sai dawafin Kudum (dawafin farko na shigowarka Makkah) wannan kuma ga maza ne kadai banda mata a duk dawafi bakwai.
3. Sumbatar bakin dutse: A lokacin fara tawafi, kuma an so a yi haka a kowanne zagaye in an samu dama. Haka ma shafar rukunil yamani.
4. Fadin Bismillahi Wallahu Akbar. Allahumma imanan bika, Wa tasdikan bi kitabika, wa-wafa'an bi-ahdika, watti-ba'an li-Sunnati Nabiyyika", a lokacin da zai fara zagaye na farko.
5. Yin addu'a a lokacin dawafi: Ba'a iyankance kuma ba'a ayyana wata addu'a ba, sai dai mai dawafi zai roki abin da Allah ya sawwaka masa, dudda cewa an sunnanta masa fadin a kowanne karshan dawafi:
﴿وَمِنهُم مَّن يَقُولُ رَبَّنَا ءَاتِنَا فِي ٱلدُّنيَا حَسَنَة وَفِي ٱلأخِرَةِ حَسَنَة وَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ٢٠١﴾
Ma'ana: “Ya Allah Ubangijin mu! Ka ba mu a nan duniya abu mai kyau, a lahira ma abu mai kyau, kuma katseratar da mu azabar wuta".
6. Addu'a a Multazam lokacin da aka gama dawafi. Wurin Multazam yana tsakanin kofar Ka'abah hajarul aswad.
7. Sallah raka'ah biyu bayan tawafi; bayan makamu Ibrahim, zai karanta Suratul Kafirun (a raka'ar farko) da Iklas (a raka'a ta biyu) bayan fatiha.
8. Shan ruwan zamzam da kuma zubawa a jiki bayan an gama sallah raka'a biyu.
9. Komawa domin sumbatar bakin dutse kafin zuwa sa'ayi.
3. RUKUNI NA UKU: SA'AYI.
Sa'ayi shi ne tafiya a tsakanin Safa da Marwa zuwa da dawowa, da niyyar bauta. Shi kuma rukuni ne a hajji da umarah.
a. SHARUDDAN SA'AYI.
1. Niyya: domin fadin Annabi ﷺ: “Dukkan aiki yana tare da niyya ne". (Bukhari da Muslim suka ruwaito).
2. Jerentawa tsakanin tawafi da sa'ayi, shi ne ya fara gabatar da tawafi kafin sa'ayi.
3. Jerantawa tsakanin sa'ayin baki-daya, tare da cewa yankewa kadan ba ta cutar wa, musamman ga wata bukata (kamar an fara sallah sai ka bi sallar in an kamala sai ka ciko sa'ayin na ka).
4. Cika zagaye kididdigagggu bakwai. Da zai rage zayaye daya ko wani sashi to da bai wadatar da shi ba. Sai dai hakikanin Magana ita ce ingantuwarsa ya ta'allakane da cikarsa.
5. Aikata shi bayan dawafi ingantacce. Na wajibi ne dawafin ko na Sunah.
b. SUNNONIN SA'AYI.
1. Sauri tsakanin alamomi biyu koraye, a gaban kwarinnan dadadde wurin da Hajara mahaifiyar (Annabi) Isma'il ta yi tattaki (Amin cin Allah ya tabbata a gare su). Kuma Sunnah ce ga maza wanda zasu iya ban da mata da kuma raunana.
2. Tsayuwa akan Safa da Marwa domin yin addua'a.
3. Yin addu'a a kowanne kai da komowa bakwannan.
4. Fadin “Allahu Akbar" sau uku lokacin kowanne hawa Safa da Marwa. Haka kuma da fadin:
لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير. لا إله إلا الله، وحده صدق وعده، ونصر عبده، وهزم الأحزاب وحده.
Ma'ana: Babu abinbautawa da cancanta sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, dukkan mulki nasa ne, kuma gareshi dukkanin godiya take, shi kuma mai iko ne akan komai. Babu abin bautawa da cancanta sai Allah shi kadai yake, ya tabbatar da alkawarinsa, ya kuma taimakawa bawansa, ya rinjayi kogiyoyin kafirci shi kadai.
5. Jerentawa tsakanin dawafi da sa'ayi ba tare da rabewa a tsakanin su ba, in ba da wani uzuri wanda yake shari'ah ba.
4. RUKUNI NA HUDU: TSAYUWAR ARAFAH.
Tsayuwar Arafah shi ne zuwa wurin da ake kira Arafah dan lokaci kadan ko mai yawa, da niyyar tsayuwa don sallar azahar a ranar tara ga watan zul-hijjah har zuwa alfijiri na ranar goma ga watan.
Duk wanda bai samu tsayuwar Arafah ba, to ba shi da aikin hajji sai dai ya yi tahalluli ya mai da shi aikin umarah, sai shekara mai zuwa ya dawo don ya ranka, kuma duk wanda makiyi (abokin gaba) ya hana shi ziyartar daki (bayan ya dakko niyyah daga mikati) to sai ya yi yanka ya cire harami.
Idan kuma rashin lafiya ce ta hana shi ko kayan abin cinsa ne suka kare, to idan ya kasance ya yi sharadi “Aikina zai tsaye ne a wurin da rashin lafiya ya tsare ni" to sai ya warware babu komai akan sa, in kuma bai yi sharadi ba to akwai hadaya akan shi.
Wajiban hajji bakwai ne:
1. Ihrami daga mikati.
2. Tsayuwa a Arafah har magariba ga wanda ya tsaya da rana.
3. Kwanan daren yanka (daren babbar sallah) a muzdalifa har zuwa bayan rabin dare.
4. Kwana a mina a cikin daren kwanikin yanyane.
5. Jifar jamrori a jere.
6. Kwalkwabo ko saisaye.
7. Dawafin ban kwana.
Wajibatan abubuwan biyu ne:
1. Yin harami daga hillu (wato wajan harami) ga mutanan Makka. Haka kuma daga mikati ga wasun su (wadanda ba 'yan Makkah ba).
2. Kwalkwabo ko saisaye.
Duk wanda ya bar rukuni daya daga cikin rukuni to aikin shi bai cika ba sai da shi.
Duk wanda ya bar wajibi zai cika shi ne da jini (wato fidiya), kuma wanda ya bar Sunnah babu komai akan shi.
Mahzurat: Su ne ayyukan da aka hana, wanda idan mai hajji ko umarah ya aikata su to (fidiya wato) yanka ya wajaba a kan shi, ko azumi, ko ciyarwa. To ya huramta ga mai harami namiji ko mace abubuwa kamar haka:
1. Aske gashin jiki gaba daya, wato na kowanne bangare.
2. Yanke kumba (farce).
3. Lullube kai (ga namiji) da fuska ga mace, sai dai idan ga wasu mutane da ba muharramanta ba ne.
4. Namiji ya sa dinkakken kaya shi ne kuwa abinda ake dinka shi a kamannin wata gaba, kamar riga, wando da sauransu.
5. Sanya turarai.
6. Farautar dabbar dake rayuwa a doron kasa wace ake ci.
7. Darin Aure.
8. Saduwa, in ya kasance kafin cire haramine (wato tahalluli) na farko to aikin gaba daya ya baci, kuma yanka ya wajaba, su kuma ci gaba da aikin, amma za su ranka shi a shekara mai zuwa (miji da matar kenan). Idan kuma bayan ya cire ihrami ne (wato tahalluli babba) na biyu kenan to bai baci ba, amma yana wajaba ya yanka akuya.
9. Rungumar mace ba tare da saduwa ba, idan ya yi inzali zai yanka rakuma, idan kuma bai yi inzali ba to zai yanka akuya, amma aikin shi bai baci ba a dukkanin yanayin biyu.
Mace kamar namiji take akan abunda aka amabata, wadanda suka gabata na mahzurat (wato abubuwan da aka hana) sai dai wajan sayan dinkakkun tufafi, za ta sanya wanda ta so, amma banda bayyanar da tsaraici, zata lullube kanta kuma ta bude fuskarta ba za ta rufe ba, sai dai a wurin mazan da suke ba muharramanta ba.
Fita ihrami na farko a aikin hajji yana faruwa da aikata biyu daga cikin abubuwa uku:
(1) Dawafi. (2) Jifa. (3) Aski ko saisaye.
Idan mace mai tamatu'i al'ada ta zo mata kafin dawafi, kuma ta ji tsoran aikin hajji ya kubuce mata, sai ta yi haraminta da shi kirani, sai ta zama mai kirani kenan (hajji da umarah a hade). Mai al'ada da mai jini haihuwa za su aikata duk wani abu da mai hajji yake yi amma banda dawafi (sai idan sun sami tsarki).
Yana halatta mai harami ya yanka dabba kowacce kamar awaki, kaji da sauran su, kuma ya halatta ya kashe dabba mai cutarwa kamar; zaki, kura, damisa da sauran duk wadanda za su cutar kamar yadda ya halatta ya yi farautar dabbobin ruwa kuma ya ci.
Yana haramta ga mai harami da wanda baida harami ya sare bishiya ko ciyawar harami sai dai izkhir, kamar yadda ya haramta a gareshi kashe dabbobin farauta a haramin. Haka farauta a madina da sare bishiya sun haramta, amma babu fidiya a cikin hakan.
Duk wanda ya ke da uzuri da yake so ya aikata daya daga cikin abunda aka hana mai harami ya aikata amma banda saduwa, kamar aski, da sanya dinkakkun tufafi da makamantan haka to ya samu ya aikata, amma zai yi fidiya kuma zai zaba a tsakanin wadannan;
1. Azumin uku.
2. Ko ciyar da miskinai shida, kowanne miskini mudun Nabiyyi guda na hatsi.
3. Ko yanka akuya.
- Duk wanda ya aikata wani abu daga cikin abubuwan da aka hana mai ihrami aikatawa akan ya jahilce hakan, ko ya manta, ko an tilastashi to babu laifi a gare shi, kuma ba zai yi fidiya ba. Domin fadin Allah Ta'ala:
﴿ رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذنَا إِن نَّسِينَا أَو أَخطَأنَا ٢٨٦﴾
Ma'ana: “Ya Ubangijin mu! Kar ka kama mu da abunda (muka aikata) da mantuwa ko da kuskure ……". (Bakara: 286). Abinda yake akansa shi ne ya bar wannan aikin da aka hana shi cikin gaggawa.
Wanda ya kashe dabbar dake rayuwa a doron kasa kuma yana cikin harami, to in ya kasance akwai irin wannan dabbar a cikin dabbobin gida, sai a ba shi zabi, ko dai ya sayi irin wannan dabbar cikin dabbobin gida ya yanka, ya ciyar da naman ga miskinan haram, ko kuma a kimanta ta sai ya sayi abin ci ya ciyar da kowanne miskini mudun Nabiyy guda, ko ya ya yi azumi na a matsayin kowanne mudun-Nabiyyi guda azumi guda.
In kuma dabbar farautar da ya kashe ta kasance wacce babu irin ta a dabbobin gida ne, to sai a ba shi zabi ko dai ya sayi abin ci na kimar dabbar sai ya raba ga mutanen da suke miskinai a harami, ko ya yi azumi a kowanne mudun – Nabiyyi azumi guda.
Fidiyar da mutumin da rungumi matarsa amma bai fitar da maniyyi ba, to fidiyar da zai yi kamar fidiyar wanda ya aikata abinda aka hana mai ihrami aikatawa ne, wato; “Azumi, ko ciyarwa, ko kuma yankan akuya."
- Fidiyar mutumin da ya sadu da iyalanshi kafin fita daga ihirami fita ta farko fidiyarsa rakuma ce, idan kuma bai samu ba to sai ya yi azumin kwana uku a lokacin hajji bakwai kuma idan ya koma ga iyalanshi, idan kuma bayan bayan fita daga ihrami ne fita ta farko, to fidiyarsa kamar fidiyar cire kazanta ce, (wato: Azumi ko ciyarwa ko kuma yanka akuya).
- Ya wajaba ga mai Tamattu'i, da Kirani su yi hadaya idan ba mazauna birnin Makka ba ne, ita ce kuma akuya ko daya bisa bakwai na rakuma, ko daya bisa bakwai na Saniya. Duk wanda bai samu abin da zai yi hadaya ba to sai ya yi azumin kwana uku a lokacin hajji, sa'anan bakwai ya yi bakwai kuma idan ya koma ga gida.
- Wanda kuma aka tsare shi idan bai sami hadaya ba to zai yi azumin kwanaki goma ne sa'annnan ya fita daga ihrami.
- Duk wanda ya maimaita aikata abu guda daya cikin abunda aka hana mai ihrami ya aikata, kuma bayi fidiya to fidiya daya kawai zai yi, (kamar wanda ya yawaita sa riga…), sabanin farauta. Amma duk wanda ya yawaita aikata abunda aka hana kuma suka kasance daban-daban (ba jinsi guda ba), kamar ya yi aski, sa'annan ya yanke akaifa, to shi zai yi fidiya a kowani jinsi.
Mawakit biyu ne:
1. Lokaci – shi ne watannin Shawwal, Zul ka'ada da Zul-hajji.
2. Wuri: - shi ne wuraren da ake daukar niyya ga wanda zai yi aikin hajji ko Umarha. Shi kuma biyar ne:
1. Zul hulaifa: - Shi ne mikatin mutanan Madina da duk wanda ya biyo ta Madinan. Kuma nisan shi daga Makkah kilomita 435, shi ne kuma mafi nisan mikati daga Makkah.
2. Juhufa: - Shi ne mikatin mutanen Sham da Misra da duk wanda ya daidaita da wurin ko ya biyo ta wurin, wani garine da yake kusa da Rabiga. Nisan shi daga Makkah kilomita 180 ne, mutane kuma a yanzu suna daukar harami ne daga Rabigh.
3. Yalamlam:- Shi ne mikatin mutanen Yaman da duk wanda ya ke daidai da su da kuma duk wanda ya biyo ta wajan, Yalamlam wani warine wanda yake nesa da Makkah kilomita 92 ne.
4. Karnul Manazil:- Shi ne mikatin mutanen Najad da Ta'if, da kuma duk wanda ya biyo ta wajan. A yanzu an fi saninsa da Wadil Kabee, tsakanin sa da Makkah kilomita 75 ne. kuma wurin da ake haramin shi ne mafi tuda da Karnul Manazil.
- Zatu Irki:- Shi ne mikatin mutanen Iraki da Khurasan da kuma tsakiya da arewacin Najadu, da duk wanda ya yi daidai da su, da kuma wanda ya biyo ta wajan, shi ma wurin kwari ne, ana kiran wurin a yanzu “Daribatu" tsakanin sa da Makkah kilomita 100 ne.
- Wadan nan sune wuraren da Shari'a ta ware don daukar harami ga dak mutanen da ke wadannan bangarorin da kuma duk wanda ya biyo ta wajan ko ba dan wurin ba ne domin aikin hajji ko umarah.
- Duk Wanda yake a inda gidansa bai kai mikati ba, to mikatinsa shi ne nan inda yake hatta mutanan Makkah za su yi niyyane daga Makkah.
- Duk wanda ya yi nufin aikin hajj daga birnin Makkah to ya yi harami (niyya kenan) daga Makkah. Duk kuma wanda zai yi umarah daga cikin Makkah to zai fita ne zuwa wajan harami daga hillu kenan ta wacce kusurwa ya so, wato wajen haramin Makkah.
- Idan hanyar sa ba ta kan mikati to yadda zai shi ne ya daidaici mikatin da yake kusa da shi. Ko da kuma yana cikin jirgin sama ne ko mota ko kuma na ruwa.
- Ba ya halatta ga wanda zai yi aikin hajji ko umarah ya wuce mikati ba tare da harami ba. Duk kuma wanda ya wuce mikati ya zama dole ya dawo mikati domin yin harami daga wurin. Idan kuma bai dawo wurin mikatin shi ba, to sai ya yi harami anan inda yake amma kuma fidiya ta kama shi, hajjin shi da umararshi sun yi daidai, in kuma ya yi haramin kafin mikati ya yi amma an karhanta hakan.
- Layya: ita ce abin da ake yankawa na daga rakuma, shanu, awaki a ranar yanka (ranar babbar sallah) da kuma ranakun busar da nama da niyyar layya, kuma sunna ce.
Daga bayan sallar idi ne na ranar dabbar sallah ne zuwa karshen ranakun busar da nama (wato: 10, 11, 12 wasu suka kara da: 13).
-An sunnantar da raba naman kashi uku, mutum ya ci kashi daya, ya yi sadaka da kashi daya, ya kuma yi kyuta da kashi daya.
Layya tana da falala mai girma domin abinda ke cikin ta na rabo da anfanuwar talakawa da kuma toshe musu hanyar roko domin bukatun su.
Ba'a layya ko hadaya da komai sai abinda ya kasance na rakumi matashi mai (akalla) shekara biyar. Da shanu maraki (akalla) mai shekara bityu. Da rago mi watanin shida. Da taure mai shekara daya.
-An akuya (da rago, da taure da tunkiya) kowannen su na halattane ga mutum daya, rakumi kuma ga mutane bakwai, Sa kuma shi ma ga mutane bakwai. Kuma ya halatta mutum ya yi layya da akuya ko rakuma ko Sa ga karankansa da kuma iyalansa. Ya kamata abinda za a yi layya da shi ya kasance ba shi aibi.
Ita ce dabbar da ake yanka wa do haihuwa, ita kuma sunna ce. An shar'anta awaki (wato abinda ya shafi raguma tumakai) biyu za'a yanka idan aka haifi namiji, mace kuma daya. Za'a yanka ne ranar bakwai da haihuwa, sai kuma a ambaci sunan jaririn, za'a yi masa aski a kuma yi sadaka da kimanin nauyin gashin (mizani) da kudi, idan ba'a samu an yi (ranar bakwai ba) to sai a yi shi a kwana na goma sha-hudu, in kuma bai samu ba sai a yi a kwana na ashirin-da-daya, in kuma bai samu ba sai aka yi a kowanne lokaci ya yi, kuma an sunnanta cewa ba a karya kashin hakika. Hakika nuna godiya ce ga ni'imar Allah madaukakin wacce take maimaituwa da kuma wani dan mai zuwa.
****** ****** ******
a. Ma'ana: shi ne amfani da iko da kuma yalwa wurin yankar kafirai.
b. Hikimar Shar'anta shi: Jihadi shi ne kolon tozon musulunci, kuma shi ne mafifici a aikin nafila, Allah ya shar'anta shi domin tabbantar manufofi kamar haka:
1. Domin Kalmar Allah ta zamo madaukakiya, kuma addini ya koma ana yi domin sa.
2. Samar da 'yanci ga bani-adam da kuma fitar da su daga duhu zuwa haske.
3. Domin tabbatar da adaci a bayan kasa, da tabbatar da gaskiya da kuma batar da cewa karya karyace, da hana zalunci da barna.
4. Domin yada addinin musulunci, da bada kariya ga musulmi, da kuma maida makircin makiya.
c. Hukincin Jihadi: Jihadi farilla ne na kifaya idan aka samu wadanda suka wadatar suna yi to laifin ya fadi daga sauran musulmai. Yana wajaba ga kowanne mai iko a wadannan halaye masu zuwa;
1. Idan ya isa sahun yaki.
2. Idan makiya suka shigo gari.
3. Idan shugaba ya bada izinin a fita.
d. Sharudan Wajibcin Jihadi.
Musulunci, hankali balaga, mazantaka (wato namiji), lafiya kenan banda maralafiya kamar; gurgu da makanta da kuma samun ciyarwa.
e. Karkasuwar Jihadi: Jihadi ya kasu kashi hudu, su ne:
1. Jihadi Nafs: Shi ne jihadi zai yi wa kansa wajan neman ilimi da aiki da shi da kira zuwa gare shi da kuma hakuri game da cutarwa a kan haka.
2. Jihadin Shaidan: Shi ne tunkude abun da zai sami bawa na shubuha da sa'awar rai.
3. Jihadin kafirai da munafikai: Wannan zai kasance da zuciya da halshe da dukiya da kuma hannu.
4. Jihadin mutane masu zalunci, bida'a da munkirai: Abun da ya fi shi ne ayi da hannu in an kasa sai a yi da harshe in an kasa said a zuciya.
f. Abinda shahidi yake da shi na falala a wurin Allah ta'ala.
Shahidi yana da abubuwa bakwai a wurin Allah. Allah ya gafarta masa a farko jinin da ya diga, ana nuna masa mazaunin sa a aljannah, ana kare shi daga azaban kabari, ana amintar da shi daga firgici mai girma, ana dandana mashi zakin imani, a aura masa matan hurul'ini, kuma ya ceci mutene bakwai daga dangin sa.
g. Ladduban yaki: Daga cikin laduban yaki na musulunci akwai rashin warware alkawari, rashin kashe mata da kananan yara idan ba su yi yaki ba, nisanta daga mamaki da kuma buri, rashin fatan haduwa da makiya, yin addu'a don neman taimako da karfi daga wurin Allah, shi ne kuam: “Ya Allah mai saukar da littafi, mai tafiyar da giragizai, mai tarwatsa kungiyoyi, Ya Allah ka tarwatsa su kuma ka taimake mu a kan su".
An haramta gudu ranar yaki in ba a cikin yanayi biyu ba:
Na daya: Sai domin ja-baya domin kara shrin yaki.
Na biyu: Sai domin koma baya wajan yan'uwa.
h. Ribatattun yaki.
1. Mata da yara ana ribace su (wato ana kamesu).
2. Maza masu yaki, shugaba yana da zabi ko ya sake su ko kuma kowa ya fanshi kansa ko kuma a kashe su.
Yana zama wajiibi ga shugaba ya yi wa sojojinsa jawabi a lokacin fita daga, kuma ya yi hani da nuna kaskanci da kuma karya, kuma ba za a nemi taimako da kafirai ba sai dai da lalura, su yi tanadin guzuri, zu tafi a natse da runduna, ya neman masu masauki mai kyau, ya hana su barna da sabo, ya yi mu su jawabin da zai karfafe su, ya kuma kwadaitar da su akan samun shahada da ya kuma umurce su da hakuri, ya kuma raba rundunar sa zuwa gida-gida, ya nuna musu masana (acikin su) da kuma masu tsaro, ya aike yan liken asiri zuwa ga makiya, kuma ya karawa wanda ya ga ya cancanta cikin sojoji, kuma ya nemi shawarar malamai da masana yaki.
i. Abinda ya wajaba ga sojoji su yi shugaba.
Ya zama wajibi ga sojoji su yi wa shugaba biyayya, kuma su yi hakuri da shi, kuma yaki bai halatta saida izininsa, saidai idan makiya sun afko gari suna kuma tsoron sharrinsa da cutarwarsa. Idan makiya suka nemi a tsagaita wuta, ko kuma sun kasance a watanni masu alfarma to anan musulmai suna da damar kulla yarjejeniyar tsagaita.
****** ****** ******
1. KASUWANCI, HUKUNCE-HUKNCENSA DA KUMA SHARUDDANSA.
2. RIBA, ABIN DAKE KAWO RUSAU DA KARAYAR TATTALIN ARZIKIN JAMA'A DA 'YANKASA, DA KUMA HUKUMCE-HUKUNCEN RIBA.
3. KODAGO, HUKUNCE-HUKUNCENSA DA KUMA SHARUDDANSA.
4. WAKAFI, HUKUNCE-HUKUNCENSA DA KUMA SHARUDDANSA.
5. WASIYYA, HUKUNCE-HUKUNCENTA DA KUMA SHARUDDANTA.
1. KASUWANCI.
a. Ma'anar shi a yare da shari'ah.
Kasuwanci: Asalin Kalmar ita ce “ba'a" kuma shi ne musayar abu mai daraja da wani abun mai daraja, ko bada kaya da karbar da kaya da kuma karbar wani kayan.
Kasuwani a Shari'ah: “Kulla musanye na dukiya wanda zai bada fa'ida na mallakar hakikanin abun ko kum anfanuwa na har'abada ba wai don menan lada ba".
Hukuncin kasuwanci: Kasuwanci abu ne shar'antace wanda aka halatta, Alkur'ani da Hadisi da kuma Ijmai'n malamai duk sun tabbatar da shar'antuwarsa, da kuma masu hankali sun nuna halastin sa.
b. Hikimar halasta kasuwanci:
Kamar yadda kudade da haja da kuma kayayyakin bukata a waste suke a tsakanin mutane, bukatar mutum ta rataya ne ga abun da ya ken a hannun abokin sa, kuma ba ya samun sa ba tare da bada wani abu ba. Daga cikin halatta kasuwanci akwai biyan bukatar sa, da isa zuwa ga gurin sa, Domin haka ne Allah madaukakin sarki ya halllata kasuwanci don tabbbatar da zaman lafiya.
RUKUNAN KASUWANCI SUNE:-
1. Siga: mai saya ya ce “Na saya". Mai sayar kuma yace: “Na sayar".
2. Masu kulla ciniki: mai saya da mai sayar wa.
3. Abunda ake kulla kasuwanci da shi: Kudi da kayan kudi.
Sigar kasuwanci: ita ce na saya, na sayar, da duk wani abun da zai kai ga nuna yarda misali mai kaya ya ce: na sayar, na ba ka, ko na mallaka ma a kaza. Shi kuma mai saya ya ce: na saya, na mallake shi, ko na karba, da makamancin haka. Kasuwamci yana inganta kuma da sigar ta hanyar aikin gefe guda. Haka kuma daga gefe biyun: na mai sayarwa da mai saya.
Ciniki ta hanyar wayar salula.
Tattaunawa akan waya ana la'akari da ita ne cewa hakan shi ne wurin ciniki, don tana karewa ne da karshen buga wayar, domin abin sani a al'adace ana hukunci ne da ire-iren wurin bayanin kulla kasuwanci da zartar da kamala wa.
SHARUDDA BAKWAI NA INGANTANCIN KASUWANCI.
1. A samu yarda a tsakanin mai saya da mai sayarwa ko abin da zai tsaya a madadin su.
2. Halascin tasarrufi tsakanin mai saya da mai sayarwa, ta yadda kowannen su zai kasance 'Da, Mukallafi kuma mai wayo.
3. Ya kansace abin sayarwar ya halasta a yi anfani da shi, don bai halasta cinikin abinda baida amfani ba, haka kuma wanda ya haramta kamar giya, alade, da abinda ba ya anfanar wa, kuma ba ya halasta saidai idan da larura kamar mushe.
4. Ya kasance abin sayarwa mallaka ne ga mai saidawa, ko wanda aka ba tsaron kaya lokacin ciniki.
5. Ya kasance wanda zai sayi kayan ya san abun da zai saya.
6. Ya kasance kudin sannan ne.
7. Ya kasance abin da za'a saida yana hannu, domin ba'a cinikin abin da ba ya hannu, kamar tsuntsun da ke sama da makamanci haka.
SHARUDDA A KASUWANCI.
Sharuddan kasuwanci biyu: ingantacce wanda zai tabbatar, da batacce wanda yake warware ciniki. Ingantacce shi ne wanda kamar anyi sharadin jinkirtar da kudi ko wani bangaran kudin, ko jingina ko kuma samun wanda ya tsaya mishi sananne, domin hakan yana cikin maslahar kulla cinikin, ko kuma sharadin wata siffa a abinda da za'a sayar, saboda Hadisi: “Musulmai suna kan sharadin su". (Ahmad/Abu Dawud).
Ya inganta mai sayarwa ya yi sharadi ga mai saya game da wani anfanin na lokaci sananne abin da ya sayar kamar zama a gida na wata daya, a missali.
Amma sharadi batacce to daga ciki fa akwai wanda ke bata ciniki kamar, daya ya yi sharadi ga dan'uwan shi akan bashi ciniki da canji, dadai sauran su. Daga cikin sharadi akwai ba ya bata ciniki, saidai sharadin yana bata kansane, kuma shi ne lalataccan sharadi, shi ne kuma su yi sharadi da cewa ba za'a samu hasara a gare shi ba duk lokacin cinikin ba, haka ba zai maida shi ko ba zai saida ba ko ba zai kyautar da shi ba, saidai idan ya kasance a sharadin a kawai wata maslaha to anan ya inganta shi sharadin.
CINIKIN DA AKA HANA.
Musulunci ya halatta cinikin dukkan wani abu wanda zai jawo alheri da albarka, kuma ya haramta wasu kasuwanci saboda jahiltar abin, ko yaudara ko cutarwa da 'yan kasuwa, ko da zukata dadai sauransu daga abin dake sabbaba hasada da kyashi da raba kan jama'a, daga cikin akwai:
1. Mulasama: kamar mutum ya ce duk tufafin da ka taba naka ne da kudi kaza, wannan cinikin batacce ne, domin samuwar jahilcin abinda zaka taba da kuma yaudara.
2. Cinikin munabaza: kamar mutum ya ce duk tufafin da ka jehomin to naka ne akan kudi kaza, wannan canikin batacce ne domin samuwar jahilci da yaudara.
3. Cinikin husat: shi ne mutum ya ce ka yi jifa da wannan tsakuwar, duk inda ta fadi ko duk kayan da ta taba naka ne da kudi kaza, shi ma wannan kasuwancin bai inganta ba domin jahiltar dake ciki da kuma yaudara.
4. Cinikin Najash: shi ne mutumin da ba zai sayi kayaba ya yi kari ga kaya da abin da mai saya bai so, shi kuma wannan harramun ne domin wannan.
5. Ciniki biyu cikin daya: shi ne mutum ya ce na sayar maka wannan domin ka sayar min da wannan ko kaima ka saya daga wurina, ko ya ce na sayar maka da wannan a yanzu naira goma in kuma zuwa gobe ne naira ashirin sai kuma su rabu kafin a ayyana akan wanne aka yarda, wannan cinikin bai inganta ba domin cinikin ya ta'allaka ne da na farko, sa'annan na biyu, ba'a kuma tabbatar da kudin sa ba.
6. Danbirni ya sayarwa da dankauye (Dillanci): shi ne cinikin kaya da tsada daga yadda aka san shi a ranar.
7. Cinikin mutum akan na dan'uwansa:- shi ne mutum ya ce ga wanda ke son sayan kaya akan Naira goma, sai ya ce ni ina da irin su zan sayar maka a kan naira tara.
8. Sayar da kaya kafin ka karba.
9. Cinikin ina: - shi ne mutum ya sayar da kaya zuwa wani lokaci, sa'annan kuma ya dawo ya sayi kayan da kudi kasa da yadda ya saya.
10. Cinikin bayan kiran sallah na biyu a ranar jumu'ah ga wanda ta zama wajibi akansa.
***** ***** *****
Hukuncin ta da Rabe-Rabenta.
Hanyoyin da musulunci ya bude domin nisantar riba.
a. Ma'anar Riba a yaran larabci: Ita ce kari da bunkasa, anacewa: Ribar dukiya shi ne idan ta karu kuma ta bunkansa, kuma ya karu sau hamsin. Ana anfani da Kalmar riba ga dukkanin cinikin da ya zama haramtacce.
Riba a gun malaman fikhu: ita ce kari akan wasu abubuwa kebbantattu. Ko kuma; Yarjejeniya ce akan wani abu kebantacce wanda ba'a sani ba a san yanayinsa ba a mahanga ta musulunci a lokacin da aka kulla yarjejeniyar, ko ma tare da jinkiri a abubuwan da za a karba biyu ko daya daga cikinsu.
b. Hikimar Haramta Riba:- musulunnci ya haramta riba ta dalilan abubuwa masu zuwa:-
1. Rashin samun daidaito tsakani wahala da anfanuwa domin kasance wan mai bashi kuma wanda ya ba da ribar, bai yi wani kokari ba, kuma bai yi wani aiki ba, sannan kuma ba ya daukar asara, na abinda ya auku na a kasuwancin ada kuma abinda ya mallaka na riba.
2. Rugujewar tattalin arzikin al'umma, da sababin mai bashi zai dogara ne da riba saboda ha shi ba zai yi wani aiki ba, sa'annan ya sa shi ya zama mai yawan hutawa mai yawan kasala, don kodayin riba da kuma kuntatawa wanda aka ba bashi, saboda neman abinda zai cika ka'idojin riba.
3. Rugujewar kyakkyawar zamantakewa tsakanin al'umma ta sanadiyyar rashin taimako tsakanin mutane, na abunda zai tamaka dole wajan tarwatsa kan jama'ah da yaduwar kyashi da son kai, maimakon taimako da soyyaya da fifita mabukata tsakanin al'umma.
4. Raba mutane zuwa mataki biyu masu jayyaya da juna, matakin masu neman wuce iyaka da masu nuna finkarfi da dukiyoyin su, da kuma matakin talakawa raunana wadanda ake cinye musu kokarin su da wahalar su ba tare da hakkki ba.
c. Nau'in Riba.
Riba ta rabu kashi biyu a wurin mafi yawan malamai:
1. Ribar Nasi'ah: Nasi'ah: ita ce jinkirtawa da bada lokaci.
Ribar Nasi'ah: Ita ce kari akan daya daga cikin kayayyaki domin jinkirta bada kudi zuwa wani lokaci sannane.
2. Ribar fadli: fadli a yare shi ne (kari) kishiyar ragi.
Ribar fadli: Ita ce kari akan daya daga cikin abin da za'a canza, wanda suka zo iri daya (wato jinsi guda), kamar zinari da zinari ko fiye da haka, haka kamar hatsi da hatsi ko fiye da dai makamancin su, na abin da zai haifar da riba a cikin su. Ana kiran shi ribar ciniki ko boyayyiyar riba.
- Imamu shafi'i ya kara nau'i na uku suna kiran ta: Ribar hannu: ita ce kuma jinkirta karbar kaya biyu ko daya daga cikin biyun.
- Wasun su sun kara nau'i na hudu suna kiran shi: Ribar bashi, ita ce wadda saharadin da aka yi ya janyo wani anfani.
- Tare da cewa wadannan rabe-raben ba su fita daga cikin wadanda aka ambato ba, na raben-raben da sauran malamai suka yi ba, domin abin abinda suka ce rbar hannu ko ribar bashi duk zai iya yiwuwa a maidasu zuwa nau'i biyun farko.
Masana tattalin arziki na wannan lokaci sun raba riba zuwa wacce aka batar da wacce ta hayayyafa.
1. Istihaki (Wacce aka batar) ita ce kari akan abin da za'a karba daga abinda aka bayay bashi da aka yi anfani da shi wajan sayan kaya na bukatuwa kamar wanda in babu shi zai iya halaka kamar abinci, abin sha, da magani da sauran su.
2. Intaji (mai hayayyafa) ita ce wadda ake karba akan bashin da akayi anfani da shi wajan ayyuka na habbakar kudin kamar maikata ko aikin gona ko don wata manufa wacce akayi kasuwanci da ita.
Kamar yadda suka rabata (ita ribar) zuwa nau'i biyu;
1. Wacce take ninkuwa: Ita ce wacce ake sanya kari mai yawa.
2. Wacce take karuwa kadan: ita ce wacce ake sanya kari kadan. Musulunci ya haramta duk kowanne irin abin da ke amsa sunan riba, daga kowanne aiki ya kasance ribar fadli ce ko riba nasi'a ko wacce ake anfana ne da yawa ko ba da yawa ba. Koma wacce iri ce ta haramta da fadin Allah Ta'ala:
﴿ وَأَحَلَّ ٱللَّهُ ٱلبَيعَ وَحَرَّمَ ٱلرِّبَواْ ٢٧٥﴾
Ma'ana: “Kuma Allah ya halatta kasuwanci kuma ya haramta riba". (Bakara: 275).
Hanyoyin da musulunci ya bude domin nisantar mu'amala da riba.
Musulunci ya kimtsa wajan shimfida hanyoyi ga mai dogara da riba da kuma hanyoyin da zasu nisantar da mutum daga fuskantar ta. Daga cikisu akwai;
1. Musulunci ya halasta mudaraba: Ita ce hadin guiwam tsakanin mutane, ya kasance dukiyar ta mutum guda ce, aikin kuma jujjuyawata wani daban yake yi, to sai riba a raba riba tare gwargodon abin da aka yi itifaki a kansa. Hasara kuma tana aka uwar kudi ne. Amma masu kasuwanci da ita da maikata ba sa daukar hasara ko kadan, domin kokarin su da aikin su shi ne asararsu.
2. Musulunci ya halatta cinikin kaya wanda za'a yi yanzu amma kayan sai nan gaba, kamar wanda ya matsu baida kudi sai ya yi cinikin wani abu sannane zuwa kaka wanda zai samar, kuma da sharadi wanda aka amba a litafin fikhu.
3. Musulunci ya halatta cinikin na zuwa wani lokaci: shi ne ayi kari akan kudin kaya na abinda za'a sayar kudi hannu, hakika kuma musulunci ya halastta yin hakan domin sauki ga maslahar mutane da kuma nisantar mu'amala da riba.
4. Musulunci ya kwadaitar akan samar kamfanoni domin bayar da bashi mai kyau, shin bashin ya kasance ne akan daidaikun mutane ko jama'ah ko hukuma…., domin tabbatar da tallafawa wajan kyautatuwar zamantakewar al'ummah.
5. Musulunci ya shari'anta bada zakka ga mutane masu bashi da yawa mabukata, da talaka wanda bai da abin da ya mallaka, da bako wanda guzurin sa ya kare da makamaci haka, don kariya da toshe kafa da kuma daga darajar su.
Wadannan sune kofofin ko hanyoyi da musulunci ya budawa kowanne mutum daga cikin mutane domin tabbatar da maslaha sa da kuma kiyaye masa dara jojinsa na mutum, kuma yana daga cikin manufofin ya samu biyan bukatar sa da amintuwa da maslahar sa, da kokari wajan aikin sa da sakamakon sa.
RIBAR BANKUNA DA KUMA HUKUNCINTA.
- Fawa'id: Jam'i ne na fa'ida wanda abinda masana tattalin arziki suke nufi da ita, ita ce kudade masu hayayyafa wadanda bankuna da asusun ajiya ke badawa akan ajiya ko su karba a matsayin bashi, ita ma tana daga cikin riba, bari ma dai ita ce ainihin riba koda sun kirata da fadi'idoji babu shakka ita ce riba da Alkur'ani da kuma Hadisi da Ijma'in malamai.
Kuma hakika malamai sun ijma'i akan haramcin kari wanda aka yi wa sharadi akan bashi. Haka ma abinda suke kira da bashi ba bashi ba ne, sai dai kamar yadda babban malamin nan na Sudiyya wato mufti Muhammad dan Ibrahim -Allah ya yi masa rahma- ya ce “Hakika abinda ake cewa bashi ne to ba bashi ne, domin abinda ake nufi da bashi shi ne kyautatawa da tausayawa, wannan wata abace a bayyane wacce take a hakika sayar da kudadene zuwa wani lokaci, kuma ribar ta ribace sananniya wacce aka yi wa sharadi.
Da wannan zamu lura da cewa wasu kudade wadanda bankuna ke karba akan bashi ko su bada ga masu ajiya ta yi daidai da riba ciccif, dukkan su suna bada ma;anar kari, saboda haka ya inganta ayi anfani da kowanne suna madadin daya, (domin dai ma'ana daya suke bayarwa bashi-da-ruwa).
a. Ma'anar ijarah (haya): ita ce yarjejeniyace akan wani anfani sannane wanda aka halasta.
b. Hukunci ta:- Ta hallasta; Ita ce kuwa tabbatacciyar yarjejeniya daga bangarori biyu.
c. Hikimar shar'anta ta: Haya akwai musanya wacce take anfanarwa tsakani mutane, wacce suke bukatuwa zuwa gare ta. Suna bukatar ma'aikata domin aiki da kuma gidaje domin zama, da ababen hawa motoci da wasu kayayyaki domin daukar kaya, hawa. An halasta haya domin saukaka wa mutane da kuma biyan bukatun su.
d. Haya nau'i biyu ce:
1. Ta kasance akan abu ne wanda ake gani, kamar na baka hayar wannan gidan ko motar.
2. Ta kasance akan aiki ne kamar wanda za'a nema don mutum ya gina kataga ko noma da makamata haka.
e. Sharadin Haya.
Shardin haya hudu ne:
1. Ta kasance abune wanda aka halasta juyawa.
2. Sanin anfaninsa, kamar gidan haya, ko hidimar da mutum zai yi, ko karantar da karatu.
3. Sanin abin da za'a biya.
4. Ta kasance wacce aka halasta anfani da ita, kamar gida domin zama, baya halatta a bada haya domin haram kamr gida don karuwanci, waka, ko ya bada gidan shi haya domin coci ko domin sayar da giya da makamantan haka.
MAS'ALA:- Idan mutum ya hawau mota, ko jirgin sama ko na ruwa ko ya bada yadi don a dinki ko ya nemi dan-dako ba tare da ciniki ba wannan ya yi akan abinda mutane suka al'adantu da shi, abin da mutane suka sani ba sai sun yi ciniki ba, sannan wanin cinikin na tsayawa madadin cinikin.
d. Sharadin abinda za'a bayar haya.
An yi sharadi akan abin da yake tabbatace wanda za'a bada haya, ya zama an san shi ta hanyar gani ko siffarsa, za'ayi ciniki ne akan anfaninta ba wai akan bangarorinta ba, kuma ya zama yana da ikon mika ta, kuma ta kunshi duk abin anfanuwa, ta kuma kasance mai bada hayar shi ke da ita, ko wacce aka izinin hakan.
e. Mas'aloli akan haya.
- Yana inganta ayi haya da abin da aka yi wakafi da shi, idan mai haya ya rasu sai ya koma ga wanda ya zo bayan shi ba za'a warwareta ba, na biyun yana da kasonshi na hayar.
- Duk abinda aka haramta cinikin sa to an haramta hayar sa, saidai abinda yake wakafi, da 'Da da kuma uwar' 'Da (ummu wala).
- Haya tana bacewa da talalacewar abida aka bayar haya, da kuma yankewar anfain abin da ake haya domin shi.
- Ya halassta a karbi ladan karantarwa, da na ginin masallaci da makamanta su. Amma aikin hajji (da wani zai yi wa wani) ya halatta ya karbi ladan idan akwai bukatar hakan.
- Idan liman ya karbi wani abu ko ladan ko malami mai karantar da Alkur'ani daga baitul mali ko aka ba shi ba da sharadi ba ya halatta ya karba.
- Mai aikin kodago ba ya biyan abinda ya lalace a hannunsa matukar bai yi sakaciba kuma bai wuce iyaka ba.
- Haya tana tabbata da zarar an kullata, yana kuma zama wajibi a bada kudin haya da zarar an bada abinda aka karba haya, idan kuma suka yarda akan bada lokaci nan gaba, ko kuma biya kadan-kadan ya halatta. Mai aiki yana cancantar a bashi hakkinsa da zarar ya gama aikin sa.
****** ****** ******
Ma'anar shi: A yare da wurin malaman fikhu.
Alwakfu an samo shi ne daga wakafa, jami'insa kuma shi ne Aukaf ana cewa ya tsaida abu, kuma ya kiyaye shi kuma ya bada shi. Duk ma'ana daya ce.
Amma wurin malaman fikhu: Shi ne tsare asalin abu, tare da bada sadakar anfaninsa sa.
1. Asalin yadda aka shar'anta wakafi.
Wakafi sunnace tabbataciya daga Mazon Allah ﷺ, haka kuma ijmai malamai. Amma abin da ya tabbata a sunnah shi ne daga cikin Bukhari da Muslim lalle Umar t ya ce: “Ya Manzon Allah! Lalle na samu dukiya a Khaibar irin wacce ban taba samun irin ta ba a rayuwa ba, me zaka umurce ni da in yi da ita?. Sai Ma'aikin Allah ﷺ ya ce: “In ka so ka tsare asalin ta, ka yi sadaka da ita ba tare da an sayar da asalin ta ba, kuma ba za'a kyautar ba, ba kuma za'a gada ba". (Bukhari, Muslim, Tirmizi, Nasa'i, Abu Dawud, Ibn Majah, Ahmad). Sai Umar ya sadaukar da ita talakawa da dangi na kusa da bayi da kuma, sabida Allah da matafiya da kuma baki, babu laifi ga wanda yake kula da ita da ya ci daga ciki ba tare da barna ba.
Kuma wakafi yana cikin abubuwan da suka kebanci musulumi ne kadai, Jabir t ya ce: “Babu wani daya daga cikin shabban Manzon Allah ﷺ wanda yake da iko face sai da ya yi wakafi".
Kuma wannan ke bayyana mana abin da mutane ke kansa yanzu shi ne akasin abin da aka sani a zamanin sahabbai, da yawan mutane yanzu babu abin da suka sani sai wasiya ba su san wakafi ba."
1. Hikimar Shar'anta Wakafi.
1. An kwadaitar ga duk wanda Allah ya yalwata masa dukiya daga cikin musu kudi da su kara biyayya ga Allah ta hanyar yawaita yin da'a, su yawaita neman kusaci ga Allah ta hanyar ware wani abu na dukiya tsayayyiya abinda asalinshi zai dawwama kuma anfaninshi ya ci gaba, domin tsoron kada dukiyar ta koma hannun wadanda ba za su iya kulawa da ita ba, bayan rasuwa, kuma zai iya kiyaye wa ba, sai ya share ayyukansa don kar ya wayi gari a karshe 'ya'yan na sa su zama cikin wadanda za'a taimaka musu saboda fatara, domin kaucewa wadannan hasashen da kuma tarayya a cikin aikin alheri aka shar'anta wa mutum wakafi a lokacin rayuwar sa, domin mai wakafin ya sa ido da kansa, kuma ya sanya shi awajan da yake so ya sanya shi da kansa, ya kuma jibinci kulawa da shi da ci gaba da bada alheransa bayan ya rasu kamar yadda yake yi a lokacin yana raye.
2. Babban shi ne babban abinda ya sanya tsayuwar masallatai da makarantu da kamanta haka na ayyukan alheri da kuma kiyaye su, domin mafi yawan masallatai a tsawon tarihi sun samu ne wajan wannan wakafi, kai saidai ma duk abunda masallaci yake bukta shimfida ne da tsaftacewa da kuma wasu da tallafi da ake ba masu kula da shi bai gusheba ana karfafarsa ne da wakafi.
4. Lafuzan Wakafi.
Wakafi na da lafuza bayyanannnu ga su kuma kamar haka:
1. Na bada (abu kaza) a matsayin wakafi.
2. Na tsare shi daga magada.
3. Na bada shi Fi sabilillahi.
Amma lafuzan kinaya su ne kamar haka:
1. Na bada sadaka.
2. Na haramta wa kaina shi.
3. Na bada shi har'abada.
Lufuzan kinaya suna kasancewa ne da daya daga cikin abubuwa uku:-
1. Niyya idan ya yi furuci, kuma ya yi niyya da daya daga cikin wadannan lufuzan kinya to ya zama wakafi.
2. Idan lafuzan suka yi kusanci da daya daga cikin lufaza bayyanannu ko na kinaya kamar na sadaukar da wani abu a matsayin wakafi da sauran su.
3. Ko ya siffanta wani abu tabbatacce na kadarar sa da siffofi kamar haka: (Abu kaza) ya haramta (a gareni) ba'a sayarwa kuma ba'a kyautarwa, kamar yadda muka bayyana a halin kinaya da sauran su, kuma yana tabbata ta hanyar ayyuka kamar mutum ya gina masallaci a filin sa sannan ya kira mutane zuwa a yi sallah.
5. NAU'UKAN WAKAFI.
Wakafi ya rabu ta fuskar da aka lura da shi kamar fuskar farko wadda ta sanya shi nau'i biyu:
1. Khairu.
2. Ahly.
1. Wakafin Khairy: shi ne wanda za'a yi wakafi tun farkon lamari akan fuskar alheri ko-da-ko lokaci ne kayyadajje, sai bayan haka ya kasance wakafi ga mutum sannane ko mutane sanannu, kamar ya yi wakafi da filin sa ga asibiti ko makaranta sannan bayan haka ga yaran shi su dauka daga baya.
2. Wakafi Ahly Ko na zuriya: shi ne wanda za'a yi wakafi tun farko lamari ga wani mutum sannane ko wasu mutane sanannu, sai kuma a sanya karshen sa alheri ne kamar ya sanya shi ga kansa sannan 'ya'yansa sannan a bar shi ga ayyukan alheri.
6. Abuwan Da Ake Wakafi Da Su.
Akwai dukiya tabbatacciya wacce za'a iya kimantata, fili, gida, wannan duk malamai sun yi ijma'i akansa. Ko wanda za'a iya dauka kamar; Littattafai da tufafi, dabbobi da kuma kayan yaki. Domin fadin Manzon Allah tsira da ammincin Allah su tabbata a gare shi: “Amma Khalid, to lalle ku kuna zaluntar Khalid, lalle shi ya tsare silkenshi na yaki kuma ya tanadar da shi ne saboda ayyukan daukaka Kalmar Allah". (Bukhari).
7. Sharuddun Wakafi.
An yi shardi ga wanda zai yi wakafi idan ya dace da shari'ah to ya yi in kuma bai dace ba to bai yi ba.
1. Ya kasance ya cancanci bayarwa, ba na fashi ba ne, ba kuma ya saya ba ne amma bai karba ba domin ya mallake shi tabbatacciyar mallaka ba.
2. Ya kasance wanda zai yi wakafi mai hankali ne, ba ya halatta wakafin mahaukaci ko mara wayo da sauran su.
3. Ya kasance ya balaga, ba ya halatta wakafin karamin yaro, daidai ne ya kasance mai wayo ne ko mara wayo.
4. Ya kasance mai lura ba ya halatta ga wawa ko gafallale.
8. SHARUDAN ABUBUWAN DA ZA'A YI WAKAFI DASU.
Ko domin wakafi ya kasance wanda za'a zartar akan abinda aka yi wakafin domin shi aka shardanta wadannan sharudda:
1. Ya kasance dukiya ce tsayayyiya, kamar gida ko waninsa.
2. Ya kasance an iyakance abun da aka yi wakafi da shi.
2. Ya kasance abunda aka yi wakafi da shi an mallake shi lokacin da aka yi wakafin.
1. Ya kasance abunda aka yi wakafi da shi sananne ne ba'a wakafi da abunda ba'a sani ba.
2. Ya kasance abunda za'a yi babu hakkin wani a ciki.
3. Ya kasance zai anfanar idan aka yi wakafi.
4. Ya kasance anfanuwar abun wakafin ta halatta.
9. YADDA ZA'A AMFANA DA ABUN DA AKAYI WAKAFI.
Ana anfana ne da abin da akayi wakafi kamar gida abun hawa, nano, kawi da kuma wabar na dabba.
10. BAN-BANCI TSAKANIN WAKAFI DA WASIYA.
1. Lalle shi wakafi yana tsare asalin dukiya ne, da kuma bada sadakar anfanuwar. Wasiya kuma ita ce mallakar da abun amma bayan mutuwa, ta hanyar bayarwa ne a abunda ya kasance ga shi kuru-kuru ko kuma amfanarwa ne.
2. Wakafi yana lizimtar mutum kum ba'a maida shi (ace an fasa) a fadin malamai ba'a bota ilimi, domin fadin Manzon Allah ﷺ ga Umar t: “Idan ka so sai ka tsareta ka yi sadakar asalinta. Sai kuma ya yi sadakar ."
Amma wasiyya tana lizimta kuma yana halatta ga wanda ya yi wasiyya ya janye wasiyyar ko kuma wani sashi nata.
3. Wakafi yana fitar da mallakar ainihin dukiya ga wanda ya bada ita ga wani sai dai tana kebanta ne ga abun da ake anfanuwar sa da wakafin.
Ita ko wasiyya tana sa mallakar ainihin dukiya ga wanda aka yi wa wasiya. Ko anfanin ta yana komawa ne ga wanda akayi wa wasiyyar.
4. Mallakar da anfanuwar wakafi hukunsa yana bayyana ne a lokacin da me wakafin yake raye da kuma bayan ya mutu. Shi kuma mallakar da wani a wasiyya ba ya bayyana sai bayan mutuwar wanda ya yi wasiyya.
5. Wakafi baida haddi akan mafi yawan sa, ita kuwa wasiyya ba ta wuce daya bisa uku na dukiya akan kayan gado.
6. Wakafi yana halatta ga wanda zai ci gado, wasiyya kuma ba ta halatta ga wanda zai ci gado, sai idan sauran magada sun yarda.
***** ****** ******
a. Ma'anar wasiyya:
Wasiyya: Ita ce umurni da sarrafa dukiya bayan mutuwa, da ta kunshi bada amana da bada kyaura dukiya, aurara da 'ya'ya mata wankan mamaci da yi mishi sallah da raba daya biya uku sauransu.
b. Asalin shar'antuwar wasiyya: Asalin ta yana cikin littaffin Allah ne da Sunnah da kuma ijmain malamai. Allah ta'ala ya ce:
﴿كُتِبَ عَلَيكُم إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ ٱلمَوتُ إِن تَرَكَ خَيرًا ٱلوَصِيَّةُ لِلوَلِدَينِ وَٱلأَقرَبِينَ بِٱلمَعرُوفِ حَقًّا عَلَى ٱلمُتَّقِينَ١٨٠﴾
Ma'ana: “An wajabta a kan ku, idan mutuwa ta zo wa dayan ku in ya bar wani alheri (to ya yi) wasiyya". (Bakarah: 180).
Manzon Allah ﷺ ya ce: “Wanne hakki ne na mutum Muslmi da zai yi wasiyya da shi zai yi kwana biyu ai face sai wasiyyarsa ta kasance a rubuce". (Bukari).
c. ABINDA AKE KULLA WASIYYA DA SHI.
1. Ibarah (Jumla).
2. Rubutu.
3. Nuni wanda ake fahimta.
Na farko:- Ibarah (wato jumla): Babu wani sabani tsakanin malaman fikhu wajan kulluwar wasiyya da lafazi bayyananne, misali ya ce; na yi wasiyya ga wane da kaza. Ko a samu zance wanda ba bayyananne ba amma ana iya fahimtarsa a matsayin wasiyya, kamar mutum ya ce na sanya ma wane abu kaza bayan mutuwa ta, ko ku shaida na yi wa wane wasiyya da abu kaza.
Na biyu: Rubutu, idan mutum ya kasa fadi sai ya rubuta kamar kurma, da mai nauyin harshe da sauran su.
Na uku: Nuni wanda ake iya fahinta, ana kulla wasiyya ta haka, idan aka samu masu karyyayun harshe da su yi nuni tare da sharadi ba za su iya Magana ba.
d. Hunkunci wasiyya.
Wasiyya an shar'anta ta kuma an yi umurni da ita, Allah madaukakin sarki ya ce:
﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ شَهَدَةُ بَينِكُم إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ ٱلمَوتُ حِينَ ٱلوَصِيَّةِ ٱثنَانِ ذَوَا عَدل مِّنكُم أَو ءَاخَرَانِ مِن غَيرِكُم إِن أَنتُم ضَرَبتُم فِي ٱلأَرضِ فَأَصَبَتكُم مُّصِيبَةُ ٱلمَوتِ تَحبِسُونَهُمَا مِن بَعدِ ٱلصَّلَوةِ فَيُقسِمَانِ بِٱللَّهِ إِنِ ٱرتَبتُم لَا نَشتَرِي بِهِ ثَمَنا وَلَو كَانَ ذَا قُربَى وَلَا نَكتُمُ شَهَدَةَ ٱللَّهِ إِنَّا إِذا لَّمِنَ ٱلأثِمِينَ١٠٦﴾
Ma'ana: “Ya ku wadanda suka yi imani! shaidu a tsakanin ku idan mutuwa ta zo muku lokacin da kuke wasiyya mutane biyu ne"……(Mai'da:106).
e. Nau'in Wasiyya:
1. Wasiya wajiba: tana wajaba akan wanda ke da bashi sannan akwai hakkoki na amana a kanshi da kuma alkawura, yana wajaba akan shi da ya rubuta su duka rubutun da zai bayyana bashi na yanzu ko na nan gaba, da duk wani abu da yake tare da shi na amana ne ko na alkawura, domin magada su kasance akan lamarin da yake a fili a lokacin da za'a yi tasarrufi da ita da kuma abunda aka wakilta shi akai.
2. Wasiyya wacce take Sunnah.
Wannan ita ce wacce aka kwadaitar da mutane su yi da daya bisa uku na dukiya, ga wanda bai cikin magada, wannan mustahabbi ne a ayyukan biyyaya da kuma hanyar alheri, ta kasance ne ga dangi ko wanda ba dangi ba, ko wani bangare kebantacce da aka ayyana kamar masallacin wane, ko kuma gamamme wanda ba'a kebanceba, kamar masallatai da makarantu, da dakunan karatu, da wuraran 'yan gudun hijira da wuraran shan-magani.
f. Gwargwadon abunda ake wasiyya da shi.
Wasiya ba ta halatta idan ta wuce daya bisa uku na dukiyar marayu, domin fadin Manzon Allah ﷺ ga Sa'ad lokacin da ya ce: “Na yi wasiyya da dukkanin dukiya ta?. Sai Manzon Allah ﷺ ya ce: A'a, ya kara cewa; Na yi wasiyya da rabin dukiya ta?. Sai Manzon Allah ﷺ ya ce: A'a. Sai ya ce da daya bisa uku. Sai Manzon Allah ﷺ ya ce daya bisa uku yana da yawa". (Bukhari/Muslim).
Baya halasta ga mutum ya yi wasiyya ga mai cin gado, ko ga wani fiye da daya bisa uku na dukiya saida yardar magada.
g. Abinda ake lura da shi wajan ingancin wasiyya.
1. Ta kasance anyi ta akan adalci.
2. Ta kasance akan yadda Allah ya shar'anta ta a harshen Annabinsa ﷺ.
3. Ya zama akan me wasiyyar ya tsarkake aikinsa domin Allah, kuma ya nufaci ayyuka na alheri da dukiyar ta sa.
h. Abinda aka shardantawa wanda zai yi wasiyya.
1. Ya kasance ya cancanci ya bada kyauta.
2. Ya kasance wanda ya mallaki abinda zai bada wasiyyarshi ne.
3. Ya yarda kuma da ganin damarsa ne.
i. Abinda aka shardantawa wanda za'a yi wa wasiyya.
1. Ya kasance an yi ne akan taimako kuma halasne.
2. Ya kasance wanda za'a yi wa wasiyyar yana nan lokacin wasiyyar a hakikance ko a kaddarance, akan haka wasiyya tana yiwuwa akan abinda babu.
3. Ya kasance mutum ne sananne.
4. Yakasance mutum ne da zai iya mallaka da cancanta.
5. Ya kasance ba wanda ya yi kisa ba ne.
6. An shardanta wanda za'a yi wa wasiyya kada ya zama yana cikin masu gado.
j. Abinda aka sharadantawa kayan da za'a yi wasiya da shi.
1- Ya kasance dukiya ce wacce za'a iya gada.
2-Ta kasance dukiyar da za'a yi wasiyyah da ita za'a iya kimantata a shar'ance.
3- Ta kasance dukiyar da za'a iya mallakar ta, ko da alokacin wasiyyar babu ita.
4- Ya kasance abinda za'a yi wasiyya da shi mallaki na wanda zai yi wasiyya a lokacin wasiyyar.
5- Kada abinda za'a wasiyya da shi ya kasance laifi ne ko abinda aka haramtaa shari'ah,
k. Tabbatar da wasiyya.
Malamai sun yi ittifakin Sunnancin a rubuta wasiyya, kuma a fara ta da sunan Allah, da godiya ga Allah da Alhamdu da makamancin haka, da salati ga Annabi ﷺ, sannan bayyanar da shahada a rubuce ko ya furuta ta bayan bismillah da Alhamdulillah da Salati ga Annabi ﷺ.
l. Nau'ukan masu wasiyya. Nau'ukan masu wasiyya uku ne.
1. Wasiyyar shugaba.
2. Wasiyyar Alkali.
3. Mai wasiyyar da ka zaba daga cikin al'ummar musulmai.
m. Abubuwan da ke bata wasiyya.
1. Janye wasiyya da bayani a fili ko bayani mai nuna janyeta.
2. Ratayar da wasiyya akan wani sharadi da bai tabbata ba.
3. Rashin barin wani abu wanda zai kasance cikin abin wasiyyar.
4. Gushewar ikon mallakar mai wasiyya.
5. Riddar wanda ya yi wasiyya yabar musulunci a wurin wasu malamai.
6. Kin karbar wasiyyar daga wand aka yi wa wasiyyar.
7. Mutuwar wanda aka yi wa wasiyya da yake sananne kafin mutuwar wanda ya yi wasiyyar.
8. Wanda aka yi wa wasiyya ya kashe wanda ya yi wasiyyar.
9. Hallakar abinda aka yi wasiyya da shi da yake sananne, ko ya bayyana na wani ne.
10. Wasiyya tana baci idan wanda a ka yi wa wasiyya yana cikin magada, kuma magada ba su tabbatar da ita ba.
****** ***** *****
- AURE.
- DA HUKUNCE-HUKUNCENSA.
- DA KUMA SHARUDDANSA.
KASHI NA UKU.
AURE.
HIKIMAR SHAR'ANTA AURE.
1. Aure na daga cikin sunnonin musulunci wanda Manzon Allah ﷺ ya kwadaitar ya ce: “Ya taron matasa duk wanda ya samu iko na ba'a to ya yi aure, domin shi ya fi rintsewa ga ido, kuma ya fi tsare wa ga farji, saboda haka duk wanda bai samu iko ba ina to ya yi azumi domin lalle shi ne kariya gareshi".(Jama'ah).
- Daga cikin hikimar aure.
1- Aure dabi'ah ne mai kyau, yana taimakawa wajan hada kan ma'aurata, ya sa su kulla soyyaya da tausaya wa juna da kuma kare su daga haramun.
2- Aure hanya ce ta alheri wajan samun 'ya'ya da yawaita dangi tare da kiyaye dangantaka.
3- Aure shi ne hanya ce mafi kyau wajan biyan bukatar 'da namiji da 'ya mace, tare da wasu cukutuka na zamani ba.
4- A aure akwai: Kosar da bukatuwa yaro na samun uwa da uba.
5-A aure akwai natsuwa tausayawa da debe kewa tsakanin ma'aurata da sauran su.
Ma'anar aure ayaran Larabci da shari'ah.
Aure a yare: Shi ne saduwa, da hadawa tsakanin abubuwa biyu, hakika kuma ana anfani da shi akan kulli.
Aure a shari'ah: Shi ne kulli ne da ake lura da shi wajan lafazi da akwai aure ko na aurar acikin jumlar, kuma abinda aka kulla akai shi ne anfanin jin dadi ko na tarayya.
An sunnanta wa wanda yake da yawan sha'awa kuma ba ya tsoron afkawa zina. An wajabtawa wanda yake tsoranta. An halastawa wanda baida sha'awa, kamar mai guntun gaba da babba, kuma an haramta aure a garin da kuke yaki da su ba tare da wata lalura ba.
Sigar Aure.
Ana daura aure da ko wanne irin lafazi wanda yake nuni da shi, da kuma kowanne yare sai a ce: Na aurar ko ya ce : Na karbi wannan auren, ko na yarda. Kuma an so a yi shi da harshen Larabci, wanda kuma ba su san shi ba sai ya yi da yaren sa.
Rukunan Aure:
Aure nada rukune biyu:
1. Bayarwa: shi ne lafazin da waliyli zai furta, ko wanda ya wakilce shi da lafazin aure ko na aurar, domin sune lafuza wanda Alkur'ani ya zo da su, Allah Ta'ala ya ce:
﴿ فَٱنكِحُواْ مَا طَابَ لَكُم مِّنَ ٱلنِّسَاءِْ٣﴾
Ma'ana: “Ku auri abin da ya yi maku dadi daga mata". …….(Nisai:3).
2. Karba:- shi ne lafazin da miji zai furuta ko wakilin sa da fadin cewa: Na karba ko na yarda. Kuma ya kasance bayarwa ya riga lafazin karba zuwa sai dai inda wani abu da ka lura da shi.
SHARUDAN AURE HUDU NE.
1. Tabbatar ma'aurata biyu tukunna.
2. Yardar ma'aurata, ba ya halatta a tilasta daya daga cikin su akan sai ya auri dayan. Za'a nemi izinin budurwa da bazawara, izinin budurwa shi ne shiru, bazawara kuma Magana, ba'a shardanta hakan bag a mahaukaci ko maimatsalar magana.
3. A samu waliyyi, an yi sharadi da ya kasance na miji 'da, baligi, mai hankali mai lura, adali. An shardanta addini ya zamo daya, baban mace shi ya fi cancantar ya aurar da ita, sannan wanda aka yi wa wasiyya, sannan Kakanata mahaifin uba, har sama. Sannan 'dan ta koda lissafin ya yi kasa (jika, jikan-jika…), sannan 'dan'uwanta uwa-daya-uba daya, sannan dan'uwanta uba-daya, sannan 'ya'yansu a hakan, sannan baffa (kanin baba ko uwan shi) na 'uwa-daya-uba-daya, sannan baffa na uba-daya, sannan 'ya'yan su, sannan wanda ya fi kusa a dangi, sannan sarki.
3. Shaidu, Aure ba ya inganta sai da shaidu biyu, adilai, maza, wadanda hukunce hukunce suka hau kansu.
4. Samun ma'aurata da babu wani da zai hana auran.
Abunda aka sunnanta da wanda aka haramta a aure.
- An sunnanta auren mata daya idan mutum ya ji tsoron adalci, addini, wacce ba kabila guda ba, budurwa, hai huwa, kyakkyawa.
- Ya halatta ga wanda ke neman aure ya yi dubi matar da zai aura ba tare da ta bude al'urar ta ba, da kuma abun da zai jawo shi zuwa ga auranta, ba tare da sun kebanta ba, haka ma mace ta kalli wanda za ta aura.
- Idan bai samu damar ganinta ba sai ya aiki wata matar da za ta yi mu'amala da ita don ta zo ta siffanta masa ita, ya haramta ga namiji ya yi neman aure kan neman dan'uwa sa har sai ya bari ko ya yi masa izini.
- An halatta bayyanannen bayani ko jurwaye mekama da wanka a wajan neman mace wadda aka sake ta saki daya ko biyu wanda ke nisantar da ita ga mijinta wanda ma bai kai ukun ba.
- Ya haramta a nemi auran matar da aka saketa sakin da za'a iya kome to ya haramta a bayyana nemanta ko ayi jurwaye mai kama da wanka, muddin tana cikin iddarta.
- An sunnanta daura aure aure ranar jumu'ah da yamma, domin akwai wani lokaci mai albarka wanda ake karbar addu'a, kuma an sunnanta a yi a masallaci in ya sawwaka.
HUKUNCE-HUKUNCE NA MUSAMMAN DA SUKA KEBANCI MACE MUSULMA.
Gabatarwa:
Yayin da Shari'ar musulunci take Magana da mukallafai, kuma hakan ya kasu kashi uku:
1- Kashin da ya kebanci maza kadai.
2- Kashin da ya kebanci mata kadai.
3- Kashin da suke tarayya a cikinsa.
Na so cikin wadannan masa'ala in ambaci mahinman hukunce-hukunce fikhu wadanda suka kebanci mace, da kuma hukunce hukunce masu girma wadanda mata da maza suka yi tarayya a ciki na ambace su a cikin kashi na uku tuntuni.
Ga bayanan kamar haka:-
MAS'ALOLI DA SUKA KEBANCI MACE.
MAS'ALA TA FARKO:
Hukuncin shafa akan baruki (shi ne gashin da mata suke dorawa akai), sanya baruki ya halatta idan akwai bukatar hakan.
Idan mace ta bukaci sanya baruk, lalle ba za ta yi shafa a kan shi ba a lokacin alwala, domin ba dan kwali ne ba ne, tunda babu makawa sai ta yi shafa akanta ko a gashin da Allah ya halitta mata.
MAS'ALA TA BIYU:
Jan-farce (kumba): wasu matan suna gangganci wajan sanya jan-farce kumba ko fanti a kumba, wanda yake hana shigar ruwa zuwa fata, wannan bai halasta ba, saidai ansa sharadin sa shi a lokacin da take da tsarki, ta kuma cire shi lokacin yin alwala.
MAS'ALA TA UKU.
Jinin Al'ada: Shi ne jini wanda ke fitowa daga gaban mace ahalin lafiya ba tare da sababin haihuwa ko bari ba.
Mafi yawan malaman fikhu suna ganin cewa yana faraway ne idan mace ta kai shekara tara, idan ta ga jini kafin ta shiga wannan shekarun to ba ya kasance wa jinin al'ada, sai dai jinin ciwo da rashin lafiya. Hakika yana daukewa a karshen rayuwa, a galibin lokaci kuma yana daukewa ne yayin da mace ta kai shekara hamsin.
Yana da nau'i shida: baki, ja, fatsifatsi, gurbatacce, tsanwa, da ruwan kasa.
Mafi karancin kwanakin al'ada shi ne dare da yini, matsakaici kuma kwana biyar, mafi yawan kwanakin kuma sune goma sha-biyar, saidai galibi shi ne kwana shida ko bakwai.
Mafi karancin tsarki kuma wanda shi ne ke raba tsakanin al'adar da ta wuce da wadda zata zo kwanaki goma sha-uku ne, a galibin lokuta yana kasancewa fiye da haka ko kasa da haka.
Al'ada tana hana mace ta yi sallah, azumi, shiga masallaci, karatun alkur'ani, tawafi da saduwa kamar yadda yake alama ce ta balaga.
MAS'ALA TA HUDU.
Jinin haihuwa: Shi ne jinin da ke fitowa daga farjin mace bayan haihuwa, ko fitowar mafi yawan 'da (lokacin haihuwa) koda kuma bari ne da halittarsa ta ciki.
Tsawon kwanakin sa shi ne galibi dai kwanaki arba'inne, idan mace ta haifi 'yan-biyu sai ta lura da jinin 'da na farko ba na biyu ba (kenan daga na farko za'a fara lissafi).
Jinin haihuwa yana hana abun da al'ada ke hana wa a musulunci.
Jinin istihala (jinin ciwo): Istihala shi ne zubar jini ba tare da lokaci na al'ada ba, ko jinin haihuwa ba, daga kasan jijiya (Rahim), duk abin da ya karu bayan kwanakin al'ada ko haihuwa ko ya takaita akan mafi karancin sa ko ya fito kafin shekarun fara al'ada shekaru tara – wannan istihada ne. Hukunncin sa hadasi ne a kowanne lokaci ba ya hana sallah ko azumi.
Mai istihala zata yi alwala domin yin kowacce sallah. Ya halasta mijin ta ya sadu da ita. Shi kuma jinin da mace mai juna biyu ta gani zata girga shi ne cikin jinin istihala.
An hana mace ta aske gashin ta saidai idan a kawai bukata. Ya haramta ga mace ta aske gashin gira ko ta yi tsaga, karin gashi, da tsaga wushirya, domin manzon Allah ﷺ “Ya la'anci mai aikatawa da wacce ake yi wa". (Mutane bakwai suka ruwaito.).
Ya haramta ga mace ta sa turare sai dai ga mijinta ko cikin tsakaninta mata.
Al'auran mace: Duk jikinta al'aurane a wurin maza wadanda ba muharamanta ba, ya wajaba a gare ta ta kare kanta daga maza kamar yadda ba ya halatta gareta ta kebanta da na miji wanda ba muharaminta ba.
Kuma ba za ta yi tafiya ba sai tare da muharramin ta, shi ne wanda ya haramta a gareta har abda saboda wani dalili halattacce na dangantaka ko surukuta ko shayarwa.
Mace zata suturta jikinta a salllah sai dai fuskarta da tafin hanunta da kuma diga diganta, yana wajaba gareta ta rufe su idan ta kasance wajan akwai maza wadanda ba muharramanta ba, an so ta rufe tafikan hannuwanta da kuma digadikanta a kodayaushe.
Sutarta ta tufafi sune kaya sakkaku ba matsatsu ba, wanda bai yi kama da kayan maza ba, kar ya zama wanda ake ganin jikin ta mai jan hankali, kar kuma ya yi kama da na kafirai, kuma kar ya zama kayan neman shuhura.
Mace tana da ado wanda halatta a gareta da kuma wanda ya haramta gareta. Zinari da azurfa turare, Hariri da mus'safir sun halatta a gareta.
Yana haramta a gareta ita mace yin ado wanda manufarsa shi ne neman shuhura da ji-da-isa, da kuma wanda zai ja hankalin mutane su kallaceta wanda zai sa su yi ta jin kanshinta, da kuma rangoda a gaban wanda ba muharramin ba.
Muryar mace ba al'aura ba ce, saidai idan ta rangwadata siranta ta kuma yana fitinar mutane, ta kuma tsawaita hakan. Amma wakarta haramun ne, sai kuma gashi mafi yawa a yanzu sun yawaita a zamaninnan na mu suka dauke shi hanyar tare dukiya. Waka ta haramta ga maza, kuma haramcin ya fi tsanani ga mata. Yana halatta ga mace alokacin bukukuwa da lokuta idi a cikin su su mata kadai, da lafuzan masu kyau wadanda babu gurmi a ciki.
Yana halatta ga mace ta yi wa yaranta kanana da mijinta wanka, kamar yadda ya halatta ta yi sallar janaza yadda maza ke yi, saidai ba ya halatta bin gawar da rakata makabarta, kuma bai halatta a gareta ziyartar makabarta, an hana ta kuma kukan mutuwa da tuge gashi da marin kumatu da yaga wuyan riga da tsige gashi, duk wadanan na daga cikin aikin maguzanci (jahiliyyah), kuma yana daga cikin manyan zunubai.
Ba ya halatta ga mace ta ta yi takaba ga wani fiye da kwanaki uku, amma ga mijinta yana wajaba ta yi wata huda da kwana goma, ta zauna a gidanta, ta nisanci ado, da sa turare, ba'a kuma iyakance mata kayan da zata sa ba.
Yana halatta ga mace ta yi ado da abin da Allah ya halasta, na daga zinari da azurfa akan abinda al'ada ta sani, kuma yana wajaba gareta ta nisanci barna da girman kai akan haka.
Babu zakka akan zinari da azurfa idan ya kasance tana anfani da su ne na yau da kullum ko saboda bukukuwa.
Yana halatta ga mace ta yi sadaka da wani abu na dukiyar mijinta ba tare da izinin sa ba akan yadda al'ada ta gadar idan ta san zai yarda da haka, yana halatta ta bashi zakkar dukiyar ta idan ya kasance yana cikin wadanda suka cancanta ne. Idan mujinta ya kasance marowaci ne baya ciyar da ita abin da yake wajibi, yana halatta gareta ta dibi abin da ya zai isheta da 'ya'yanta akan karantarwar addini.
MAS'ALA TA GOMA SHA UKU.
Yana halasta ga mace mai juna-biyu ko mai shayarwa ta sha azumi, idan ta ji tsoron cutuwar danta ko kanta, yana wajaba a gareta ta ranka ne kawai a cikin wannan halin banda ciyarwa. Amma idan ta ji tsoron danta to za ta ranka kuma ta ciyar. Wannan ya danganta ne ga mace juna-biyu, ita kuma mai shayarwa, idan yaron ya karbi nonon wata matar wacce zata shayar da shi, sai ta bada shi, amma ba zata ajiye azumin ba, kuma hukuncin shayarwar shi ne hukuncin uwar.
Ba ya halasta mace ta yi azumin nafila ba tare da izinin mijinta ba in yana gida.
MAS'ALA TA GOMA SHA HUDU.
Ba ya halatta ga na miji ya hana matar sa sauke faralin hajji, idan ta nemi izinin hakan, ya kuma taimaka mata wurin sauke wannan farali, ammma hajjin nafila yana halasta ya hanata idan hakan zai daba maslaharsa da ta yayanta.
MAS'ALA TA GOMA SHA BIYAR.
Mace zata sanya tufafin ta da ta saba sakawa a gida a lokacin harami (da hajji ko da umarah), saidai zata kiyaye lokacin ihrahimta wadannan abubuwa:
1. Tufafin da akwai turare.
2. Safar hannu.
3. Nikabi.
4. Matsattsun tufafin.
MAS'ALA TA GOMA SHA SHIDA.
Mace mai jin haihuwa da al'ada za ta yi wanka kuma ta yi harami, sai ta yi duk aikin hajji amma banda tawafi sai in ta sami tsarki.
MAS'ALA TA GOMA SHA BAKWAI.
An shar'anta yin talbiya ga mahajjata. maza suna daga muryarsu da ita talbiyar, mata kuma suna asurtawa. Ba ya halasta mace ta yi sassarfa a dawafi ko sa'ayi, kuma ba za ta daga muryarta ba a lokacin addu'a ba, kuma ba za ta bi cunkoso da turmatsetseniya ba a wajan hajrul aswad ba ko wanin sa.
MAS'ALA TA GOMA SHA TAKWAS.
Aski da saisaye ayyukka ne a hajji da umarah, saisaye yana kasancewa ga mace a matsayin aski sabanin namiji, saboda ba ya halatta ga mace ta aske gashin kanta.
Siffar yadda za ta yi saisaye shi ne ta yanke ko wanne kulli gwargwadon gabar yatsa (anmula), ko kuma ta kama gashinta idan ba ta da kitso sai ta yanke shi gwargodon gabar yatsan.
An so a gaggauta dawafin farilla ga mata tun a ranar yanka, idan tana tsoron gabatowar al'adarta. Sayyidatu Aisha ta kasance -Allah ya kara mata yarda- tana umrtar mata da su gaggauta dawafin farilla ranar yanka don tsoron al'ada, domin mai al'ada ba ta dawafi na bankwana, idan ta yi dawafin farilla, idan ta kasance lokacin fitarta daga Makkah tana al'ada.
Ba ya halasta ga mace musulma ta auri wanda ba musulmi ba, daidaine ya kasance mushiriki ne ko dan'kwaminisanci ko buda ko wanin sa, ko daga cikin Ahlul kitab (wato kirista ko bayahude), domin namiji na da hakki tsayyaye akan matar sa da ta yi masa biyayya, wannan shi ne ma'anar shugabanci, ba ya halasta ga kafiri ko mushiriki ya samu iko da fada-a-ji akan wanda yake shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammad ﷺ Manzon Allah ne.
Reno: Shi ne tsayuwa da kula da kananan yaro ko yarinya ko wadanda ba su da wayo.
Uwace ta ke da hakin renon yaro ko yarinya, kuma ana tilasta mata idan ta ki, wacce take biye da ita a wannan tsarin ita ce mahaifiyarta (kaka kenan), sannan sai kakani mata na kusa, sai na kusa, sannan sa uba, sannan sai iyayanshi mata (iyayan uba, kakannin yaron), sannan sai kaka, sannan sai iyayanshi (kakannin kakannin yaron kenana), sannan 'yar'uwa uwa-daya-uba-daya, sannan 'yar'uwa uwa-daya, sannan sai 'yar'uwa uba-daya, sannan gwaggwanni, sannan innoni, sannan innonin mahaifiyarsa, sannan innonin mahaifinsa, sannan gwaggwannin babansa, sannan 'ya'ya mata na 'yan'uwansa, sannan 'ya'ya mata na baffanninsa, da gwaggwanninsa, sannan 'ya'ya mata na baffannin babansa, da 'ya'ya mata na gwaggwanninsa, sannan sauran dangi maza na bangaren uba wanda ya fi kusa, sannan sauran dangi makusanta (na bangaren uwa), sannan kuma sai hukuma.
Yana wajaba ga uba ya bada ladan kulawa idan an bukaci haka. Kuma an shardanta ga wanda zai yi reno: Balaga, da hankali, da iko akan tarbiya, da amana, da kyawawan dabi'u, da musulunci, kuma kuma kada ta kasance mai aure, idan kuma ta yi aure to hakkinta na reno ya fadi, idan kuma yaron ya kai shekara bakwai sai a basa hi zabi tsakanin iyayan na shi, sai ya zauna da wanda ya zaba. Ita 'ya mace babanta ne ya fi karfin hakki akanta bayan shekara bakwai har ta yi aure ta tare.
Malaman mazahabobi hudu sun yi ittikafi akan wajibine mace ta rufe jikin ta gaba daya a gaban maza wadanda ba muharamanta ba, daidaine da wadanda suke ganin fuska da tafukan hannu al'aura ne ko ba al'auraba, kuma ma wadanda suke ganin fuska da tafukan hannu ba al'aura ba ne suna ganinsu al'aura ne a wannan lokacin, domin domin yadda barna ta yadu, da kuma sako-sako da suke yi da addinin su, da kuma rashin kulawarsu wurin kallon mace kallo na haramun.
Wannan shi ne abunda ya sawwaka wurin tarashi da kuma wallafa wa, a wannan aiki na gaggawa, ina mai rokon Allah madaukaki mai iko, ya anfanar da shi wannan aiki. Allah shi ne wanda yasan niyya, shi ne kuma mai shiyarwa zuwa ga hanya madaidaiciya.
Dr. Salihu Ibn Ganim AsSadlan,
Malamin fikhu a kwalajin Shari'ah, Riyad.
Kammalawar ta kasance ne a farkon,
Zul hijja, shekara ta 1413. B.H.
(May, 1993).