×

ƘAYATA GURAREN ZAMA Taƙaitattun Darussa cikin abubuwan da bai kamata Musulmi ya jahilce su ba. (Hausa)

shiryawa:

Description

Wanda ya wallafa wannan littafin ya tattaro abubuwa masu mahimmanci da bai kamata Musulmi ya jahilce su ba a cikin Aƙidah, hukunce-hukunce, kyawawan halaye da mu'amaloli tsakanin Mutane. Ya rubuta littafin da uslubu (salo) mai sauƙi, kuma ya yi amfani da Luga (yare) da kowa zai iya fahimtarsa cikin sauƙi. Ya kuma tsara littafin ya kasa shi zuwa gajejjerun babuka; saboda Mai karatu ko Mai karantar da shi ya samu sauƙi. Fatanmu wannan littafin ya amfani Musulmi gaba-ɗaya. - Mai-gida ya kamata ya rinƙa karanta shi tare da iyalansa lokaci bayan lokaci, zai yi kyau ya ƙara da wani littafin da ya san zai amfane su. - Limami zai iya karantar da Mamunsa wannan littafin bayan Salloli. - Mai wa'azi zai iya ɗaukan wannan littafin domin ya samu abin da zai gabatarwa mutane a wurin wa'azin nasa. - Gidanjen Talabijin da Rediyo za su iya samun abin da za su gabatar da shirye-shiryensu a ciki. - Mutum Musulmi namiji ko mace za su iya amfani da wannan littafin ta hanyar karatunsa su kaɗai ko tare da 'yan'uwa da abokan karatu. Da wasu hanyoyin ma ban da waɗanda muka ambata.

Download Book

معلومات المادة باللغة العربية