×
جدبد!

تطبيق موسوعة بيان الإسلام

احصل عليه الآن!

تعريف موجز بالإسلام (هوسا)

إعداد: Scientific Research Admission of Islamic University, Madinah Munawara

الوصف

التعريف الموجز بالإسلام: تعريف موجز بالدين الإسلامي وبيان شموليته لجميع جوانب الحياة مع بيان أهم أركانه الستة.

تنزيل الكتاب

    تعريف موجز بالإسلام

    بلغة : الهوسا

    Introduction to Islam in Hausa Language

    DA SUNAN ALLAH MAI MATUKAR RAHAMA DA

    MATUKAR JIN KAI

    TAKAITACCEN BAYANI GAME DA MUSULUNCI

    Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah; Ubangijin talikai, sannan salati da taslimi ga shugaban manzanni; Annabinmu MUHAMMADU, hada da gabadayan alayensa da sahabbansa. Bayan haka.

    Shi dai MUSULUNCI, shi ne sakon Allah na karshe - daga jerin sakwanninSa - zuwa gabadayan al'umma, wanda Ya saukar da shi ga cikamakon annabawanSa; MUHAMMADU DAN ABDULLAHI, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

    MUSULUNCI shi ne addinin gaskiya wanda Allah ba Ya karbar wani addini daga wani mahaluki in ba shi ba. Kuma, hakika Allah Ya sanya shi addini sassauka da ba wata wahala a cikinsa; don bai wajabtawa mabiyansa abin da ba za su iya ba, bai kuma dora masu abin da ya fi karfinsu ba.

    Hakanan, MUSULUNCI addini ne da kadaita Allah ne tushensa, rahama ruhinsa, gaskiya takensa; ya tsaya a kanta tsayin-daka, kamar yadda ya ke cike makil da adalci, zuwa gareshi yake kira, kuma a kansa yake kaiwa yake komowa.

    Harwalau, MUSULUNCI shi ne addinin nan mai girma wanda yake fuskantar da bayin Allah zuwa ga duk wani abu mai amfani a garesu a addininsu da duniyarsu, yake kuma gargadinsu daga duk wani abin da yake mai cutarwa ne a garesu a addininsu da rayuwarsu.

    Haka zalika, MUSULUNCI shi ne addinin da Allah Ya gyara akidu, da halaye, da rayuwar duniya da ta lahira da shi. Da kuma shi ne ya gyara tsakanin soye-soyen ran da suke a rarrabe, da zukatan da suke nesa da juna. Ta haka ne ya tseratar da su daga duffan bata zuwa hasken shiriya, ya kuma yi masu ja-gaba zuwa hanya madaidaiciya.

    Sannan - bayan dukkanin abubuwan da suka gabata - MUSULUNCI shi ne tsayayyen addini, wanda aka kyautata shi matuka gaya cikin kafatanin labarurrukansa, da daukacin hukunce-hukuncensa. Babu wani labari da ya bayar sai da gaskiya, kuma ba bu wani hukunci da ya yi sai da alheri da adalci, daga ingantattun akidu, da kyawawan ayyuka, da halaye mafifita da ladubba madaukaka.

    MANUFAR SAKON MUSULUNCI

    Manufar sakon musulunci ita ce tabbatar da wadannan abubuwa:

    (1) Sanar da mutane Ubangijinsu (mahaliccinsu) ta hanyar ilmantar da su sunayenSa wadanda suke iyaka ne wajen kyau, da sifofinSa wadanda suke sun kai kololuwa wajen daukaka, da ayyukanSa cikakku.

    (2) Kiran bayin Allah zuwa bautar Allah Shi kadai, ba shi da abokin tarayya (wato su aikata abubuwan da ya wajabta masu su kuma bar wadanda ya hane su). Kuma wannan bauta ce kadai za ta gyara masu duniyarsu da lahirarsu.

    (3) Tunatar da su halinsu, da makomarsu bayan mutuwarsu, da kuma abubuwan da za su gamu da su a kaburburansu, da kuma lokacin tashinsu daga cikinsu ranar kiyama suna rayayyu, hada da lokacin yi masu hisabi, da kuma tuna masu makomarsu cewa dayan biyu ce: ko dai aljanna ko wuta.

    GINSHIKAN MUSULUNCI

    Ginshikan musulunci da suka fi muhimmanci a takaice su ne:

    GINSHIKI NA FARKO: AKIDA

    Wato imani da jiga-jigan imani guda shida:

    JIGO NA FARKO: IMANI DA ALLAH

    Wannan kuma ya kunshi abubuwa masu zuwa:

    (1) IMANI DA RUBUBIYYAR ALLAH

    Wato imani da cewar ba wani ubangiji, mahalicci, mamallaki, mai gudanarwa da sarrafa al'amuran bayinsa sai shi.

    (2) IMANI DA ULUHIYYAR ALLAH

    Wato imani da cewa Shi kadai ne abin bauta na gaskiya; duk wani abin bauta ba shi ba, karya ne.

    (3) IMANI DA SUNAYEN ALLAH DA SIFOFINSA

    Wato imani da cewa tabbas Allah Yana da sunaye masu matukar kyau, da cikakkun sifofi masu matukar daukaka, a tabbatar masa da su kamar yadda suka zo a Al-Kur'aninSa da sunnar manzonSar.

    JIGO NA BIYU: IMANI DA MALA'IKUN ALLAH

    Mala'iku manyan bayi ne da Allah Madaukakin Sarki Ya halicce su, Ya kuma dora masu ayyuka daban-daban, su kuma suka mika wuya gareshi, suna masu yi masa biyayya, kamar yadda suke bauta masa ba-dare-ba-rana.

    Daga cikin wadannan Mala'iku akwai:

    1- JIBRILU, wanda aka wakilta wajen sauko da wahayi, yana sauko da shi daga Allah zuwa wanda Allah din Ya so na daga AnnabawanSa da ManzanninSa.

    2- MIKA'ILU; wanda a ka wakilta wajen ruwa da tsirrai.

    3- ISRA'FILU; wanda a ka wakilta wajen busa kaho lokacin da komai da kowa zai mutu, da lokacin tashinsu daga kaburburansu ranar kiyama.

    4. MALAKUL MAUTI (MALA'IKAN MUTUWA); wanda a ka wakilta wajen karbar ran duk wanda zai mutu.

    JIGO NA UKU: IMANI DA LITTATTAFAN ALLAH

    Ba shakka Allah Mai matukar daukaka da buwaya Ya saukar da littattafai ga manzanninSa. Duk wata shiriya, da alheri, da gyara suna cikinsu.

    Wadanda muka sani daga cikin wadannan littattafai su ne:

    1. ATTAURAT; Saukakken littafin Allah zuwa Annabi MUSA ﷺ‬ kuma shi ne littafin Bani Israa'ila mafi girma.

    2. AL-INJIL; Saukakken littafin Allah zuwa Annabi ISA ﷺ‬

    3. AZZABUR; Wanda Allah Ya bai wa Annabi DAWUD ﷺ‬

    4. SUHUFU IBRAHIM; Na Annabi IBRAHIM ﷺ‬

    5. ALKUR'ANI MAI GIRMA; Littafin da Allah Madaukakin sarki Ya saukar da shi zuwa Annabinmu MUHAMMADU ﷺ‬, karshen annabawan Allah, sai Allah Ya shafe daukacin littattafan da suka gabata da wannan Al-Kur'ani, kamar yadda Ya yi alkawarin kare shi; don kuwa zai wanzu hujja a kan gabadayan halitta har zuwa ranar kiyama

    JIGO NA HUDU: IMANI DA MANZANNI

    Ba shakka Allah Madaukakin Sarki Ya aika manzanni zuwa bayinSa. Na farkonsu dai shi ne Annabi NUHU ﷺ‬, na karshensu kuma Annabi MUHAMMADU ﷺ‬.

    Gabadayan manzannin Allah mutane ne, 'yan Adam; halittarsu aka yi; ba su da wani abu daga cikin abubuwan da Allah Ya kebanta da su (kamar yin arzuki, ko ruwa, rayawa ko matarwa ... d.ss) domin su bayi ne daga bayin Allah, Allah Ta'ala Ya girmama su da aiko su da Ya yi da sakonSa.

    Allah Madaukakin Sarki Ya rufe aiko da sakwanninSa da sakon da Ya aiko MUHAMMADU ﷺ‬ da shi, Ya kuma aiko shi zuwa daukacin mutane. Babu wani annabi bayansa.

    JIGO NA BIYAR: IMANI DA RANAR LAHIRA

    Ranar lahira ita ce ranar kiyama da ba wata rana bayanta. Ranar da Allah zai tashi mutane daga kaburburansu suna rayayyu, don wasu su wanzu a gidan ni'ima (ALJANNA) wasu kuma a gidan azaba mai matukar radadi (WUTA).

    Imani da ranar lahira shi ne: Imani da duk abubuwan da za su kasance bayan mutuwa, daga tambayar kabari, da ni'imarsa da azabarsa, da kuma duk wani abu da zai kasance bayan wannan hali, kamar raya matattu da tashinsu daga kaburburansu, da hisabi, har dai a kai ga shiga Aljanna ko Wuta.

    JIGO NA SHIDA: IMANI DA KADDARA

    Imani da kaddara shi ne mutum ya yi imani da cewa hakika Allah Ya kaddara duk wasu abubuwa da za su kasance tun kafin kasancewarsu, ya kuma samar da daukacin halittu kamar yadda ya rigaya a iliminSa, kuma yake kunshe a cikin hikimarSa.

    Dukkanin abubuwa sanannu ne kuma rubutattu a wurin Allah Ta'ala, shi Ya so samuwarsu, kuma shi Ya samar da su.

    GINSHIKI NA BIYU: JIGAJIGAN MUSULUNCI

    Shi dai musulunci ginannen addini ne daga wasu jigajigai guda biyar, mutum ba zai zama musulmin gaskiya ba sai ya yi imani da su gabadaya da zuciyarsa, yana mai aikata su da gabbansa.

    WADANNAN JIGAJIGAI SU NE

    JIGO NA FARKO: KALMAR SHAHADA

    Wato:

    شهادة ألا إله إلا الله وأن محمداً رسول الله

    “SHAHADATU AN LA ILAHA ILLA ALLAH, WA ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH". Shahada ita ce mabudin musulunci, kuma tushensa da a ka a za harsashinsa a kanta.

    Abin da a ke nufi da الإله shi ne abin da a ke bautawa.

    MA'ANAR: شهادة ألا إله إلا الله “LA ILAHA ILLA ALLAH" Babu wanda ya cancanci a bauta masa sai Allah Shi kadai, Shi ne abin bautawa na gaskiya, kuma duk wani abin bautawa ba shi ba, karya ne, kuma shirme ne.

    MA'ANAR: شهادة أن محمدا رسول الله “SHAHADATU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH" Ita ce: Gaskata MUHAMMADU MANZON ALLAH ﷺ‬ cikin duk abin da ya fada, da aikata duk abin da ya ce a yi, da barin duk abin da ya ce a bari, kar kuma a kuskura a bautawa Allah sai da abin da ya shar'anta.

    JIGO NA BIYU: SALLOLI

    Salloli ne guda biyar, kowa ce da lokacinta. Allah Ya yi horo da su don bayi su ba shi hakkinSa, su kuma gode ni'imominSa. Kamar yadda ta ke wata kullalliyar alaka ce tsakanin musulmi da ubangijinsa, da ya ke kiransa a cikinta, ya ke kuma ganawa da shi.

    Hakanan, Allah Ya shar'anta su don su hana musulmi aikata alfasha da miyagun ayyuka.

    Bayan haka, alherin addini da gyaran imani, da ladan Allah na duniya da lahira duk Allah Ya rataya su da wadannan salloli. Ka ga musulmi ya samu abin da zai ba shi jin dadin duniya da na lahira; mutane su na cikin damuwa a zukatansu da jikkunansu, shi kuwa garau ba abin da ya dame shi, kullum ya na cikin walwala da annashuwa.

    JIGO NA UKU: ZAKKA

    Zakka ita ce sadakar da wanda ta wajaba a kansa ya ke bayar da ita duk shekara ga wadanda suka cancance ta kamar fakirai da shauran wadanda ya halatta a ba su.

    Zakka ba ta wajaba a kan fakiri tun da bai mallaki gwargwadon abin da shari'a ta kayyade za a fitar masa da zakka ba (wato NISABI). Don haka tana wajaba ne a kan mawadata.

    Allah Ya wajabta masu ita don kammala masu musuluncinsu da kyautata yanayi da halayensu, da kiyaye su, su da dukiyoyinsu daga masifu da bala'ai, da kuma tsarkake su daga zunubai. Hakannan, don share hawayen fakirai da mabukata, da kula da manyan masalahohinsu, wadanda rashinsu ya ke ci wa kowannensu tuwo a kwarya.

    Tare da duk wadancan abubuwan da a ka ambata za ka ga abin da a ka ce mawadatan su bayar, bai fi cikin cokali ba in ka kwatanta da dukiya da arzukin da Allah Ya yi masu.

    JIGO NA HUDU: AZUMI

    Wato azumtar watan Ramalana mai albarka; watan tara a jerin watannin shekarar hijira.

    A cikinsa musulmi su na haduwa kwansu da kwarkwatarsu, su bar manyan sha'awowinsu da rana; ba ci, ba sha, ba saduwa da iyali (tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana). Kuma Allah Madaukakin Sarki, Yana musanya masu wadancan abubuwa da suka bari daga falalarSa, da ihsaninSa; wato Ya cika masu addininsu, da imaninsu, Ya kuma kankare masu zunubansu, Ya kuma daga darajojinsu, da dai shauransu na daga manyan alheran duniya da na lahira da Ya rataya su da azumi.

    JIGO NA BIYAR: HAJI

    Haji shi ne zuwa dakin Allah Mai girma (da ke Maka), a wani lokaci takamaimai don gudanar da wasu ayyukan ibadu na musamman. Allah Madaukakin Sarki Ya farlanta haji ga mai iko sau daya kacal a rayuwarsa gabadaya.

    A lokacin aikin haji ne daukacin musulmi su ke yin tururuwa su hadu - daga duk fadin duniya - a fiyayyaun wurare a bayan kasa, suna masu bautawa ubangiji daya, suna sanye da kaya iri daya, ba bu bambanci tsakanin shugaba da talaka, babu bambanci tsakanin mawadaci da mabukaci, babu bambanci tsakanin fari da baki.

    Haka, za su yi dafifi gabadaya don gabatar da wasu iyakantattun ibadu, alal misali tsayuwar arfa, dawafi (wato zagaya Ka'aba madaukakiya alkiblar musulmi), sa'ayi (wato kai-kawo tsakanin dutsen Safa da dutsen Marwa). Wasu ke nan daga cikin ibadu mafiya girma da a ke gabatarwa a wadannan wurare masu albarka.

    Hakika Allah ne kadai Ya san dumbin alfanu na addini da na duniya da aikin haji ya tattaro; don ba za su kirgu ba.

    GINSHIKI NA UKU

    Sannan hakika musulunci ya tsara rayuwar mabiyansa daidaikunsu da jama'unsu da abin da zai tabbatar masu jin dadin duniya da na lahira.

    DON KUWA ya halatta masu aure ya kuma kwadaitar da su yinsa, ya kuma haramta masu zina da luwadi, da duk sauran ayyukan assha.

    SANNAN ya wajabta masu sada zumunta, da tausayin fakirai da musakai da kula da su. Ya wajabta, ya kuma kwadaitar da su da siffatuwa da duk wani kyakkyawan hali ya kuma haramta hada da kada akalarsu daga duk wani mummunan hali.

    Sannan ya halatta masu neman na-kansu, su nemi halaliyarsu, ta hanyar kasuwanci, ko kodago, da makamantansu. Ya kuma haramta masu riba, da duk wani haramtaccen ciniki, kazalika duk wani abin da akwai algus ko garari a ciki.

    Hakanan ya kula da bambancin mutane wajen kiyaye tsare-tsare da dokokinsa, da kiyaye hakkokin wasu, haka ce ma ta sa ya shar'anta wasu ukubobi masu tsawatarwa (wanda duk a ka zartarwa da daya daga ciki ya bar sha'awar kuma aikata laifin da ya janyo masa ita, kai! waninsa ma ba zai yi tunanin aikatawa ba).

    Wasu ukubobin sun shafi keta hakkokin Allah Madaukaki kamar ridda (yin abin da zai fitar da mutum daga musulunci), da zina, da shan giya. Wasu kuma sun shafi daukacin nau'oin ta'adda ga hakkokin mutane, kamar kisan-kai ko sata ko kazafi (zargin kamamme ko kamammiya da zina ba tare da shedu ba), ko yin ta'adda da duka, ko duk wata cutarwa. Hakika, duk wanda ya yi duba da idon basira zai ga kowace ukuba ta dace da laifin da a ka shar'antata dominsa, don zai ga hukunci ne tsaka-tsaki (ba sako-sako, ba kuma shige-gona-da-iri).

    Bugu-da-kari, musulunci ya tsara ya kuma tantance alakar da ke akwai tsakanin shuwagabanni da talakawansu, haka ce ma ta sa ya wajabtawa talakawa bin shuwagabaninsu cikin duk abin da ba sabon Allah ba ne, ya kuma haramta masu tawaye da fito-na-fito da su, saboda kanana da manyan barnace-barnacen da hakan ke haifarwa.

    A karshe, zai yiwu mu ce ba wani shakku ko tababa kan cewar musulunci ya kunshi gini da samar da sahihiyar alaka hada da ingantaccen aiki tsakanin bawa da ubangijinsa, da tsakanin mutum da ragowar mutanen da suke kewaye da shi a cikin dukanin al'amura na yau da kullum. Ba wani alheri na daga halaye da mu'amaloli sai ya nuna wa al'umma ya kuma kwadaitar da su don su aikata. Hakanan babu wani sharri a cikin halaye da mu'amaloli sai ya gargadi al'umma ya kuma hana su aikata shi. Hakika wannan yana bayyana mana kuru-kuru cikar wannan addini da kyawunsa ta kowace fuska.

    DUKKANIN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI

    FASSARAR : MUHAMMAD NURA ABDULLAHI

    معلومات المادة باللغة الأصلية